• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Manufofin Tinubu na bunƙasa masana’antu suna samar da ayyuka, ayyukan yi da ƙirƙire-ƙirƙire – Ministan Yaɗa Labarai

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
August 4, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Manufofin Tinubu na bunƙasa masana’antu suna samar da ayyuka, ayyukan yi da ƙirƙire-ƙirƙire – Ministan Yaɗa Labarai
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, tare da sauran manyan baƙi a wajen rangadin da Tawagar Yaɗa Labarai ta Fadar Shugaban Ƙasa ta kai hedikwatar Hukumar Bunƙasa Kimiyya da Injiniya ta Ƙasa (NASENI) da ke Abuja a yau Talata

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, tare da sauran manyan baƙi a wajen rangadin da Tawagar Yaɗa Labarai ta Fadar Shugaban Ƙasa ta kai hedikwatar Hukumar Bunƙasa Kimiyya da Injiniya ta Ƙasa (NASENI) da ke Abuja a yau Talata

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, tare da sauran manyan baƙi a wajen rangadin da Tawagar Yaɗa Labarai ta Fadar Shugaban Ƙasa ta kai hedikwatar Hukumar Bunƙasa Kimiyya da Injiniya ta Ƙasa (NASENI) da ke Abuja a yau Talata

yayin rangadin da Tawagar Yaɗa Labarai ta Fadar Shugaban Ƙasa ta kai
.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce manufofin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na bunƙasa masana’antu a ƙarƙashin Ajandar Sabunta Fata suna ci gaba da samar da manyan ayyuka, ayyukan yi, ƙirƙire-ƙirƙire, da damarmakin tattalin arziki a faɗin ƙasar nan.

Idris ya bayyana hakan ne a ranar Talata a hedikwatar Hukumar Bunƙasa Kimiyya da Injiniya ta Ƙasa (NASENI) da ke Abuja, yayin rangadin da Tawagar Yaɗa Labarai ta Fadar Shugaban Ƙasa ta kai hukumar.

Ya ce an ƙaddamar da Rangadin Yaɗa Labarai na Ajandar Sabunta Fata ne domin bai wa ‘yan Nijeriya damar ganin ayyuka da shirye-shiryen da Gwamnatin Tarayya take aiwatarwa da idon su.

Ministan ya ce: “Muna son ‘yan Nijeriya su gani da idon su yadda manufofin gwamnati ke komawa ayyuka na zahiri, samar da ayyukan yi, ƙirƙire-ƙirƙire, da damarmaki. Ana ƙara tabbatar da gaskiya idan hukumomin gwamnati suna hulɗa kai-tsaye da jama’a, kuma ana ƙara ƙarfafa ɗaukar nauyi idan ‘yan ƙasa za su iya tantance cigaban da aka samu da kansu.”

Idris ya bayyana NASENI a matsayin muhimmiyar hukuma da ke jagorantar sauyin masana’antun Nijeriya ta hanyar kimiyya, aikin injiniya da fasaha, inda take aiwatar da ayyuka a fannonin masana’antun cikin gida, makamashi mai sabuntawa, aikin gona na zamani, fasahar zamani, da bunƙasa ƙwarewar ma’aikata.

Ana nuna wa Minusta Idris wani abu a lokacin ziyarar

A cewar sa, manufar Shugaba Tinubu ita ce gina tattalin arziki mai ɗorewa kuma mai dogaro da kai, wanda ya ta’allaƙa kan ƙirƙire-ƙirƙire, ƙara darajar kayayyakin cikin gida da kuma ƙarfafa gasa a fannin masana’antu.

Ya ce: “Manufar mu a bayyane take; ita ce sauya Nijeriya daga ƙasar da ta fi zama mai amfani da kayayyaki zuwa ƙasar da ke samarwa, ƙirƙire-ƙirƙire da fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje.”

Ministan ya ƙara da cewa Ajandar Sabunta Fata ta sanya bunƙasa masana’antu, fasaha da ƙarfafa matasa a matsayin ginshiƙan sauya tattalin arzikin ƙasa, ta hanyar samar da yanayi mai kyau ga zuba jari, kasuwanci da samar da ayyukan yi masu ɗorewa.

Ya kuma yaba wa shugabanci da ma’aikatan NASENI bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen bunƙasa fasaha da hanyoyin aikin injiniya na cikin gida domin ƙarfafa ƙarfin samar da kayayyaki a ƙasar da rage dogaro da kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje.

Haka kuma, Idris ya yaba wa membobin Tawagar Yaɗa Labarai ta Fadar Shugaban Ƙasa bisa rawar da suke takawa wajen bayyana gaskiya ta hanyar yaɗa sahihan bayanai, rahotanni masu daidaito da kuma na gani da ido kan yadda ake aiwatar da manyan shirye-shirye da ayyukan gwamnati.

Tun da farko, Mataimakin Shugaban Hukumar kuma Babban Jami’in Gudanarwa na NASENI, Khalil Suleiman Halilu, ya ce hukumar tana aiwatar da ingantacciyar dabarar bunƙasa masana’antu da ta mayar da hankali kan masana’antun cikin gida, musayar fasaha, ƙirƙire-ƙirƙire a fannin kiwon lafiya da kuma amfani da binciken kimiyya wajen samar da kayayyaki.

Ya ce ayyukan NASENI yanzu sun shafi manyan sassa takwas na masana’antu, tare da aiwatar da ayyuka a dukkan shiyyoyin siyasar ƙasar nan guda shida da kuma Babban Birnin Tarayya.

Tawagar Yaɗa Labarai ta Fadar Shugaban Ƙasa ta kai hedikwatar Hukumar Bunƙasa Kimiyya da Injiniya ta Ƙasa (NASENI) da ke Abuja

Halilu ya ce: “Manufar mu ita ce gina masana’antu masu ɗorewa ta hanyar ƙera kayayyakin da suka dace da kasuwar Nijeriya, haɗa su a cikin gida, ƙara yawan abubuwan da ake samarwa a cikin gida a hankali, tare da gina masana’antun da za su iya yin gogayya a kasuwannin duniya. Ta haka ne muka samu damar kafa fiye da masana’antu 20 cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.”

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga; Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Cif Sunday Dare; Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Daidaita Manufofi, Hadiza Bala Usman; Babbar Mataimakiya ta Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Temitope Ajayi; Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Hulɗa da Jama’a da Shigar da ‘Yan Ƙasa Cikin Ayyukan Gwamnati; da sauran manyan baƙi.

Tags: Fadar Shugaban ƘasaHukumar Bunƙasa Kimiyya da Injiniya ta Ƙasa (NASENI)Mohammed IdrisTawagar Yaɗa Labarai
Previous Post

Tinubu ya amince da ƙarin albashi har kashi 80 ga jami’an sojoji

Next Post

Sojoji sun kuɓutar da mutum 14, sun ƙwato dabbobi 281 daga hannun ’yan ta’adda

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post
Sojoji sun kuɓutar da mutum 14, sun ƙwato dabbobi 281 daga hannun ’yan ta’adda

Sojoji sun kuɓutar da mutum 14, sun ƙwato dabbobi 281 daga hannun ’yan ta'adda

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!