Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa dakarun ta na Birged ta 6 na Sojan Najeriya/Sashi na 3, Operation Whirl Stroke (OPWS), sun kama wani fitaccen shugaban masu garkuwa da mutane a kudancin Jihar Taraba.
Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na wucin-gadi, Birged ta 6, Laftanar Umar Muhammad, ya ce a cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin Litinin cewa a yayin wani samame da aka gudanar a ranar 23 ga Nuwamba, 2025, dakarun suka cafke wanda ake zargi da jagorar masu garkuwa da mutane yayin da yake ƙoƙarin tserewa daga Ƙaramar Hukumar Wukari.
A cewar sanarwar, wanda ake zargin, mai suna Alhaji Abubakar Bawa, ana zaton makusanci ne ga Umar Musa, wani shahararren jagoran garkuwa da mutane da dakarun Birged ta 6 suka kama a ranar 22 ga Nuwamba, 2025.
Binciken farko ya nuna cewa akwai ƙarfi da alaƙa mai zurfi tsakanin waɗannan mutanen biyu da kuma wata babbar ƙungiyar laifuffuka da ke da alhakin garkuwa da mutane da dama, hare-hare, da kuma shirya aikata laifuka a faɗin yankin.
Da yake mayar da martani kan ci gaban lamarin, Kwamandan Birged ta 6/Sashi na 3 OPWS, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya yaba wa dakarun bisa ƙwarewar su, jajircewa, da daidaitaccen aikin da suka gudanar.
Ya ce kama Bawa “hujja ce ta bayyana cewa Operation Zafin Wuta na cimma manufar sa ta rushe ƙungiyoyin laifuka da dawo da tsaro ga al’ummomin da lamarin ya shafa.”

Ya tabbatar da jajircewar Birged ɗin wajen ci gaba da ayyukan share fage, yana jaddada cewa babu wani ɓarawo da zai tsere daga hukunci matuƙar ayyukan ke tafiya da irin wannan sauri.
“Wannan sabuwar nasarar ta ƙara ƙarfafa aniyar Rundunar Sojin Najeriya wajen kawar da duk wani barazanar aikata laifi a Kudancin Taraba da kuma dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin. Sojoji a ƙarƙashin Birged ta 6 suna cikin shirin ko-ta-kwana yayin da bincike kan dangantakar wanda ake zargin ke ƙara zurfi,” inji sanarwar.
Rundunar Sojin Najeriya ta kuma shawarci mazauna yankin su kasance cikin shiri, su kuma rika ba da sahihin bayani domin taimaka wa hukumomin tsaro a ƙoƙarin su na ci gaba.
Ana ci gaba da tsare wanda ake zargin, inda ake gudanar da ƙarin bincike a kansa.







