Wani sabon ango, Malam Abubakar Abdulkarim, wanda aka fi sani da Ɗan Gaske, ana zargin matar sa ta kashe shi ta hanyar yankan rago kwanaki uku kacal da yin auren su a garin Jibiya, Ƙaramar Hukumar Jibiya ta Jihar Katsina.
Wannan lamari mai tayar da hankali, wanda ya faru da yammacin shekaranjiya Lahadi, ya girgiza al’umma tare da haifar da tambayoyi game da abin da ya haifar da kisan gillar.
Abdulkarim, wanda ya auri Zainab Muhammad a ranar Alhamis da ta gabata, wato 20 ga Nuwamba, rahotanni sun bayyana cewa an kai masa hari ne yayin da yake barci a gidan su da ke unguwar Tashar Buja, inda aka yi masa mugun yanka da wuƙa a wuya.
Wani ɗan’uwan mamacin, Aminu Ɗanladi, ya ce shi da sauran ’yan’uwa suna tare da angon a safiyar ranar suna tattaunawa kan shirye-shiryen wata ziyarar ‘yan’uwa da za su je daga baya da yamma.
“Mun je muna shirin fita. Ya tashi ya bar mu ya koma gida domin ya shirya,” inji Ɗanladi. “Ba da jimawa ba sai muka ji labarin cewa an same shi ya mutu. Abin ya ba mu baƙin ciki ƙwarai.”
Ɗanladi ya ƙaryata ji-ta-ji-tar da ke yawo cewa auren dole ne aka yi, ya ce ma’auratan sun zauna lafiya kuma ba su nuna wata matsala tsakanin su ba kafin auren ko bayan auren.
Majiyoyi a unguwar sun shaida wa manema labarai cewa matar, wadda ake kyautata zaton ta ɗan haura shekaru 20 kaɗan da haihuwa, ’yar asalin cikin birnin Katsina ce, kuma ta nuna halaye masu ban-mamaki bayan faruwar lamarin.
An ce ta bar gidan bayan abin da ya faru, ta je gidan maƙwabta tana neman abinci.
Wannan halayyar ta rashin damuwa, duk da cewa sabuwar amarya ce, ta haifar da zargi a zukatan wasu mata manya, wanda ya sa nan da nan suka yanke shawarar bin ta zuwa gidan.
“Da suka shiga gidan, sai suka tarar da angon kwance cikin jini,” inji wata majiya a garin. “Suka yi ihu suka sanar da jami’an tsaro.”
Ana zargin cewa Zainab ta yanka shi ne lokacin da yake barci a tsakanin ƙarfe 12 na rana zuwa 1 na rana.
An samu bayanin cewa matar ta taɓa yin aure a da amma aka sake ta, abin da ake zargin ba a sanar da angon da iyalin sa ba kafin auren.
Rahotanni sun ce wata yar’uwar sa ce ta haɗa su, kasancewar sun san juna tun lokacin da suke ɗalibta a Makarantar Gwamnati ta ‘Yan Mata (GGSS) da ke Jibiya.
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Katsina ta tabbatar da faruwar lamarin a jiya Litinin, tana mai cewa an kama wadda ake zargi.
Jami’in hulɗa da jama’a na ’yan sanda, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce ofishin su na Jibiya ya samu kiran gaggawa kusan ƙarfe 1:30 na rana, inda aka hanzarta tura jami’ai zuwa wurin.
“Da suka isa, jami’an sun same shi kwance ba shi motsi cikin jini tare da yanka a wuya mai zurfi,” inji Aliyu. “An garzaya da shi asibiti domin ceton ran sa, amma abin takaici aka tabbatar da mutuwar sa tun kafin a fara ba shi agaji.”
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Katsina, Bello Shehu, ya ba da umurnin a gudanar da ingantacce kuma cikakken bincike, tare da roƙon jama’a da ke da bayanai masu amfani da su taimaka wa hukuma.







