Mutane a garuruwan Onitsha, Nnewi da sauran sassan Jihar Anambra sun ci gaba da yin zaman dirshan a gida na kowane Litinin da suka daɗe suna yi, domin nuna goyon baya ga shugaban Ƙungiyar ’Yan Asalin Biyafra (IPOB), Mazi Nnamdi Kanu, duk da hukuncin ɗaurin rai-da-rai da aka yanke masa tare da tsare shi a kurkuku.
Kasuwanni, makarantu, bankuna, asibitoci da ofisoshin gwamnati sun kasance a rufe, sannan tituna sun kasance kusan babu kowa, abin da ke nuna irin goyon bayan da jama’a ke nuna wa Kanu.
Wasu mazauna yankin sun shaida wa jaridar Vanguard cewa zaman gidan na Litinin zaɓi ne na jama’a, ba tilas da IPOB ta ƙaƙaba ba.
Sun ce iƙirarin da aka yi a baya cewa IPOB ce ke tilasta zaman gidan ba daidai ba ne, suna mai cewa duk wani aikin ta’addanci da aka gani a lokutan baya na wanda ya ga dama ne, ba umarnin ƙungiyar ba.
Obed Nwachukwu ya ce, “Waɗanda ke sa ran kasuwanni da shaguna za su buɗe saboda kama da tsare Kanu, za su jira. Muna bada cikakken goyon baya a gare shi har sai ya samu ’yanci.”
Chief Okwudili Okoye ya ƙara da cewa, “Maganganun Gwamnatin Tarayya da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta yanke ba su da inganci. Zaman gidan na Litinin zai ci gaba a matsayin na ganin dama domin neman adalci da dai-daito ga ’yan Igbo. Al’amura za su koma daidai ne kawai idan Nnamdi Kanu ya samu ’yanci.”
Mutanen yankin sun jaddada cewa wannan zanga-zangar ba ta tsaya ga ƙungiyar IPOB kaɗai ba, abin da take nufi shi ne nuna goyon baya ga Kanu da kuma tsayuwa kan abin da suka kira rashin adalci ga Inyamirai.







