• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Sojoji sun gama da ‘yan ta’adda sama da 80, sun ceto mutum 34 a jihohi

Wakilin Mu by Wakilin Mu
December 29, 2025
in Tsaro
A A
0
Sojoji sun gama da ‘yan ta’adda sama da 80, sun ceto mutum 34 a jihohi
Sojojin Nijeriya a bakin aiki

Sojojin Nijeriya a bakin aiki

Rundunar Sojan Ƙasa ta Nijeriya ta bayyana cewa dakarun ta sun hallaka ‘yan ta’adda sama da 80, tare da ceto mutane 34 da aka sace, a jerin hare-haren haɗin gwiwa da aka gudanar tsakanin ranakun 25 zuwa 29 ga Disamba, 2025.

Wata majiya mai tushe daga Hedikwatar Sojin Ƙasa ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) cewa an samu waɗannan nasarori ne a jihohin Borno, Adamawa, Sokoto, Katsina, Neja, Zamfara, Filato, Delta, Cross River da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT).

A Jihar Borno, majiyar ta ce hare-haren sama tare da bin diddigi na ƙasa da aka kai a Sowolwolo, cikin Ƙaramar Hukumar Bama, da kewayenta, sun yi sanadin hallaka ‘yan ta’adda 19, tare da rusa sansanonin ajiyar kayayyakin su da tarwatsa hanyoyin sadarwar ISWAP da JAS.

Ta ƙara da cewa wasu hare-hare na gaba da aka kai a yankunan Gulumba Gana, Kumshe, Kasho Miri da Chongolokura sun yi sanadin hallaka ƙarin ‘yan ta’adda 38. Haka kuma, bayanan leƙen asiri da sa ido (ISR) sun gano manyan shugabannin ‘yan ta’adda da ake shirin kai musu hari nan gaba.

A jihohin Neja da Katsina kuwa, majiyar ta bayyana cewa dakarun soji sun fatattaki hare-haren ‘yan ta’adda da aka kai sansanin FOB Kwanar Dutse a Ƙaramar Hukumar Mariga, da kuma kan hanyar Shanono–Katsina.

A yayin wannan samame, an ceto farar hula guda ɗaya tare da ƙwato shanu 78 da tumaki 28 da ‘yan ta’addan suka sace.

Game da ayyukan ceto daga hannun masu garkuwa da mutane, majiyar ta ce a jihar Kebbi, dakarun Bataliya ta 223 sun ceto mutane 16 bayan samun bayanan sirri a ƙauyen Unashi da ke Ƙaramar Hukumar Danko Wasagu.

A jihar Filato kuma, an ceto mutum guda a yankin Yaka Naji Jandutse da ke Ƙaramar Hukumar Wase.

Majiyar ta ƙara da cewa dakarun sun kuma daƙile ayyukan ta’addanci da laifuka a sassa daban-daban na ƙasar, inda suka cafke masu haƙar ma’adinan zinare ba bisa ƙa’ida ba guda 11 a birnin Tarayya Abuja. Haka kuma, an kama wasu mutane biyu da ake zargi da fashi da makami a Filato, tare da kwato kuɗaɗen da suka sace.

A jihar Delta, an cafke masu satar ɗanyen mai guda biyu, inda aka ƙwato jarkoki 104 (lita 2,600) na ɗanyen mai.

A Kuros Riba kuwa, an kama wasu da ake zargin ‘yan fashin teku ne mutum uku da ke da alaƙa da ƙungiyar ‘yan bindiga ta BIG JOE.

Majiyar ta jaddada cewa waɗannan ayyuka na nuna ƙudirin sojojin Najeriya na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tabbatar da bin doka da oda, da kuma wanzar da zaman lafiya da tsaro a dukkan yankunan da abin ya shafa.

Ta kuma sake tabbatar da aniyar Rundunar Sojin Ƙasa ta ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro bisa sahihan bayanan sirri, ceto waɗanda aka sace, da kuma murƙushe duk wata barazana daga ‘yan ta’adda da masu aikata laifuka a faɗin ƙasar.

Tags: rashin tsarota'addanci
Previous Post

Fitaccen ɗan dambe, Anthony Joshua, ya tsallake rijiya da baya yayin da hatsarin mota ya kashe mutum biyu a Ogun

Next Post

Yadda bankin CBN ya hana ‘yan Nijeriya fuskantar ƙarancin kuɗi a ATM da bankuna yayin hutun ƙarshen shekara

Related Posts

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
EFCC ta samu nasarar hukunta mutumin da ya yi ƙoƙarin sumogar zinari mai darajar Naira biliyan 4.4 a Kano
Tsaro

EFCC ta samu nasarar hukunta mutumin da ya yi ƙoƙarin sumogar zinari mai darajar Naira biliyan 4.4 a Kano

November 17, 2026
Sojoji sun halaka ’yan ta’adda, sun ceto mutum 16, sun ƙwato babura 38 a Neja da Kebbi
Tsaro

Sojoji sun halaka ’yan ta’adda, sun ceto mutum 16, sun ƙwato babura 38 a Neja da Kebbi

November 6, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta buƙaci bincike kan bidiyon atisayen muzaharar Izala
Tsaro

’Yan sanda sun kama matashin Izala kan bidiyon da ke tunzura rikicin addini

October 27, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka
Tsaro

’Yan sanda a Katsina sun tabbatar da kashe Sheikh Yahaya Masussuka da abokin sa

October 26, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka
Tsaro

Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka

October 26, 2026
Next Post
Yadda bankin CBN ya hana ‘yan Nijeriya fuskantar ƙarancin kuɗi a ATM da bankuna yayin hutun ƙarshen shekara

Yadda bankin CBN ya hana 'yan Nijeriya fuskantar ƙarancin kuɗi a ATM da bankuna yayin hutun ƙarshen shekara

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!