An tabbatar da mutuwar mutane biyu sakamakon wani haɗarin mota da ya ritsa da fitaccen ɗan dambe ɗan Nijeriya–Birtaniya, Anthony Joshua, a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan a Jihar Ogun.
Haɗarin ya faru ne a ranar Litinin, lokacin da wata mota da ke ɗauke da tsohon gwarzon damben nauyin heavyweight na duniya ta yi karo da wata babbar mota (tirela) da ke tsaye a kan hanyar da ke cike da cunkoso.
Motar, Lexus SUV mai lamba KRD 850 HN, tana cikin ayarin motocin da ke ɗauke da Anthony Joshua lokacin da haɗarin ya faru.
Da yake tabbatar da lamarin, kakakin Hukumar Kare Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) reshen Jihar Ogun, Afolabi Odunsi, ya ce mutane biyu sun rasu a haɗarin, yayin da fitaccen ɗan damben ya tsira da ran sa.
Odunsi ya bayyana wa manema labarai cewa jimillar mutane biyar ne haɗarin ya ritsa da su.
“Gaskiya ne, amma shi (Anthony Joshua) yana raye. Mutane biyar abin ya shafa, biyu sun mutu. Zan aiko muku da sanarwa nan ba da jimawa ba,” inji kakakin FRSC.
Ko da yake ba a bayyana sunayen mutanen da suka rasu ba nan take, Odunsi ya ce jami’an ceto sun kai ɗauki cikin gaggawa, kuma an fara bincike domin gano musabbabin hatsarin.
Anthony Joshua ya shahara a duniya baki ɗaya saboda nasarorin sa a wasan dambe na ƙwararru. Shi ɗan ƙasar Nijeriya da Birtaniya ne.
Asalin sa ya fito ne daga Shagamu a Ƙaramar Hukumar Shagamu ta Jihar Ogun, inda ake kallon sa a matsayin abin alfahari da abin koyi ga matasa da dama a Nijeriya.
Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, Anthony Joshua ko ‘yan tawagar sa ba su fitar da wata sanarwa a hukumance game da lamarin ba.







