• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Sojin sama sun kashe ‘yan bindiga 23 da ke ƙoƙarin tserewa bayan sun kai hari a Kano

Wakilin Mu by Wakilin Mu
January 4, 2026
in Tsaro
A A
0
Sojin sama sun kashe ‘yan bindiga 23 da ke ƙoƙarin tserewa bayan sun kai hari a Kano
Gawarwakin 'yan ta'adda da aka kashe

Gawarwakin 'yan ta'adda da aka kashe

Rundunar Haɗin Gwiwa (JTF) tare da goyon bayan sashen sama na Operation Fansan Yamma sun hallaka aƙalla ‘yan bindiga 23 da suke ƙoƙarin tserewa daga Jihar Kano bayan sun kai hare-hare a ƙananan hukumomin Shanono da Tsanyawa.

Wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Soja na Birged ta 3 na Rundunar Sojin Nijeriya, Manjo Zubairu Babatunde, ya fitar a Kano a yau Lahadi, ta bayyana cewa ‘yan bindigar sun ƙaddamar da hare-haren ne a daren Alhamis zuwa safiyar Juma’a.

Sanarwar ta ce dakarun ƙasa sun daƙile hare-haren cikin nasara tare da yi wa maharan mummunar asara, kafin su bi sawun waɗanda suka tsere zuwa ƙauyen Karaɗuwa a Ƙaramar Hukumar Matazu ta Jihar Katsina.

A cewar Babatunde, rahotannin leƙen asiri sun nuna cewa ‘yan bindigar sun taru a Ɗanmarke da ke Matazu domin binne wasu daga cikin ‘yan’uwan su da aka kashe a yayin artabun da dakarun soji.

Ya ce: “Ɓangaren sama na Sector 2 Operation Fansan Yamma ya gano ‘yan bindigar tare da bibiyar motsin su har sai da baburan su suka taru bayan sun ƙetare wani busasshen rafi,” inji sanarwar. “Daga nan aka kai farmakin sama cikin ƙwarewa, wanda ya yi sanadin hallaka aƙalla ‘yan ta’adda 23, yayin da ake zargin wasu da dama sun jikkata.”

Sanarwar ta ƙara da cewa aikin, wanda ya samu goyon bayan ayyukan leƙen asiri na sama (ISR), ya kuma haifar da lalata makamai da kayan aiki da dama na ‘yan bindigar.

Kwamandan Birged ta 3 na Rundunar Sojin Nijeriya ya yaba wa sashen sama da dakarun ƙasa bisa jarumtaka da jajircewar su a yayin aikin, yana mai cewa, “Jarumtaka da juriya da suka nuna abin a yaba ne.”

Babatunde ya tabbatar da cewa halin tsaro a Jihar Kano na nan cikin kwanciyar hankali, inda dakaru ke ci gaba da sintiri da sa ido a yankunan da abin ya shafa.

Ya ce ƙwazon aiki da ƙwarin gwiwar dakarun na da matuƙar gamsarwa.

Rundunar Sojin Nijeriya ta gode wa al’umma kan goyon bayan da suke bayarwa a yaƙin da ake yi da ‘yan bindiga da ta’addanci, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro bayanai cikin gaggawa.

Ta jaddada cewa sojoji, tare da sauran hukumomin tsaro, za su ci gaba da ɗaukar dukkan matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a da tabbatar da tsaron ƙasa.

Tags: 'yan ta'addahariKanosojojitsaro
Previous Post

Muhimmin lokaci a Nijeriya: Hujjar da ta sa hanyar da aka ɗauka ita ce mai ɓullewa

Next Post

Tinubu ya umurci jami’an tsaro su gano ‘yan ta’addar da suka yi kisan gilla a Kasuwar Daji

Related Posts

Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya taya Kiristoci murnar bikin Ista
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa al’ummar Neja kan rasuwar mutane a Wushishi, ta bayar da umarnin bincike

September 18, 2026
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja

September 18, 2026
Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa
Tsaro

Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa

September 9, 2026
Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam

September 1, 2026
Next Post
Tinubu ya umurci jami’an tsaro su gano ‘yan ta’addar da suka yi kisan gilla a Kasuwar Daji

Tinubu ya umurci jami'an tsaro su gano 'yan ta'addar da suka yi kisan gilla a Kasuwar Daji

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!