Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa shirye-shiryen ƙarfafa matasa na gwamnatin Bola Ahmed Tinubu suna fitowa ne daga sahihin ƙudirin faɗaɗa damarmaki ga matasan Nijeriya, ba wai saboda la’akari da siyasar jam’iyya ba.
Idris ya yi wannan bayani ne a daren Talata a Abuja, yayin wani taron mu’amala da matasa daga reshen matasan APC da kuma cibiyoyin ilimi na gaba da sakandare a faɗin Babban Birnin Tarayya, a Cibiyar Albarkatu ta The Nest, Abuja.
Shugaban Matasa na Ƙasa na APC, Dakta Dayo Israel, shi ne ya jagoranci taron, wanda aka gudanar cikin tattaunawa a bayyane da gaskiya.
A cewar Ministan, shirye-shiryen da gwamnatin Tinubu ta mayar da hankali a kan su kan matasa an tsara su ne domin su kasance na kowa da kowa, masu sauƙin samu, kuma masu tasiri, ba tare da la’akari da alaƙar siyasar mutum ba.
Ya ce: “NELFUND na ’yan Nijeriya ne; ba na APC ba. Shirin 3MTT na ’yan Nijeriya ne; ba na APC ba.
“Duk abin da Shugaban Ƙasa yake yi shi ne domin dawo da wadata, mutunci, da sabunta fata, domin matasa su cimma cikakkiyar damar su kuma su sake yin imani da ƙasar su.”
Ya bayyana cewa, bisa sababbin bayanai da ke hannu, sama da ɗalibai 788,000 a halin yanzu suna cin gajiyar Asusun Rancen Ilimi na Nijeriya (NELFUND), inda aka ware sama da ₦250 biliyan domin biyan kuɗaɗen karatu da kula da rayuwar ɗalibai a manyan makarantu a faɗin ƙasar nan.
Ministan ya kuma jaddada Shirin Ƙwarewar Fasaha Miliyan Uku (3MTT), wani muhimmin shirin ƙwarewar dijital da Ministan Sadarwa, Ƙirƙira da Tattalin Arzikin Dijital ya ƙaddamar a madadin Shugaba Tinubu.
Shirin yana da nufin horas da ’yan Nijeriya miliyan uku a fagen ƙwarewar fasaha da dijital da ake matuƙar buƙata, domin inganta damar samun aiki da shiga gasa a tattalin arzikin dijital na duniya.
“Abin da ya fi burge ni shi ne, har ma waɗanda ke cewa waɗannan shirye-shirye ba gaskiya ba ne suna shiga ciki, har da mutane daga wasu jam’iyyun siyasa,” inji shi, ya ƙara da cewa, “Hakan yana nuna cewa shirye-shiryen suna aiki kuma suna isa ga ’yan Nijeriya kamar yadda aka tsara.”
Idris ya bayyana gwamnatin Tinubu a matsayin wadda za a tuna da ita a tarihin Nijeriya a matsayin mafi abokantaka da matasa, ba kawai saboda manyan shirye-shiryen ƙarfafawa ba, har ma da naɗa matasa a muhimman muƙaman shugabanci.
Ya ce: “Dole matasa su fara da amincewa da wannan gwamnati. Gwamnati ce da ta zuba jari sosai a makomar ku, kuma tana ci gaba da sauraro, tattaunawa, da samar da damarmaki.”
Dangane da tattalin arziki, Ministan ya ce sauye-sauyen da Shugaban Ƙasa ya ɗauka cikin ƙarfin hali sun fara haifar da sakamako mai kyau, inda alamun farfaɗowa ke ƙara bayyana.
Ya nuna raguwar farashin abinci a hankali da kuma saukar hauhawar farashi a matsayin hujjar cewa tattalin arzikin ya fara gyaruwa.
“Hauhawar farashi yana sauka,” inji Idris, ya ƙara da cewa, “Shugaban Ƙasa ya yi hasashen sauka zuwa kashi 15 cikin 100, kuma a yau mun riga mun kai kashi 14.45 cikin 100. Wannan ba daidaituwa ba ce; sakamakon tsare-tsaren manufofi ne da aka ɗauka da gasken gaske.”
Ya kuma bayyana cewa ficewar Nijeriya daga jerin Financial Action Task Force (FATF) mai launin toka babbar nasara ce da za ta ƙarfafa amincin tsarin kuɗi, ta ƙara gwiwar masu zuba jari, tare da inganta damar shigar Nijeriya kasuwannin kuɗi na duniya.
Ministan ya buƙaci matasan Nijeriya da su ci gaba da mara wa gwamnati baya yayin da take shimfiɗa tubalan wadata mai ɗorewa ga ƙasa.
Haka kuma ya yi kira ga matasa da su yi amfani da tasirin su da yawan su a kafafen sada zumunta cikin ɗa’a, ta hanyar yaɗa sahihan bayanai da kuma yaƙar labaran ƙarya.
A ƙarshe, Idris ya sake jaddada cewa Ajandar Sabuwar Fata (Renewed Hope Agenda) ta ginu ne a ƙaƙƙarfan tushe a kan ƙarfafa matasa, haɗin kai, da sabunta ƙasa, yana mai jaddada cewa makomar da gwamnati take ginawa ta dukkan ’yan Nijeriya ce.







