Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tattauna da shugabannin ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya (NLC) tare da Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin APC, Hope Uzodimma, Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, da Gwamnan Jihar Kebbi State, Dakta Nasir Idris, da Ƙaramin Ministan Ƙwadago, Honorable Nkeiruka Onyejeocha. Shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero shi ne ya jagoranci tawagar NLC zuwa taron wanda aka yi a Fadar jiyaShugaban Ƙasa a Abuja a daren Talata.







