Gwamnatin Tarayya ta bada sanarwar sabon tsari na sadarwa da jama’a, inda ta koma daga dogaro da tarukan manema labarai na lokaci-lokaci zuwa mu’amala kai-tsaye, tsari-tsari, da ma’aikatun da ke aiwatar da ayyuka, domin tabbatar da cewa ’yan Nijeriya sun fahimci sauye-sauyen da ake yi da amfanin su sosai.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar aiki da ya kai Ma’aikatar Lafiya da Walwalar Jama’a ta Tarayya a ranar Laraba, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa aiwatar da Ajandar Sabuwar Fata (Renewed Hope Agenda) ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Da yake tarbar tawagar, Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Lafiya da Walwalar Jama’a ta Tarayya, Daju Kachollom S., ta bayyana ziyarar a matsayin mai muhimmanci kuma mai kyau, tana mai jaddada cewa ingantacciyar sadarwa tana da matuƙar muhimmanci ga nasarar sauye-sauyen da ake aiwatarwa a fannin lafiya.
Ta ce Ma’aikatar ta samu gagarumin cigaba a cikin shekaru biyu da suka gabata, amma ta jaddada cewa wajibi ne a bayyana waɗannan nasarori ga ’yan Nijeriya domin samun ƙara amincewa, amfani da ayyuka, da ƙwarin gwiwar jama’a.
Idris ya bayyana cewa Ma’aikatar sa tana yin mu’amala sosai da manyan ma’aikatun da ke gudanar da ayyuka domin tabbatar da cewa labaran ayyukan gwamnati suna isa ga jama’a yadda ya kamata.
A cewar sa, shugabanci ba ya cika sai an haɗa shi da sadarwa, yana mai jaddada cewa, “Abin da ba a faɗa ba, galibi ana ɗauka kamar bai faru ba ne.”
Ya yaba da jagorancin Ma’aikatar Lafiya da Walwalar Jama’a saboda ba da fifiko ga rigakafin cututtuka, farfaɗo da kula da lafiya ta matakin farko, bunƙasa masana’antar likitanci, faɗaɗa ayyukan kula da masu cutar daji (cancer), da rage yawon neman magani a ƙasashen waje.
Ya ce waɗannan sauye-sauyen suna da tasiri kai-tsaye kuma na dindindin a rayuwar ’yan Nijeriya.
Ya tabbatar da cewa Ma’aikatar Yaɗa Labarai za ta yi amfani da kafafen ta da hukumomin ta wajen yaɗa sauye-sauyen fannin lafiya, ƙarfafa wayar da kai kan rigakafin cututtuka, da tabbatar da isar da sahihan bayanai a faɗin ƙasar nan.
Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya lafiya a jerin farko na Ajandar Sabuwar Fata ne domin lafiyayyar al’umma ginshiƙi ce ta cigaban ƙasa da bunƙasar tattalin arziki.
Ya bayyana cewa Shirin Zuba Jari na Sabunta Fannin Lafiya na Ma’aikatar ya mayar da hankali ne kan ƙarfafa shugabanci, faɗaɗa ayyukan kula da lafiya masu inganci, bunƙasa samar da magunguna a cikin gida, inganta tsaron lafiya, da tabbatar da adalci wajen samun kulawa.
Farfesa Pate ya bayyana ci gaba da aka samu wajen farfaɗo da kula da lafiya ta matakin farko, faɗaɗa allurar rigakafi, rigakafin ɓarkewar cututtuka, faɗaɗa jinyar cutar daji, da ƙara masu shiga inshorar lafiya.
Ya yi la’akari da cewa yawancin nasarorin fannin lafiya ana auna su ne ta yawan matsalolin da aka hana faruwar su, ba wai waɗanda aka shawo kan su bayan sun faru ba.
Ya jaddada cewa ingantacciyar sadarwa tana taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa ’yan ƙasa su fahimci rigakafin lafiya da jarin da gwamnati ke zubawa.
Haka kuma, Ƙaramin Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Dakta Iziaq Adekunle Salako, ya ce daidaituwar Ajandar Sabuwar Fata da Tsarin Sabunta Fannin Lafiya ya samar da haske da jagora ga sauye-sauyen da ake aiwatarwa.
Ya bayyana ingantawar da aka samu wajen amfani da fasahar lafiya ta dijital, samar da wutar lantarki ga cibiyoyin lafiya, kula da ma’aikata, da rage rikice-rikicen masana’antu ta hanyar tattaunawa mai ma’ana.
Dakta Salako ya ce Nijeriya yanzu tana da damar kula da cututtuka da dama a cikin gida, musamman a fannin kula da cutar daji, lamarin da ke rage buƙatar neman magani a ƙasashen waje tare da jawo marasa lafiya daga ƙasashen maƙwabta.
Ya jaddada muhimmancin ci gaba da hulɗa da kafafen yaɗa labarai wajen gina amincewar jama’a da tallafa wa cigaban ƙasa.
Ziyarar ta ƙare da yarjejeniya tsakanin ma’aikatun biyu na ƙarfafa haɗin gwiwa, faɗaɗa wayar da kan jama’a, da tabbatar da cewa ’yan Nijeriya sun fahimta, sun samu dama, kuma sun amfana da sauye-sauyen da ake aiwatarwa a fannin kiwon lafiya, daidai da Ajandar Sabuwar Fata ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.







