• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru 65 Da ‘Yanci: Iya dogaro da kai shi ne cikakken ‘yanci – Tanimu Yakubu

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
October 3, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Aiki Da Kasafin 2025 Cikin Satumba – Yakubu
Dakta Tanimu Yakubu

Dakta Tanimu Yakubu

Babban Darakta a Ofishin Kasafin Kuɗaɗen Gwamnatin Tarayya, Dakta Tanimu Yakubu, ya bayyana cewa duk wani ‘yancin da ƙasa ba za ta iya dogaro da kanta wajen samar da kuɗaɗen bunƙasa tattalin arzikin ta ba, to ba ‘yanci ba ne, holoƙo ne, hadarin kaka.

Yakubu ya bayyana haka a cikin wani saƙon da ya fitar ga ‘yan Nijeriya a ranar zagayowar samun ‘yanci, 1 ga Oktoba, 2025.

A cikin saƙon mai ɗauke da irin yadda gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke gagarumin aikin ciyar da ƙasa gaba ta hanyar tattalin kuɗaɗen ƙasa, Yakubu wanda ƙwararren masanin tattalin arziki ne, ya ce:

“Shekaru sittin da biyar kenan tun bayan da iyayen mu kuma shugabannin mu masu kishi suka ɗaga tuta mai launin kore da fari da kore, ta samun ‘yanci, tare da kafa tarihin rera taken ƙasa mai tabbatar da ƙarshen mulkin mallaka. ‘Yanci ya tabbatar mana mulkin kai a baki. Amma samun ‘yanci ya zama ‘holoƙo hadarin kaka’ idan ba mu da ƙarfin dogaro da kan mu.

“Mun daɗe tsawon lokaci muna dogara da ciwo bashi. Mun riƙa ci da amfani da abubuwan da ba mu ke samar da su ba. Mun riƙa ciwo bashi ido-rufe. Muka zura ido tsawon lokaci ‘yan ƙaƙuduba na yi wa ƙasar mu yankan aljihu suna kwashe mana arziki.

“A yau kuwa mun kawo ƙarfi, mun farka. Mun fahimci tabbas ba samun ‘yanci kaɗai ne mafita ba. Abin da Nijeriya ke buƙata a yanzu shi ne ‘yancin dogaro da kanta, ta yadda za ta iya riƙe kan ta.”

Da ya koma kan muhimmancin cire tallafin fetur kuwa, Yakubu ya ce: “Abu na farko shi ne an cire tallafin fetur, mun daina lissafin dawakin Rano da aikin-baban-giwa, wato bayar da tallafin fetur – tsarin da aka ragargaje tiriliyoyin naira. An cire tallafin, an toshe hanyar da wasu ‘yan gadangarƙama ke karkatar da Naira tiriliyan huɗu a duk shekara. Waɗannan maƙudan kuɗaɗe a yanzu gwamnati ta karkata su wajen gina titina, makarantu da kuma ayyukan bayar da tallafin sauƙaƙa wa marasa galihu.

“Abu na biyu kuma shi ne mun kawar da tsarin musayar kuɗi mai fuska biyu, wato mai bambancin farashi. Yanzu farashi ɗaya ne. Kasuwa ɗaya ce, kuma gaskiya ɗaya ce.”

Ya ce waɗannan tsare-tsaren bunƙasa tattalin arzikin ƙasa sun zo da tsauri. To amma a gaskiya sun kasance tamkar magani mai ɗaci a baki, kuma mai ingancin warkar da ciwo. Tsare-tsare ne da suka zama na tilas. Su ne mafita ga ƙasar da ta yi hoɓɓasar tsayawa da ƙafafun ta, maimakon ci gaba da dogaro da kayan aro.

“Gwamnatin Tinubu ta bijiro da sauya Dokar Kuɗaɗe (FRA). A yanzu akwai ƙa’idar adadin da za a riƙa yi wa basussuka waigi. A yanzu duk kowane bashin da aka ciwo tilas a ga tasiri da alfanun sa wajen gina makarantu, asibitoci ko gina titina. Lokacin ciwo bashi a yi bushasha ya wuce. Sai dai a ciwo bashi idan ya kama, domin a gina ƙasa,” cewar sa.

Da ya koma kan raba arzikin ƙasa bisa turbar adalci, Yakubu ya ce abu ne mai muhimmanci. “Dalili kenan muka bijiro da Dokar Bada Lamuni ga Ɗalibai, wato ‘Education Loan Fund Act’. Domin a tabbatar cewa talauci bai hana yaro ko guda ɗaya cika burin sa na samun ilmi ba. Za a samar wa kowane fikira da zalaƙa tsanin takawa ya kai gaci. Za a buɗe wa kowa ƙofar samun hasken cimma muradi.

“Kuma dalili kenan muka riƙa matsa-lamba domin Ƙananan Hukumomi su samu ‘yancin cin gashin kuɗaɗen su. Har yanzu ana kan wannan gwadaben, amma lokacin wannan ‘yanci ya zo.

“Tilas daga yanzu za a riƙa gina asibitocin kula da marasa lafiya a wuraren da al’umma suke zaune, ba inda gwamna ke so a riƙa ginawa ba. Tilas a gina makarantu a cikin ƙauyuka, ba sai a manyan garuruwa ko a babban birnin jiha kaɗai ba. Wannan sabon tsari shi ne zai ceto yankunan karkara.

Ya ce ya zama tilas mu kasance muna amfani da kuɗaɗen shigar da gwamnati ke samu ne wajen gina al’umma ta hanyar ta hanyar tsara ingantaccen kasafin kuɗaɗe.

Ya ce gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da gina titinan jiragen ƙasa, inganta yawan wutar lantarki da ayyukan raya karkara.

Ya ce gwamnati ta tsaurara Asusun Bai Ɗaya na Gwamnatin Tarayya (TSA), an jaddada tsarin biyan albashi na IPPIS da kuma na GIFMIS. An fasa gayyar ma’aikatan bogi. An ɗinke aljifan da aka huje kuɗaɗen gwamnati na zirarewa. A yanzu ma’aikatu sun san cewa za a iya ƙwaƙulo duk inda wani kobo ya maƙale.

Daga ƙarshe ya ce idan ana kashe kuɗaɗe ta hanyar da ta dace, za a kai ga samun ƙasaita. “Ita kuma ƙasaitar iya dogaro da kai, a nan ne alƙawarin samun ‘yanci na gaskiya yake,” inji Yakubu.

Tags: 'yancin kaidogaroTanimu Yakubu
Previous Post

CBN ya yi alƙawarin samar da takardun Naira masu tsafta

Next Post

Gwamnatin Tinubu na ci gaba da tallafa wa manoman Arewa da kayan aikin gona 

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
Gwamnatin Tinubu na ci gaba da tallafa wa manoman Arewa da kayan aikin gona 

Gwamnatin Tinubu na ci gaba da tallafa wa manoman Arewa da kayan aikin gona 

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!