• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya yi alƙawarin samar da takardun Naira masu tsafta

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
October 3, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Yadda tsare-tsaren CBN ke daƙile hauhawar farashi da tsadar rayuwa
Babban Bankin Nijeriya (CBN)

Babban Bankin Nijeriya (CBN)

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi alƙawarin ci gaba da aikin samar da takardun Naira masu tsafta.

Sannan kuma bankin ya ƙara yin kira ga ‘yan Nijeriya su riƙa ɗaukar Naira da daraja, su daina shafa wa takardun kuɗaɗe datti.

Wannan kira da alƙawari ya fito daga bakin Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Hajiya Hakama Ali, a lokacin da take jawabi a Dandalin Baje-kolin Ƙasa da Ƙasa na 20 a ranar Alhamis, a Abuja, Babban Birnin Tarayya.

Hajiya Hakama, wadda ta yi jawabin a Ranar CBN a wurin taron, ta ce “a riƙa yin hada-hada da naira cikin riƙon darajtawa, a daina shafa mata datti. A daina yin liƙi, a daina sayar, a daina duƙunƙune ta, kuma a guji buga jabun kuɗaɗe.

“Sannan muna ƙara yin kira ku zama kyawawan jakadun Bankin CBN masu riƙe Naira da daraja. CBN ba zai iya wannan aiki shi kaɗai ba, sai da gudunmawar ku. Naira ita ce abin alfaharin mu.

“Muna fatan ganin ci gaba da bada haɗin kai daga dukkan masu ruwa da tsaki a harkokin hada-hadar kuɗaɗe. Samun wannan nasara abu ne da sai an haɗa hannu za mu iya shawo kan ƙalubalen saisaita tattalin arziki, domin mu samu ƙasaitacciyar bunƙasa,” inji ta.

Ta ce shugabannin CBN na ta bakin ƙoƙarin shawo kan matsalolin da za a kawar domin bunƙasa yawan kayan da ake sarrafawa a cikin gida da kuma ƙarfafa tattalin arziki.

Ta ce kaiwa ga ƙololuwar arzikin dogaro da kai ga ƙasa abu ne mai buƙatar shika-shikai uku da suka haɗa da, “tsarin harkokin kuɗaɗe mai ƙarfi, ingantacciyar kasuwar hada-hadar musayar kuɗaɗen waje da kuma haɗin gwiwa mai ƙarfi tsakanin ɓangarorin kula da harkokin kuɗaɗe.

“Tuni an fara ganin kyakkyawan sakamako daga ƙoƙarin da CBN ke yi, ta inda har asusun kuɗaɗen waje ya kai Dala biliyan 43.05 tun a ranar 11 ga Satumba, 2025. Wato ya ƙaru daga Dala biliyan 40 ɗin da yake a ƙarshen watan Yuli, 2025.”

Ta ce CBN na ta ƙoƙarin bunƙasa tattalin arziki, yayin da zuwa yanzu manyan bankuna 14 sun cika sharuɗɗan mallakar Naira biliyan 500 a matsayin mafi ƙarancin jari. Ta ce CBN na ci gaba da tabbatar da sauran bankunan sun kammala cika sharuɗɗan cikin nasara.

An fara wannan baje-koli a ranar 25 ga Satumba, kuma za a rufe shi a ranar 6 ga Oktoba.

Tags: CBNHakama AliNaira
Previous Post

Ba cewa na yi na daina takara ba, inji Atiku kan hirar sa da BBC Hausa

Next Post

Shekaru 65 Da ‘Yanci: Iya dogaro da kai shi ne cikakken ‘yanci – Tanimu Yakubu

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Aiki Da Kasafin 2025 Cikin Satumba – Yakubu

Shekaru 65 Da 'Yanci: Iya dogaro da kai shi ne cikakken 'yanci - Tanimu Yakubu

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!