• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

El-Rufai ya rubuta wa Ribaɗu takardar neman ƙarin haske kan zargin shigo da ‘guba mai haɗari’

ALI KANO by ALI KANO
February 15, 2026
in Siyasa
A A
0
El-Rufai ya rubuta wa Ribaɗu takardar neman ƙarin haske kan zargin shigo da ‘guba mai haɗari’
Daga hagu: Malam Nuhu Ribaɗu da Malam Nasir El-Rufai

Daga hagu: Malam Nuhu Ribaɗu da Malam Nasir El-Rufai

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya rubuta takarda zuwa ga Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu, yana neman ƙarin bayani kan rahotannin da ke cewa wai Ofishin NSA ɗin (ONSA) ya sayo kimanin kilo 10 na thallium sulphate, wani sinadari mai matuƙar guba.

A cikin wasiƙar mai taken “Neman Ƙarin Bayani kan Sayo Thallium Sulphate,” El-Rufai ya ce yana ɗaukar matakin ne a matsayin sa na ɗan kasa mai kishin ƙasa, domin neman gaskiya da tabbatar da tsaro dangane da bayanan da ya bayyana a matsayin masu matuƙar muhimmanci da haɗari.

A cewar sa, bayanan da ke hannun wasu shugabannin adawa na siyasa sun nuna cewa an yi zargin sayen sinadarin ne daga wani mai samarwa a ƙasar Poland.

Ya ce: “Saboda gishirin thallium sinadarai ne masu tsananin guba kuma ana kula da su da tsauraran matakai, na yi imanin yana da muhimmanci domin kare lafiyar jama’a, tabbatar da dimokiradiyya, da kuma kiyaye amincewar jama’a a fayyace wasu bayanai.”

Ya lissafo muhimman batutuwa shida da ya nemi a yi masa ƙarin haske a kan su:

  • Manufar shigo da thallium sulphate da yadda za a yi amfani da shi.
  • Sunan mai samar da sinadarin da kuma ko an shigo da shi ne bisa wani izinin sinadarai ko na tsaro da ake da shi a baya.
  • Jimillar adadin sinadarin da aka sayo da kuma irin yanayin sa ko ƙarfin sa.
  • Hanyoyin ajiyewa da tsaron sinadarin bayan ya iso.
  • Kulawar hukumomi da haɗin gwiwa da cibiyoyi masu alhakin kula da lafiyar jama’a da muhalli, ciki har da NAFDAC, NCDC, da sauran hukumomi.
  • Ko an gudanar da kimanta haɗarin lafiyar jama’a ko shirye-shiryen rage haɗari, idan an yi la’akari da tsananin gubar sinadarin.

El-Rufai ya jaddada cewa tambayoyin sa sun fito ne “da kyakkyawar niyya,” kuma manufar sa ita ce tabbatar da bin doka, ƙa’idojin tsaro, da kuma fayyace gaskiya.

Ya ce: “Amintuwar jama’a da sahihancin cibiyoyin ƙasa na ƙara ƙarfi ne idan aka fuskanci duk wata barazana a buɗe kuma aka sarrafa ta yadda ya dace.”

Wannan al’amarin ya zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar ƙarin taƙaddama ta siyasa tsakanin El-Rufai da gwamnati mai ci yanzu.

Idan kun tuna, a wata hira da ya yi da gidan talbijin na Arise, El-Rufai ya zargi Ribaɗu da kitsa wani yunƙuri na kama shi a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Ya ce an sanar da shi wannan zargin ne bayan wata majiya da bai bayyana ba ta ce an yi kutse an saurari wayar Ribaɗu a asirce.

Ya ce: “Gwamnati tana tunanin ita kaɗai ce ke sauraron kiran wayar mutane, amma mu ma muna da hanyoyin mu. Ya yi kiran ya ba da umarni. Wani ya saurari wayar sa. Gwamnati tana sauraron kiran mu ba tare da umurnin kotu ba. Wani ya saurari wayar sa ya gaya mana cewa ya ba da umurnin.”

Waɗannan kalamai sun haifar da muhawara a bainar jama’a kan yadda ake sa ido kan sadarwa, harkokin tsaro na ƙasa, da iyakar ikon ɓangaren zartarwa.

Tsohon gwamnan, wanda ya sha zargin gwamnatin da yi masa farautar siyasa, ya kuma ce zai amsa gayyatar da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta yi masa.

Rahotanni sun nuna cewa an aike masa da gayyatar ne yayin da yake ƙasar waje, kuma ya ce zai bayyana a gaban hukumar a gobe Litinin.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ofishin Ribaɗu dai ba su fitar da wata sanarwa kan wasiƙar ta El-Rufai ba.

Tags: adawagubaNasirElrufaiNuhuRibaduzargi
Previous Post

Tinubu zai kai ziyarar aiki a Yola, zai ƙaddamar da ayyukan gwamnati

Next Post

Shigo da guba: Ofishin Ribaɗu sun musanta zargin El-Rufai, sun ce ya kai shaida ga DSS

Related Posts

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko
Siyasa

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu
Siyasa

Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu

September 10, 2026
Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027
Siyasa

Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027

September 9, 2026
Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2
Siyasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2

September 2, 2026
Zaɓen 2027: Matawalle ya ce zai sama wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20
Siyasa

Zaɓen 2027: Matawalle ya ce zai sama wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20

August 26, 2026
Siyasa

Tinubu ya janye jerin sunayen Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen APC – Rahoto

August 25, 2026
Next Post
El-Rufai ya rubuta wa Ribaɗu takardar neman ƙarin haske kan zargin shigo da ‘guba mai haɗari’

Shigo da guba: Ofishin Ribaɗu sun musanta zargin El-Rufai, sun ce ya kai shaida ga DSS

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!