• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Thursday, May 14, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Nijeriya da Dubai za su karɓi baƙuncin taron Investopia a Legas – Tinubu 

Wakilin Mu by Wakilin Mu
January 13, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Nijeriya da Dubai za su karɓi baƙuncin taron Investopia a Legas – Tinubu 
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana taron jawabi a taron Abu Dhabi Sustainability Week (ADSW) na 2026... yau a birnin Abu Dhabi 

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana taron jawabi a taron Abu Dhabi Sustainability Week (ADSW) na 2026... yau a birnin Abu Dhabi 

Nijeriya da Dubai za su karɓi baƙuncin taron Investopia a Legas – Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Nijeriya za ta karɓi baƙuncin taron Investopia tare da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) a birnin Legas a watan Fabrairu mai zuwa, domin jawo hankalin masu zuba jari daga sassa daban-daban na duniya.

Shugaban ya bayyana haka ne a yau a yayin taron Abu Dhabi Sustainability Week (ADSW) na 2026.

Ya ce shirin zai taimaka wajen bunƙasa jarin da zai tallafa wa cigaban tattalin arziki mai ɗorewa.

A gefen taron, Nijeriya da UAE sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tattalin arziki ta CEPA, wadda ke da nufin zurfafa haɗin gwiwa a fannonin kasuwanci, makamashi, gine-gine, sufurin kayayyaki da kasuwancin zamani na intanet.

Shugaban UAE, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, tare da ministocin ƙasashen biyu, sun halarci sanya hannun kan yarjejeniyar da Tinubu ya bayyana a matsayin abin tarihi da dabarar bunƙasa dangantakar ƙasashen biyu.

Tinubu ya bayyana cewa Investopia zai haɗa masu zuba jari, ‘yan kasuwa, masu ƙirƙire-ƙirƙire da masu tsara manufofi domin mayar da ra’ayoyi zuwa jarin da zai amfani al’umma.

Ya ce Nijeriya na da burin tara kusan dala biliyan 30 a duk shekara domin ayyukan sauyin yanayi da masana’antu masu kare muhalli, yana mai jaddada buƙatar sauya tsarin hadahadar kuɗin duniya domin sauƙaƙa wa ƙasashe masu tasowa samun jari ba tare da nauyin bashi ba.

Shugaban ya kuma yi nuni da gyare-gyaren makamashi da tattalin arziki da gwamnatin sa ke aiwatarwa, ciki har da Dokar Lantarki ta 2023 da kuma manufofin kasuwar man fetur, yana cewa hakan ya ƙara amincewar masu zuba jari.

Ya ƙara da cewa fitar da kayayyakin da ba na mai ba ta ƙaru da kashi 21 cikin 100, tare da alƙawarin cewa Nijeriya a shirye take ta yi aiki da abokan hulɗa domin gina cigaba mai ɗorewa, adalci da amfani ga kowa.

Tags: Abu DhabiADSW 2026Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Previous Post

Amurka ta kawo wa Nijeriya kayan soja domin tsaro

Next Post

Rawar da Babban Bankin Nijeriya ke takawa a tallafin kuɗin noma

Related Posts

Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai

May 12, 2026
Lamiɗo Yuguda, sabon Mataimakin Gwamnan CBN ya shiga ofis
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lamiɗo Yuguda, sabon Mataimakin Gwamnan CBN ya shiga ofis

May 12, 2026
Yadda tsare-tsaren CBN ke daƙile hauhawar farashi da tsadar rayuwa
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙwaƙudumar kasa biyan tulin bashin da manyan bankuna suka bayar laifin daraktoci da manyan masu hannayen jarin su ne, ba laifin CBN ba

May 8, 2026
Tsauraran matakai da ƙa’idojin da CBN ya gindaya, dangane da bashin naira tiriliyan 2.9 da kamfanin Nestoil ya kasa biyan wasu bankunan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tsauraran matakai da ƙa’idojin da CBN ya gindaya, dangane da bashin naira tiriliyan 2.9 da kamfanin Nestoil ya kasa biyan wasu bankunan Nijeriya

May 7, 2026
Manyan nasarorin da CBN ya samu cikin 2025
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Yadda ƙarfin laƙani da dafa’in CBN ke hana girgizar tattalin arzikin duniya yi wa Nijeriya barazana

May 6, 2026
Tinubu ya gana da manyan masu zuba jari na duniya a Paris
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya gana da manyan masu zuba jari na duniya a Paris

May 5, 2026
Next Post
Rawar da Babban Bankin Nijeriya ke takawa a tallafin kuɗin noma

Rawar da Babban Bankin Nijeriya ke takawa a tallafin kuɗin noma

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!