Amurka ta kawo kayan aikin soja ga hukumomin tsaron Nijeriya domin ƙarfafa ayyukan tsaro a wasu sassan ƙasar nan.
An bayyana hakan ne a wani saƙo da Rundunar Sojin Amurka a Afrika (AFRICOM) ta wallafa a shafin X a yau Talata.
“Dakarun Amurka sun miƙa muhimman kayan aikin soja ga abokan hulɗar mu na Nijeriya a Abuja. Wannan miƙawar na tallafa wa ayyukan da Nijeriya ke ci gaba da yi tare da jaddada haɗin gwiwar mu ta tsaro,” inji saƙon.
Gwamnatin Tarayya ta ce gwamnatin Amurka ta tabbatar da shirin ta na zurfafa haɗin gwiwar tsaro da Nijeriya, ciki har da samar da ingantaccen tallafin bayanan sirri, kayan tsaro da sauran kayayyaki domin ƙarfafa ayyukan da ake yi na yaƙi da ’yan ta’adda da ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi a ƙasar nan.
A watan Nuwamban da ya gabata, gwamnatin ta aika wata tawaga zuwa birnin Washington da nufin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu da kuma buɗe sababbin hanyoyin haɗin kai.
Tawagar, wadda Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro na Ƙasa (NSA), Nuhu Ribaɗu, ya jagoranta, ta gana da manyan jami’ai a Majalisar Dokokin Amurka, da Ofishin Addini na Fadar White House, da Ma’aikatar Harkokin Waje, da Majalisar Tsaron Ƙasa, da kuma Ma’aikatar Tsaro.
Membobin tawagar sun haɗa da Babban Lauyan Tarayya, Lateef Fagbemi; Babban Hafsan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede; Babban Hafsan Leƙen Asirin Tsaro, Laftanar Janar Emmanuel Undiandeye; Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun; da wakilai biyu daga Ofishin NSA.
A yayin taron, tawagar Nijeriya ta musanta zargin kisan ƙare dangi da aka ce ana yi a Nijeriya, tana jaddada cewa hare-haren tashin hankali na shafar iyalai da al’umma ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba.
Haka kuma, ta yi watsi da yadda ake karkatar da bayanin halin da ake ciki, tana cewa irin wannan bayani zai ƙara raba ’yan Nijeriya ne kawai tare da gurɓata gaskiyar abin da ke faruwa a ƙasa.
“Tattaunawar ta ba da dama mai yawa wajen gyara kuskuren fahimta game da Najeriya, ta samar da haɗin gwiwa mai ma’ana da Amurka bisa neman mafita, ta ƙarfafa amincewa tsakanin ɓangarorin biyu, tare da inganta tsari na bai ɗaya wajen kare al’umma masu rauni, musamman a yankin Midil Bel,” inji sanarwar da kakakin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar.
A cewar Onanuga, ƙasashen biyu sun amince da aiwatar da tsarin haɗin gwiwa wanda ba ya ɗaurewa doka, tare da kafa Ƙungiyar Aiki ta Haɗin Gwiwa (Joint Working Group) domin tabbatar da tsari guda da haɗin kai a fannoni da aka amince da su.
Ya ce a nasu ɓangaren, tawagar Nijeriya ta sake tabbatar da ƙudirin gwamnati na ƙarfafa matakan kare fararen hula.
“Gwamnatin Tarayya na sake jaddada sanin ta game da ƙaruwa da damuwa kan ’yancin addini da tsaro, tare da ƙarfafa ’yan ƙasa su kwantar da hankalin su cewa ana ɗaukar matakai masu ƙarfi, gaggawa, kuma masu haɗin kai domin tabbatar da tsaron ƙasa.
“Haka kuma, Amurka ta bayyana shirin ta na bayar da tallafi na ƙarin taimako, ciki har da agajin jinƙai ga al’ummomin da abin ya shafa a Midil Bel, da kuma tallafin fasaha domin ƙarfafa hanyoyin gargaɗin wuri,” inji Onanuga.







