1. Kare darajar Naira a kasuwar hadahadar musayar kuɗaɗen waje.
2. Sa-ido kan bankuna domin tabbatar da suna bin ƙa’idoji da sharuɗɗan da CBN ya gindaya masu.
3. Rangadin wayar da kan jama’a kan illar wulaƙanta Naira.
4. Kawar da wahalhalun hadahadar kuɗaɗe a ƙarshen shekara.
5. Soke lasin bankuna biyu – Aso Savings and Loans Plc da Unions Homes Saving Loans Plc.
6. Bijiro wa cibiyoyin hadahadar POS hanyoyin magance yawan tangarɗar tura kuɗaɗe.
7. Kaddamar da Kwamitin Asusun Bada Bashi ga Manoma (ACGSF)
8. Sabunta wa BDC 82 rajistar iznin sana’ar canjin kuɗaɗen waje.
9. Matsa-lamba kan dokar ƙarfafa yawan jarin bankuna.
10. Ƙara adadin kuɗaɗen da za a iya cira da ATM.
11. Umartar bankuna su mayar wa waɗanda aka zambace ta ‘APPs’ kuɗaɗen su cikin sa’o’i 48.
12. Ceto tattalin arzikin Nijeriya
13. Dokar bankuna su janye talloli masu ɗauke da salo da sigar yaudarar kwastomomi.
14. Dokar hukunta masu rubuta cakin kuɗi na bogi.
15. Hana tashin farashin kayan abinci.
16. Gindaya sabbin ƙa’idojin amfani da POS.
17. Gargaɗin a yi kaffa-kaffa da ‘Zuldar Microfinance Bank’ .
18. Ƙaddamar da Shirin Daƙile Tsadar Rayuwa (DGAS).
19. Tallabar tattalin arzikin Nijeriya a lokacin da farashin ɗanye mai ke faɗuwar-‘yan-bori.
20. Wanzar da daidaiton farashin kayan abinci daidai da aljihun talaka.






