• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Majalisar Wakilai ta gayyaci Matatar Ɗangote da NMDPRA kan rikicin man fetur

ALI KANO by ALI KANO
December 16, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Majalisar Wakilai ta gayyaci Matatar Ɗangote da NMDPRA kan rikicin man fetur
Zauren Majalisar Wakilai ta Tarayya

Zauren Majalisar Wakilai ta Tarayya

Kwamitin Haɗin Gwiwa na Majalisar Wakilai kan Albarkatun Man Fetur ya gayyaci Matatar Ɗangote da Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur na Cikin Teku (NMDPRA) domin warware saɓanin da ke barazana ga ɓangaren man fetur na Cikin teku.

Shugaban kwamitin, Ikenga Ugochinyere, shi ne ya bayyana haka bayan wani taron gaggawa da aka gudanar a Abuja ranar Litinin, inda ya ce tashin hankalin da ke ƙaruwa na iya lalata daidaiton da aka samu kwanan nan.

Ya ce dole ne kwamitin ya ɗauki mataki cikin gaggawa, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin daidaita samarwa, farashi da tsari a sabon tsarin harkokin man fetur na Nijeriya bayan cire tallafin mai.

Ya ce: “Babban batun shi ne sabon rikicin da ya taso sakamakon damuwa da zarge-zargen da Alhaji Aliko Ɗangote ya gabatar kan NMDPRA.

“Muna kare daidaiton da aka samu da ƙyar; samun mafita mai ɗorewa na buƙatar gano muhimman matsaloli, shi ya sa muka gayyaci Ɗangote da shugabannin NMDPRA.”

Daga hagu: Alhaji Aliko Ɗangote da Shugaban NMDPRA, Injiniya Farouk Ahmed

Ya ƙara da cewa ƙorafe-ƙorafen da aka karɓa sun shafi bayar da lasisin shigo da mai da kuma ko matatun mai na cikin gida za su iya biyan buƙatar man fetur ta kullum a Nijeriya.

Ugochinyere ya ce za a binciki dukkan batutuwan da suka rage lokacin da masu ruwa da tsaki a harkokin tace mai da kula da tsari suka bayyana a gaban kwamitin.

Tags: Aliko DangoteFarouk AhmedfeturIkenga UgochinyereMajalisar Wakilaimatatun maiƊangote
Previous Post

CBN ya soke lasin bankuna biyu bayan sun karya ƙa’ida da kasa cika sharuɗɗa

Next Post

Dalilin da ya sa Buhari ya kasa rabuwa da Mamman Daura – Fatima Buhari

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post
Dalilin da ya sa Buhari ya kasa rabuwa da Mamman Daura – Fatima Buhari

Dalilin da ya sa Buhari ya kasa rabuwa da Mamman Daura – Fatima Buhari

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!