• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya soke lasin bankuna biyu bayan sun karya ƙa’ida da kasa cika sharuɗɗa

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
December 16, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
CBN ya soke lasin bankuna biyu bayan sun karya ƙa’ida da kasa cika sharuɗɗa
Tamburan bankunan da aka soke wa lasisin

Tamburan bankunan da aka soke wa lasisin

Babban Bankin Najeriya (CBN), ya sanar da gaggauta soke lasin gudanar da hadahadar bayar da rancen gina gidaje da jingina na ‘Aso Savings and Loans Plc’ da kuma ‘Union Homes Savings and Loans Plc’.

Wannan mataki dai wani yunƙuri ne na ƙarfafa sashen Bankunan Gidaje da kuma tabbatar da bin ƙa’idojin banki.

Kamar yadda wata sanarwa da Daraktar Yaɗa Labarai da Sadarwa ta CBN mai riƙo, Hajiya Hakama Ali, ta wallafa a shafin X na bankin a ranar Talata, CBN ya bayyana cewa bankunan sun karya wasu tanade-tanade na Dokar Bankuna da Sauran Cibiyoyin Kuɗi (BOFIA) ta 2020 da kuma Sabbin Ka’idojin Gudanar da Bankunan Gidaje a Nijeriya.

A kan haka ne Hakama ta ce CBN ya soke lasin domin hakan na daga cikin ci gaba da ƙoƙarin CBN na tabbatar da tsaro da ingancin tsarin banki, kare ajiyar kuɗin abokan hulɗa, da tabbatar da cewa bankuna masu ƙarfi ta fuskar kuɗi kaɗai ke aiki a kasuwar bankunan gidaje.

“Daga cikin laifuffukan da aka gani a fili, akwai gaza cika mafi ƙarancin kuɗin hannun jari da aka tanada, rashin isassun kadarori da za su rufe basussuka, kasancewa cikin matsanancin ƙarancin jari inda ƙimar wadatar jari ta faɗi ƙasa da abin da doka ta tanada, da kuma rashin bin umarnin da CBN ta bayar,” inji bankin.

Daga nan CBN ya jaddada cewa wannan mataki ya dace da aikin sa na tabbatar da daidaito da kwanciyar hankali a tsarin kuɗin ƙasa da kuma kare amincewar jama’a ga sashen banki.

Daraktar Sadarwar ta sake tabbatar da ƙudirin CBN na gina tsarin kuɗi mai ƙarfi da nagarta a Nijeriya.

Bankunan gidaje su ne cibiyoyin kuɗi da ke bayar da rancen sayen gida da sauran kayayyakin tallafin gidaje, kuma CBN na sanya musu tsauraran ƙa’idoji domin kare abokan hulɗa da tabbatar da kwanciyar hankalin tsarin kuɗi Nijeriya.

Tags: Aso Savings and Loans PlcbankunaCBNlasisiUnion Homes Savings and Loans Plc
Previous Post

Bankwana da 2025: Yadda tsare-tsaren CBN ya saukar da malejin hauhawar farashi zuwa kashi 14.45 a ƙarshen shekara

Next Post

Majalisar Wakilai ta gayyaci Matatar Ɗangote da NMDPRA kan rikicin man fetur

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post
Majalisar Wakilai ta gayyaci Matatar Ɗangote da NMDPRA kan rikicin man fetur

Majalisar Wakilai ta gayyaci Matatar Ɗangote da NMDPRA kan rikicin man fetur

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!