• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Kotu ta hana Hadiza yi wa tsohon minista Kabiru Turaki zargin ɗirka mata cikin  shege

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
September 17, 2025
in Labarai
A A
0
Kotu ta hana Hadiza yi wa tsohon minista Kabiru Turaki zargin ɗirka mata cikin  shege
Hadiza Musa Baffa da Kabiru Turaki

Hadiza Musa Baffa da Kabiru Turaki

Babbar Kotun Yanki (Upper Area Court) da ke Abuja ta dakatar da wata mai suna Hadiza Musa Baffa daga gabatar da shaidar gwajin jinin ɗan ta, wanda ta yi iƙirarin cewa tsohon Ministan Ayyukan Musamman, Kabiru Tanimu Turaki, shi ne ya ɗirka mata cikin da ta haifi yarinya ba ta hanyar aure ba.

Mai Shari’a Adamu Isah ne ya yanke hukuncin a ranar 4 ga Satumba, inda ya ƙi amince wa Hadiza ta yi amfani da wani gwajin ƙwayoyin halittar da ita da lauyan ta suka yi, wato DNA, mai nuna cewa “tabbas ɗan na Kabiru Turaki ne”.

Alƙalin ya ce, “Kotu ta haramta maki, ke Hadiza Musa Baffa, cewa kada ke ko wani naki, makusantan ki, ejan ɗin ki, ko wani wakilin ki ya buga ko ya wallafa bayani, hoto, furuci ko wata alama a jaridu ko a soshiyal midiya mai nuna cewa ‘yar da kika haifa ba ta hanyar aure ba ta Kabiru Turaki ce.”

Turaki ne dai ya shigar da ƙara cewa yana roƙon kotun da ta hana Hadiza da iyayen ta su riƙa amfani da ‘yan sanda suna takura masa kan cewa sai ya amince shi ne ya yi mata cikin da ta haifi ‘yar.

Sauran waɗanda ya maka a kotun sun haɗa da mahaifin Hadiza, Musa Baffa, da mahaifiyar ta, Uwani Arabi, da kuma ‘yan sanda.

Hadiza dai ta yi zargin cewa Turaki ya watsar da ita bayan ya ɗirka mata cikin shege.

Wannan rigima dai ba sabuwa ba ce, domin tun cikin 2024 aka fara tafka ta a Babbar Kotun Tarayya, Abuja, inda lauyan Turaki mai suna Abdul’aziz Ibrahim ya shigar da ƙara cewa bai yarda da yadda ‘yan sanda suka tilasta wa Turaki har aka ɗebi jinin sa domin a yi gwaji ba bisa ƙa’ida ba.

Ya shaida wa kotu cewa ta bada umurnin haramcin gwajin da aka yi masa, kuma ta hana Hadiza Baffa alaƙanta ‘yar da ta haifa da Turaki.

Lauya ya shaida wa kotu cewa ‘yan sandan FCIB da ke hedikwatar su ta Area 10 Garki, sun gayyaci Turaki ya je a ranar 5 ga Nuwamba, 2024, inda suka tsare shi tsawon sa’o’i shida.

“Sun hana shi fita, suka shigo da wani likitan da bai yarda da shi ba, suka ɗebi jinin sa domin yin gwajin DNA. Daga nan suka shigar da ƙara a kan sa a wata Kotun Majistare a Abuja.”

Ya shaida wa kotun cewa ‘yan sanda sun danne masa haƙƙi.

To a ranar 18 ga Fabrairu, 2025, Mai Shari’a Inyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya, Abuja, ya yanke cewa ba zai yanke hukunci ba sai ya ji ta ɓangaren waɗanda Turaki ke ƙara, wato Hadiza, iyayen ta da kuma ‘yan sanda.

Asalin Rigimar:

Cikin Satumba 2024 ne dai wannan bahallatsa ta auka wa tsohon minista Kabiru Turaki, inda ya garzaya kotu ya ƙaryata ƙorafin Hadiza.

Rahotanni a lokacin sun bayyana cewa Turaki, wanda babban lauya ne, ya ƙaryata ƙorafin Hadiza a Babbar Kotun Yanki da ke unguwar Kado a Abuja, ya nemi ta hana ‘yan sanda binciken tankiyar haƙƙin mallakar jinjirin da ake zargin shi ne ya ɗirka wa wata ɗalibar ciki, ta haifi yarinya.

Kotun ta hana ‘yan sanda bincike, domin shari’a tana gaban ta, sai ta yanke hukunci tukunna.

Mai Shari’a Ahmadu ya umurci Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Nijeriya da dukkan jami’an sa kada su karɓi duk wani ƙorafi daga Uwani Arabi da mijin ta Musa Baffa da kuma ‘yar su, Hadiza Baffa.

Kotun ta ce tunda maganar tana kotu, babu sauran wani bincike da ‘yan sanda za su yi, sai dai a jira hukunci daga kotun kawai.

Mai Shari’a ya bada umurnin ne bayan lauyan Turaki ya shigar da ƙorafi a ranar 2 ga Satumba.

Turaki dai ya jaddada wa kotun cewa ba shi ne ya ɗirka wa Hadiza ciki ba.

Ya yi zargin cewa Hadiza tana da wani saurayi, wanda ke kwana da ita, kuma shi ne ya ɗirka mata ciki.

Haɗuwar Alaƙaƙai:

Turaki ya shaida wa kotu cewa a wani lokaci a cikin 2016, Uwani wadda ya sani tun a Kano kafin ta kai ga auren Musa, ta kira shi a waya, inda ta nemi shawarar sa kan shirin da take yi na cire ‘yar ta Hadiza daga Jami’ar Maiduguri saboda fitintinun Boko Haram.

Ya ce ya shawarce ta da ta nema wa ‘yar Jami’ar Bayero ta Kano, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo ta Sokoto, ko kuma Jami’ar Ilorin.

Ya ce bayan makonni da yin wannan magana, sai Uwani ta kira shi ta ce tana neman alfarmar ya kama mata masauki ita da ‘yar ta, za su shigo Abuja tare, shi kuma ya yi mata wannan alfarma, inda ya kama masu wurin sauka a masaukin baƙi na Ideal Guest House, wanda ke Garki.

Ya ce a Abuja, Uwani ta samar wa ‘yar ta Hadiza gurbin karatu a Jami’ar Baze har ma ya ba su tallafin naira miliyan 1 domin kuɗin yin rajistar sabon ɗalibi naira miliyan 3 ne a lokacin.

Turaki ya ce Uwani ta roƙe shi da cewa tana so ya zama ubanɗakin Hadiza, wato ta damƙa masa amanar ‘yar ta kenan.

Turaki ya ce shi ya ci gaba da ɗaukar ɗawainiyar karatun Hadiza da sauran haƙƙoƙin kyautatawa na kula da ita. Ya ce to ya yi mamaki ƙwarai da ya gano Hadiza ta saka sunan sa a matsayin sunan baban ta, wato ta koma Hadiza Turaki, da haɗin bakin mahaifiyar, ba da sanin sa ba.

Ya ce da ya ga lamarin aika-aikar Hadiza ya wuce makaɗi da rawa, sai ya kore ta kuma ya umurci ma’aikatan ofishin sa da cewa kada su sake bari ta je ofishin sa.

Ya yi zargin cewa bayan ya kore ta, bayan kamar wata ɗaya ko fin wata ɗaya, sai Uwani ta kira shi a waya, ta ce tana so ta gan shi.

Ya ce a ganawar sa da Uwani, ta shaida masa cewa an yi wa Hadiza cikin shege, kuma ta ce shi ne ya ɗirka mata shi.

Turaki ya ce nan take ya ce ba shi ba ne, suna dai so ne su ƙala masa sharri.

Ya yi zargin cewa mahaifin Hadiza, Malam Musa, wanda ya ce ya watsar da ‘yar sa tsawon shekaru 28, ya kira shi cikin watan Mayu, dangane da maganar cikin na ‘yar sa.

‘Turaki Ne Ya Ɗirka Wa ‘Yar Mu Ciki’

A nasu bayanin a kotu, wanda sun shaida a rubuce a madadin su uku, sun ce duk bayanan da Turaki ya yi wa kotu, ƙarya ya shirga, bai faɗi gaskiyar abin da ya faru ba.

Hadiza da Uwani sun ce shi tsohon Ministan ne da kan sa ya nemi zai taimaka masu ya saka Hadiza a Jami’ar Baze, kuma ya ce zai ɗauki nauyin karatun ta da wurin kwanan ta, kuma zai riƙe ta amana tamkar ‘yar cikin sa.

Sun ce shi ne da kan sa ya zaɓi zai saka ta a Baze, ba su ne suka zaɓi jami’ar ba.

Suka ce lokacin da ta shiga jami’ar kuɗin rajista Naira 950,000 ne, kuma shi ya ba ta dala 2,000 don ta yi rajista.

Uwani ta ce ba ta roƙi Turaki ya zama uban riƙon Hadiza ba, shi ne da kan sa ya ce zai zama, ashe ba ta sani ba ya yi haka ne don ya riƙa lalata da ‘yar ta.

Uwani ta ce Turaki ya yi wa kotu ƙarya da ya ce ta roƙi ya bai wa ‘yar ta mota.

Ta ce ya kira ta ta je ofishin sa da ke Titin TY Ɗanjuma a Asokoro, Abuja. Tana zuwa mamaki ya kama ta, ganin yadda aka damƙa mata takardun mota, mai ɗauke da sunan “HADIZA TURAKI.” Ta ce aka nuna mata mota samfurin Toyota Almera.

‘Shi Ne Ya Maida Ni Hadiza Turaki’

Hadiza ta ce Turaki ne ya maida sunan ta “Hadiza Turaki” a takardun motar da ya sai mata da kuma sunan asusun bankin ta a Bankin GT, inda yake tura mata kuɗaɗe ta hannun mai kula da asusun sa na bankin.

Ta ce ta samu matsala da karatun ta, kuma ta shiga halin tarangahuma sanadiyyar amfani da ita da tsohon ministan ya riƙa yi.

Ta ce ya sha zuwa makaranta ya kai mata ziyara, yana ɗaukar ta yana kwanciya da ita, amma ba da son ran ta ba.

Ta ce Turaki ya sha yi mata barazanar cewa kada ta kuskura ta shaida wa iyayen ta cewa yana lalata da ita. Ta ce wannan tsaka-mai-wuya da ya jefa ta ne ya haifar mata dalilin samun matsalar kasa ci gaba da karatu.

Ta ce yayin da ya lura tana cikin damuwa, sai ya yi ta yi mata alƙawarin zai aure ta, har ya riƙa tura mata saƙonnin soyayya ta WhatsApp, ita ma tana tura masa.

Ta ce lokacin da ta sanar da shi tana da ciki, ya yi ta ƙoƙarin ba ta shawarar ta zubar da cikin.

Ta ce ta zaɓi ta haihu bayan an ba ta shawarar gara ta haifi abin ta, idan aka yi la’akari da haɗarin da ke tattare da zubar da ciki. Ta ce ya fusata sosai da ya ga ta ƙi zubar da cikin.

Ta shaida wa kotu cewa ta haihu a ranar 3 ga Afrilu, 2023. “Kuma yayin da ya kalli jinjirar ya ga lallai ta yi kama da shi, kamar kwabo-da-kwabo, sai ya ce lallai ‘yar sa ce,” inji ta.

Ta kuma yi iƙirarin cewa shi ya biya kuɗin kwanciyar ta naƙuda, zuwa awon ciki, haihuwa da sauran ɗawainiyar maijego da jinjira a Asibitin Nizamiyye da ke Abuja.

Kotu ta ɗage sauraren shari’ar zuwa ranar 24 ga Satumba, 2024.

To bayan shekara ɗaya dai kotun ta yanke hukunci a makon da ya gabata.

Previous Post

Hukumar Kwastam ta dakatar da aiwatar da harajin kashi 4 cikin ɗari na kayan da ake shigo da su bisa umarnin Ma’aikatar Kuɗi 

Next Post

Gwamnatin Tarayya ta fara aikin samar da lantarki daga hasken rana a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano

Related Posts

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista
Siyasa

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista

May 5, 2026
Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya: Nijeriya na neman a haɗa gwiwa a yaƙi masu yaɗa labaran ƙarya
Labarai

Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya: Nijeriya na neman a haɗa gwiwa a yaƙi masu yaɗa labaran ƙarya

May 4, 2026
Kwankwaso da Obi sun koma NDC
Siyasa

Kwankwaso da Obi sun koma NDC

May 3, 2026
Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi
Siyasa

Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi

May 3, 2026
Shettima ya ƙaddamar da jigilar maniyyatan Hajjin bana da kwashe alhazai 500 a Abuja
Labarai

Shettima ya ƙaddamar da jigilar maniyyatan Hajjin bana da kwashe alhazai 500 a Abuja

May 3, 2026
Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC
Siyasa

Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC

May 1, 2026
Next Post
Gwamnatin Tarayya ta fara aikin samar da lantarki daga hasken rana a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano

Gwamnatin Tarayya ta fara aikin samar da lantarki daga hasken rana a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!