Wasu daga cikin al’ummar Jihar Nasarawa sun bayyana jin daɗin su da ayyukan raya ƙasa da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa, suka ce ayyukan suna taimakawa wajen inganta rayuwar su da bunƙasa harkokin tattalin arziki a jihar.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da bayyana ayyukan raya ƙasa da gwamnatin Tinubu take aiwatarwa a sassa daban-daban na Nijeriya.
A wani rangadi da wasu wakilan kafafen yaɗa labarai suka kai Jihar Nasarawa, tawagar ta duba wasu muhimman ayyukan more rayuwa da shirye-shiryen bunƙasa tattalin arziki, domin gani da idon ta tare da tantance yadda suke tasiri ga rayuwar al’umma.
Tawagar, wadda ta samu rakiyar wakilan Fadar Shugaban Ƙasa, ƙarƙashin jagorancin Hadimin Shugaba Tinubu kan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa, Bayo Onanuga, da Hadimin Shugaban Ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labarai, Abdulaziz Abdulaziz, da Dada Olusegun da sauran jami’ai, ta ziyarci wurare daban-daban da ake gudanar da ayyukan raya ƙasa.
Daga cikin wuraren da tawagar ta ziyarta akwai cibiyoyin koyar da sana’o’in hannu, waɗanda ake aiwatar da su ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Tinubu tare da haɗin gwiwar gwamnatin Jihar Nasarawa, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Injiniya Abdullahi A. Sule.

Daga cikin wuraren da tawagar ta ziyarta akwai katafariyar Sakatariyar Gwamnatin Jihar Nasarawa, wadda ke daga cikin manyan gine-ginen gwamnati da ake amfani da su wajen inganta ayyukan gudanar da mulki da samar da kyakkyawan yanayi ga ma’aikatan gwamnati da al’umma.
Tawagar ta duba wasu manyan hanyoyi, ciki har da hanyar Shabu, wadda ke da muhimmiyar alaƙa da zirga-zirgar jama’a da harkokin kasuwanci zuwa wasu sassan jihar da kuma hanyar Taraba.
A cewar mazauna yankunan da aka ziyarta, irin waɗannan ayyuka na taimakawa wajen rage wahalhalun sufuri, tare da buɗe sabbin damarmaki na kasuwanci da zuba jari.
Wata muhimmiyar cibiyar da tawagar ta ziyarta ita ce cibiyar koyar da walda da sauran sana’o’in hannu, wadda aka samar domin bai wa matasa damar koyon sana’o’i da dogaro da kan su.
An bayyana cewa irin waɗannan shirye-shirye na da matuƙar muhimmanci wajen rage zaman kashe wando tsakanin matasa, tare da ba su damar zama masu amfani ga kan su, iyalan su da al’umma baki ɗaya.
Shugaba Tinubu, tare da haɗin gwiwar gwamnatin Jihar Nasarawa, na ƙoƙarin ƙara saka jari a fannin ƙarfafa matasa da samar da hanyoyin dogaro da kai, musamman ta hanyar koyar da sana’o’i da bunƙasa ƙananan masana’antu.
Tawagar ta kuma kai ziyara wasu yankunan da ambaliyar ruwa ta taɓa, inda aka gudanar da ayyukan gyaran manyan kwalbatoci da magudanan ruwa domin rage barazanar ambaliya da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Daga cikin wuraren da aka duba akwai yankin Hanyar Lafiya zuwa Doma, da kuma Gadar Kilema da ke cikin birnin Lafiya, inda ake ganin ayyukan gyaran ababen more rayuwa sun taimaka wajen inganta zirga-zirga da sauƙaƙa rayuwar mazauna yankunan.
Mazauna yankunan da tawagar ta ziyarta sun bayyana farin cikin su kan ayyukan da ake gudanarwa, inda suka ce inganta hanyoyi, magudanan ruwa, samar da sana’o’i da sauran ayyukan more rayuwa na taimakawa wajen sauƙaƙa rayuwar su.
Wasu daga cikin su sun ce suna fatan ayyukan za su ci gaba da yaɗuwa zuwa sauran sassan jihar, domin ƙarin jama’a su amfana.
Abin da tawagar ta gani a yayin ziyarar ya nuna cewa wasu yankunan Arewa na samun ƙarin ayyukan more rayuwa da shirye-shiryen bunƙasa tattalin arziki.
Masu goyon bayan gwamnatin Shugaba Tinubu na kallon waɗannan ayyuka a matsayin wani ɓangare na shirin sabunta ababen more rayuwa da ƙarfafa tattalin arzikin yankunan Arewa.
A ra’ayin su, irin waɗannan matakai na iya taimakawa wajen sauya yanayin cigaban Arewa, daga matsalolin da suka daɗe suna addabar yankin zuwa wani sabon yanayi na ci gaba mai ɗorewa.
Sai dai, burin da ake nunawa shi ne ganin an faɗaɗa irin waɗannan ayyuka zuwa sauran sassan Arewa, domin samar da cigaba mai ɗorewa, ƙarfafa tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma.
A Nasarawa, abin da ya fi bayyana yayin ziyarar shi ne yadda haɗin gwiwar Gwamnatin Tarayya da gwamnatin jihar ke mayar da wasu muhimman shirye-shiryen raya ƙasa zuwa ayyukan da jama’a za su iya gani da idon su kuma su amfana da su.







