Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya amince da sakin Naira biliyan 1.5 domin biyan garatutin ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya, da kuma garatutin iyalan ma’aikatan da suka rasu.
Wannan mataki ya sake nuna aniyar gwamnatin Bago na kula da jin daɗin ma’aikata da masu ritaya, tare da tabbatar da cewa waɗanda suka sadaukar da rayuwar su wajen yi wa jihar hidima sun samu haƙƙoƙin su cikin adalci da mutunci.
Gwamnatin ta ce kuɗin zai taimaka wajen rage wa dubban masu ritaya da iyalan ma’aikatan da suka rasu wahalhalun da suke fuskanta, musamman sakamakon jinkirin biyan haƙƙoƙin su.
Haka kuma, matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na cika alƙawurran da ta ɗauka tare da inganta walwalar ma’aikata, masu ritaya da iyalan su.
Masu ruwa da tsaki sun yaba da matakin, inda suka bayyana shi a matsayin wani muhimmin ci gaba wajen magance matsalolin garatuti da kuma tabbatar da cewa tsofaffin ma’aikatan gwamnati da iyalan waɗanda suka rasu sun samu haƙƙoƙin su.







