• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Tinubu na so malamai su yi amfani da matsayin su wajen yaƙi da ta’addanci

ALI KANO by ALI KANO
August 9, 2026
in Labarai
A A
0
Tinubu na so malamai su yi amfani da matsayin su wajen yaƙi da ta’addanci
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, yana isar da saƙon Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a wajen babban taron Mauludin Shehu Ahmad Al-Tijjani (RTA) yau Lahadi a Kano

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, yana isar da saƙon Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a wajen babban taron Mauludin Shehu Ahmad Al-Tijjani (RTA) yau Lahadi a Kano

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci malaman addini a Nijeriya, Afrika da sauran sassa na duniya da su ci gaba da amfani da muryoyin su wajen yaƙi da ta’addanci, garkuwa da mutane da amfani da addini wajen haddasa kisa da tashin hankali.

Shugaban ya ce babu wata ibada ta gaskiya da za ta samu karɓuwa ta hanyar zubar da jinin mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

Tinubu ya yi wannan kiran ne a yau Lahadi a Kano, cikin saƙon fatan alheri da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya isar a madadin sa a wajen babban taron Mauludin Shehu Ahmad Al-Tijjani (RTA).

Ya ce malaman addini suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen wayar da kan matasa, koyar da zaman lafiya, ilimin addini da kyawawan ɗabi’u, tare da yin kira ga shugabannin siyasa da su gudanar da mulki bisa adalci da tausayi.

Shugaban Ƙasar ya ce ƙalubalen da duniya ke fuskanta, waɗanda suka haɗa da yaƙe-yaƙe, matsin tattalin arziki, yunwa, ta’addanci da rikice-rikicen da ake haddasawa da sunan addini ko ƙabilanci, sun ƙara tabbatar da muhimmancin rawar da shugabannin addini za su taka wajen samar da zaman lafiya.

A cewar sa, ɗariƙar Tijjaniyya, saboda faɗin hanyoyin sadarwar ta a Yammacin Afrika da Arewacin Afrika, tana da babbar dama wajen taimakawa wajen sasanta rikice-rikice, yaƙi da tsattsauran ra’ayi da kuma jagorantar matasa zuwa kyawawan ɗabi’u da tsarkin zuciya.

Tinubu ya bayyana Nijeriya a matsayin ƙasa mai matuƙar muhimmanci ga zaman lafiyar yankin, saboda matsayin ta a tsakanin Yammacin Afrika, yankin Sahel, Tafkin Chadi da Tekun Gini.

Ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da kare ’yancin ’yan Nijeriya na gudanar da addinin su, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da malaman addini da sarakunan gargajiya domin tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da mutunta juna.

Shugaban ya kuma yi ta’aziyyar rasuwar marigayi Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, yana mai cewa rashin sa ya yi matuƙar tasiri a wajen taron.

Tinubu ya bayyana mariganyin a matsayin malami, uba kuma mai fafutukar zaman lafiya da kyakkyawar fahimta.

Ya ce hanya mafi kyau ta girmama Shehun ita ce a ci gaba da gadon ilimin Alƙur’ani da ya bari, tare da koyar da kyawawan ɗabi’u, bautar Allah, zaman lafiya da kuma kula da jin daɗin al’ummar da ya bari a baya.

Tags: addiniKanoMauludiSanata George AkumeShehu Ahmad Al-Tijjani (RTA)Shugaba Bola Ahmed TinubuTijjaniyya
Previous Post

Jama’ar Nasarawa sun yaba a wa Tinubu kan ayyukan raya ƙasa

Next Post

Burkina Faso ta ragargaji Flying Eagles da ci 4-1, ta katse mafarkin Nijeriya na zuwa gasar Kofin Duniya na U-20

Related Posts

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya
Labarai

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya

September 29, 2026
Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
Next Post
Burkina Faso ta ragargaji Flying Eagles da ci 4-1, ta katse mafarkin Nijeriya na zuwa gasar Kofin Duniya na U-20

Burkina Faso ta ragargaji Flying Eagles da ci 4-1, ta katse mafarkin Nijeriya na zuwa gasar Kofin Duniya na U-20

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!