Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kan ta ta Ƙasa (INEC) ta cire sunayen ’yan takarar gwamna na kam’iyyar PDP a jihohin Gombe da Ogun daga jerin sunayen ƙarshe na ’yan takarar zaɓen gwamnonin jihohin da za a gudanar a shekarar 2027.
Sheikh Isa Ali Pantami, wanda kwanan nan ya lashe sabon zaɓen fitar da ɗan takarar gwamna na PDP a Gombe, bai bayyana a jerin sunayen jihar ba. Haka kuma Ladi Adebutu, ɗan takarar gwamna na PDP a Ogun, da mataimakin sa ba su bayyana a cikin jerin sunayen ’yan takarar jihar ba. Babu ɗan takarar PDP a cikin kowanne daga cikin jerin sunayen biyu.
A Gombe, jerin sunayen ya ƙunshi ’yan takara 16, inda aka bayyana Jamil Gwamna a matsayin ɗan takarar APC, tare da Balah Adams a matsayin mataimakinsa. Jerin sunayen Jihar Ogun ya ƙunshi ’yan takarar gwamna 13, inda aka bayyana Solomon Adeola a matsayin ɗan takarar Jam’iyyar APC, tare da Kudirat Balogun a matsayin mataimakiyar sa.
Kowane jerin sunaye ya ƙunshi sunayen ’yan takara, jam’iyyun su, sunayen mataimakan su, shekarun su, jinsin su da cancantar karatun su, tare da ƙarin bayanai a inda ya dace. Sai dai, babu wani daga cikin takardun biyu da ya bayyana dalilin cire ’yan takarar PDP da mataimakan su.







