Shugaba Bola Tinubu ya buƙaci Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, da ɗaukacin Masarautar Katsina da su ƙara ƙaimi wajen yi wa Nijeriya addu’ar samun zaman lafiya, haɗin kai, tsaro da wadata.
Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Siyasa da Sauran Al’amura, Alhaji Ibrahim Kabir Masari, ne ya isar da saƙon Shugaban Ƙasar yayin ziyarar girmamawa da tawagar shugaban ƙasar ta kai wa Sarkin a fadar sa, bayan gudanar da bikin ɗaurin auren ’ya’yan sa maza uku a Katsina ranar Asabar.
Masari ya halarci bikin tare da tawagar Shugaban Ƙasa, wadda ta haɗa da Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, wanda ya wakilci Tinubu a wajen bikin, tare da kasancewa waliyyin aure ga angwayen uku, Usman Abdulmumini Kabir, Dikko Abdulmumini Kabir da Umar Abdulmumini Kabir.
An gudanar da bikin ɗaurin auren a Babban Masallacin Sarkin Katsina, inda jami’an gwamnati, malaman addini da sauran manyan baƙi suka halarta.
A yayin ziyarar fadar, Masari ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa yana matuƙar godiya da addu’o’i da goyon bayan da sarakunan gargajiya da malaman addini ke ci gaba da yi wa ƙasar nan.
Ya kuma yi kira da a ƙara himma wajen yin addu’o’i da neman shiriyar Allah domin shawo kan ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta da kuma bunƙasa cigaban ta.
Ziyarar ta kuma sake jaddada muhimmancin ci gaba da kyautata hulɗa tsakanin Gwamnatin Tarayya da hukumomin sarautun gargajiya wajen ƙarfafa haɗin kan ƙasa, zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ishaq Samaila na Ofishin Yaɗa Labarai na Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Siyasa da Sauran Al’amura ne ya sanya wa sanarwar hannu.







