Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, ya yi martani kan cire sunan sa daga jerin sunayen ‘yan takarar da aka amince da su domin shiga zaɓen gwamnan Jihar Gombe na shekarar 2027.
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kan ta ta Ƙasa (INEC) ce ta fitar da jerin sunayen a yau Asabar.
Wata sanarwar manema labarai da aka wallafa a shafukan sada zumunta na Pantami, wadda Farfesa Suleiman Mohammed Gombe ya sanya wa hannu, ta ce: “An jawo hankalin mu kan rashin sanya sunan ɗan takarar mu, Farfesa Isa Ali Ibrahim (Pantami), CON, PhD, FCIIS, FBCS, FNCS, wanda ya lashe sabon zaɓen fitar da gwani da aka gudanar a ranar 29 ga Satumba, 2026, bisa umurnin Babbar Kotun Tarayya, a cikin jerin sunayen da INEC ta fitar.
“Mun fahimci damuwar da wannan lamari ya haifar a tsakanin ɗimbin magoya bayan mu na jam’iyyar PDP da Kungiyar Pantamiyya a faɗin Jihar Gombe da ma wajen ta.
“Muna son tabbatar wa da dukkan magoya bayan mu da su kwantar da hankalin su, su tsaya tsayin daka, tare da ci gaba da kasancewa masu fata. Wannan ƙalubale ne na ɗan lokaci, kuma wani abu ne da kan faru a cikin tsarin zaɓe, ba wai hukunci na ƙarshe ba, in sha Allah.
“Muna sane da wasu mutane da ke aiki a bayan fage domin kawo cikas ga samun shugabanci nagari a Jihar Gombe. Sai dai ƙungiyoyin mu na shari’a da hulɗa da hukumomi sun riga sun fara tattaunawa da hukumomin da abin ya shafa na jam’iyya da kuma INEC, domin tabbatar da bin ƙa’idoji yadda ya kamata da kuma gyara matsalar cikin wa’adin da doka ta tanada.
“Da ikon Allah, za a warware wannan matsala.
“Muna kira ga magoya bayan mu da su ci gaba da ƙoƙarin wayar da kan jama’a da tattara goyon baya, tare da mayar da hankali kan aƙidar mu ta bai wa bil’adama hidima.
“Jam’iyyar PDP da Ƙungiyar Pantamiyya suna nan da ƙarfi, cikin haɗin kai, kuma a shirye suke wajen ceto da ’yantar da al’ummar mu. Babu wata tangarɗa da za ta karkatar da mu daga tafarkin mu, in sha Allah.
“Allah Ya albarkaci Jihar Gombe, kuma Allah Ya albarkaci Tarayyar Jamhuriyar Nijeriya.”







