Gwamnatin Tarayya za ta fara ɗaukar ma’aikatan Hukumar Tsaron Daji – Ribadu
.
.
Mai ba wa Shugaban Ƙasa shawara kan Tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya ce Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da tsarin ɗaukar ma’aikata ƙarƙashin shirin Masu Tsaron Daji (Forest Guards) a matsayin wani ɓangare na yaƙi da matsalolin tsaro a ƙarƙashin shirin Renewed Hope Agenda na Shugaba Bola Tinubu.
Ribadu ya bayyana haka ne a Abuja a ranar Laraba yayin ƙaddamar da sababbin motocin aiki 46 da aka raba wa sassan tsaro daban-daban a faɗin ƙasar nan.
Ya ce ƙasar tsarin zai bai wa kowace jiha damar ɗaukar ma’aikata tsakanin 2,000 zuwa 5,000 gwargwadon ƙarfin su.
Ya ce shirin zai taimaka wajen kare al’ummomi, dazuzzuka da albarkatun ƙasa.
Ribadu ya ƙara da cewa akwai sauye-sauye masu ma’ana da ake samu kullum a fannin tsaro, waɗanda ko da ba su fito fili ba, ana ganin tasirin su a rayuwar al’umma.






