A farkon makon nan dai rahotanni daga Hukumar Yaƙi da Cin-hanci da Zamba (EFCC) sun tabbatar da tsare wasu manyan jami’an Hukumar Alhazai ta Ƙasa, ciki har da Kwamishinan Harkokin Kudaden, Ma’aikata da Tsare-tsare na hukumar ta NAHCON, wato Aliyu Abdulrazak, bisa zargin badaƙala da harƙallar maƙudan kuɗaɗe.
Kafafen yaɗa labarai ciki har da Sahara Reporters sun wallafa cewa an yi tsare har da Daraktan Harkokin Kuɗaɗe, Aminu Y. Muhammed, waɗanda aka ce sun amsa gayyatar da EFCC ta yi masu a ranar Litinin, misalin ƙarfe 11 na rana.
Wannan tangara-gatsar dai ta biyo bayan zarge-zargen almubazzaranci da karkatar da kuɗaɗen gudanar da aikin Hajjin 2025 ne da Gamayyar Ƙungiyar Shugabannin Hukumar Jin Daɗin Alhazai da Hukumomi suka yi ne, waɗanda suka nuna cewa “an samu sakaci a aikin Hajji na 2025, a ƙarƙashin Shugaban NAHCON, Abdullahi Saleh Usman”, wanda aka fi sani da Abdullahi Pakistan.
A wani taro da ƙungiyar ta gamayyar Shugabannin Hukumar Alhazai na Jihohi suka yi da NAHCON a makon jiya a Abuja, sun tayar da tashin-tashina 16, waɗanda bakwai daga cikin su kai-tsaye zargi ne na badaƙala da yi wa kuɗaɗen hukuma ‘yar-burum-burum, waɗanda su ne EFCC ke bincike a yanzu.
An ruwaito cewa cikin binciken da EFCC ke wa Abdulrazak da Muhammed, har ma wani tsohon zargi na karkatar da wasu maƙudan kuɗaɗe, tun a zamanin tsohon shugaban NAHCON, Jalal Arabi.
New Citizen Hausa ta ci karo da rahotannin da suka tabbatar da cewa tun a farkon Agusta sai da EFCC ta titsiye wasu manyan ma’aikatan NAHCON ta yi masu tambayoyin ƙwaƙwaf, dangane salwantar kuɗaɗe.
Waɗanda aka titsiye a farkon watan dai sun haɗa da Mataimakin Daraktan Hada-hadar Kudade, Abdulmalik Diggi, Mashawarci na Musamman ga Shugaban NAHCON, Sirajo Usman Salisu, Mataimakin Darakta na Ofishin Shugaba, Barista Nura Danladi.
Bincike ya nuna cewa EFCC na nan ta na tantance zargin salwantar Naira biliyan 50 a ƙarƙashin jagorancin Abdullahi Pakistan.
Daga cikin zarge-zargen akwai na yin bindiga da Naira biliyan 25 da aka ce an kashe a tantinan kwanan mahajjata na Masha’ir, Naira biliyan 1.6 da kuma wasu Naira biliyan 7.9 na biyan kuɗaɗen gidajen mahajjata a Makkah.
Sannan an kuma zargi Pakistan da yin gaban-gabara wajen rattaba hannun amincewa a cire Naira biliyan 25, domin ɗaukar ɗawainiyar jami’an hukuma, masu ruwa da tsaki, matan su da ‘ya’yan su a lokacin aikin Hajji.
An kuma tabbatar da labarin cewa tun kafin wannan kamu, sai da EFCC ta fara kama su Ahmad Jalal Arabi da Zikirullah Kunle Hassan da kuma tsohon Kwamishinan Harkokin Kuɗaɗe, Nura Yakasai, duk an tsare su, an bayar da belin su.






