GWAMNATIN Tarayya ta ce ta raba kimanin naira biliyan 50 kai-tsaye ga cibiyoyin kiwon lafiya na sha-ka-tafi (PHCs) a faɗin ƙasar nan ta hanyar Asusun Samar da Kiwon Lafiya na (BHCPF).
Ministan Kiwon Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate, ne ya bayyana haka a Abuja a ranar Litinin.
Ya ce hakan ya samar da ci gaba mai ma’ana wajen inganta tsarin kiwon lafiya a matakin ƙasa.
Pate ya kuma ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta kuma saki sama da N20 biliyan don gyara da sabunta cibiyoyin kiwon lafiya 4,362 a jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya (FCT).
Ministan ya ƙara da cewa sama da mutane miliyan 37 ne suka je cibiyoyin kiwon lafiya na sha-ka-tafi a faɗin Nijeriya a watanni huɗu na farkon shekarar 2025, wanda ke nuna cewa sabbin matakan gwamnatin Tinubu na tasiri wajen tsare-tsaren kiwon lafiya da samar da bayanan ƙididdigar waɗanda aka duba.
Haka kuma, ya ce shirin inshorar lafiya na gwamnati ya samu ci gaba sosai inda ake sa ran shigar da mutane fiye da na shekara ta 2024 da suka kai miliyan 2.4 kafin ƙarshen shekara.







