• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Thursday, October 1, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gwamnati ta dakatar da kuɗin harajin kwastam da kashi 4 kan kayan da ake shigo da su daga waje

Wakilin Mu by Wakilin Mu
September 15, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Gwamnati ta dakatar da kuɗin harajin kwastam da kashi 4 kan kayan da ake shigo da su daga waje
Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam Adewale Adeniyi

Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam Adewale Adeniyi

Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta dakatar da aiwatar da kuɗin harajin kashi 4 cikin ɗari na farashin kaya kafin ɗauko su daga ƙasar da aka samo su (Free on Board [FOB]) da Hukumar Kwastam ta sanya a kan kayayyakin da ake shigo da su ƙasar nan.

Ma’aikatar Kuɗi ta ce an ɗauki wannan mataki ne bayan dogon nazari da shawarwari daga masana harkar kasuwanci, masana tattalin arziki da kuma jami’an gwamnati.

A cewar ma’aikatar, an gano cewa harajin na iya jefa ƙasa cikin ƙarin matsaloli na hauhawar farashi, tsadar kayayyaki, da kuma rage gasa a harkokin kasuwanci.

Wata sanarwa da Babban Sakataren Ma’aikatar Kuɗi, R.O. Omachi, ya fitar, ta ce yawancin ’yan kasuwa da masu shigo da kaya sun nuna damuwa kan wannan haraji saboda nauyin da zai ɗora masu.

Sanarwar ta ce dakatarwar za ta bada damar tattaunawa da sake nazari kan tsarin, tare da shirin samar da wata hanya mafi daidaito da za ta taimaka wajen tara kuɗaɗen shiga da kuma tabbatar da ci gaban tattalin arzikin ƙasa.

Ma’aikatar ta kuma umurci hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da bin wannan umarni kai-tsaye.

Previous Post

‎Tinubu ya gama hutu, zai dawo Abuja gobe

Next Post

Wani ya gudu ya bar dala miliyan 7 a banki a Legas

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
Wani ya gudu ya bar dala miliyan 7 a banki a Legas

Wani ya gudu ya bar dala miliyan 7 a banki a Legas

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!