Wani mutum da ba a san ko wanene ba ya gudu ya bar zunzurutun tsabar kuɗi har dalar Amurka miliyan bakwai a wani banki a Legas.
Hakan ta sa Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke hukuncin cewa a mallaka wa Gwamnatin Tarayya kuɗin, waɗanda sun kai kimanin naira biliyan 10.8.
Su dai waɗannan kuɗi, an ɓoye su ne a sirrance a wata taskar adana kuɗi ta reshen bankin da ke lamba 114 Titin Adeola Odeku, Victoria Island, Legas.
Mai Shari’a Emeka Nwite ya yanke hukunci a jiya Litinin, bisa ƙarar da Hukumar Yaƙi da Almundahanar Kuɗi (EFCC) ta shigar tun da fari, cewa a miƙa kuɗin ga gwamnati tunda ba a san mai su ba.
Tun a ranar 27 ga Agusta ne EFCC ta samu hukuncin wucin-gadi na kotu cewa a karɓe kuɗin a mallaka su ga gwamnati.
Babban lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo (SAN), ya shaida wa kotun cewa EFCC ta bi umurnin kotun na wallafa yekuwa a babbar jarida a ranar 1 ga Satumba inda ta yi kira ga duk wanda ya san yana da ta-cewa a kan wannan kuɗi da ya bayyana kan sa.
Ya ce: “Amma tun daga ranar da aka wallafa sanarwar babu wani mutum ko kamfani da ya zo ya ce kuɗin sa ne.”
Oyedepo ya roƙi kotun da ta bada umurnin ƙarshe na karɓe kuɗin a ba gwamnati.
Sai dai kuma an samu wani lauya wai shi Darlington Ozurumba wanda ya bayyana a kotun yana faɗin wai yana wakiltar wani da bai bayyana ko wanene ba a kan kes ɗin, amma kuma wai ba ya adawa da buƙatar da EFCC ta kawo kan al’amarin.
Mai Shari’a Nwite ya ce ya dai lura babu wata takarda da aka kawo masa da take adawa da buƙatar EFCC, don haka ya bada umurnin a karɓe kuɗin nan dala miliyan bakwai, sun zama mallakin Gwamnatin Tarayya har abada.
Ita dai EFCC, ta yi cikakken bayani a kotu kan yadda wannan badaƙalar ta fara, ta ce wasu jami’an ta ne aka ƙyanƙyasa wa labarin cewa an ɓoye kuɗin a ɗakin ajiya na bankin, su kuma suka yi wuf suka je suka tarar da kuɗin.
Hukumar ta yaƙi da cin hanci da rashawar ta ce an kai kuɗin a bankin ne ta wata hanya da ta haifar da zargi a tsakanin ranakun 25 da 26 ga Maris, 2025, kuma ba a rubuta sunan kowa da sunan nasa ba ne.
Maimakon haka, masu binciken sun gano cewa an jingine tsabar kuɗin a cikin taskar ajiya ta bankin.
A takardar bayani da ta kai kotun, EFCC ta ce ta tattauna da jami’in kula da tsabar kuɗi na bankin, Mista Agba Emmanuel Fortune, wanda ya faɗa masu cewa wai wasu mutane biyu, Suleiman Sani (wanda daga baya aka tabbatar da cewa sunan sa Fagge Sani Sanusi ta hanyar katin sa na ɗan ƙasa, wato ‘national ID card’) da Idris Ahmed Olatunji su ne da kan su suka kawo kuɗin har dalar Amurka miliyan bakwai a zuwa biyu ko zuwa uku, suka ba shi ya aje masu.
Ƙarin bincike ya nuna cewa wata mai suna Ifeoma Delphine Nwogbo, wadda ita ce Jami’ar Yaɗa Labarai ta bankin, tana da masaniya game da kuɗin, inda ta ce wai kuɗin wata matar ne wadda manajar daraktar wani kamfani ce.
To amma da aka tuntuɓi matar da take manajar darakta, sai ta ƙaryata labarin cewa wai ita ce ta kawo kuɗin wuri na gugar wuri har dala miliyan bakwai a bankin. Ta ce ita dai ta san ta ranci dala miliyan bakwai daga bankin domin wata hidima, kuma ba ta biya su ba tukuna.
EFCC ta ce ta ga laifin bankin da har bai kawo rahoton da ake kira “Suspicious Transaction Report (STR)” ba wanda ake rubutawa idan an ga shigar kuɗin da ake zargin yanayin su a banki, ana miƙa rahoton ne ga Cibiyar Bayanan Sirri Game Da Kuɗi ta Nijeriya, wato “Nigerian Financial Intelligence Unit (NFIU)” duk da yake akwai ayar tambaya game da wannan kuɗi.
Hukumar ta ce ta gamsu matuƙa cewa wannan kuɗi na wata harƙalla ne da aka yi wadda ta karya doka, domin babu wani bayani da ke nuna cewa an yi wata harkar gaskiya ne da su a wajen waɗanda suka kawo su, ko jami’an bankin, ko kamfanin da aka ambata.
Hakan ce ta sa aka kwashe kuɗin baki ɗaya aka adana su a asusun Gwamnatin Tarayya da ke Babban Bankin Nijeriya (CBN) kafin a gama shari’ar da EFCC ta shigar a kotun.
Yanzu dai kotun ta yi wa tufka hanci, tunda ta yanke hukuncin cewa kuɗi sun zama na gwamnati domin an rasa gane mai su, saboda ya noƙe.
Da ma haka ake yi, wato idan an rasa gane mamallakin wasu kuɗi ko kadara, to sun zama mallakin baitulmali.







