• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gwamnati ta dakatar da ƙudirin ƙarin harajin kashi 15 cikin ɗari kan shigo da fetur da dizal

Wakilin Mu by Wakilin Mu
November 13, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Gwamnati ta dakatar da ƙudirin ƙarin harajin kashi 15 cikin ɗari kan shigo da fetur da dizal
Gidan mai

Gidan mai

Hukumar kula da harkokin man fetur (Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority, NMDPRA) ta bayyana cewa ba za a aiwatar da ƙudirin ƙarin harajin kashi 15 cikin ɗari kan shigo da man fetur (PMS) da dizal ba.

Wannan bayanin yana ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, George Ene-Ita, ya fitar a shafin su na X a yau Alhamis, inda ya ce aiwatar da harajin da aka tsara ba ya cikin tsarin gwamnati a halin yanzu.

Hukumar ta tabbatar da cewa akwai wadataccen isasshen man fetur, dizal da iskar gas (LPG) a ƙasar nan, wanda ake samu daga masana’antun cikin gida da kuma shigo da su daga waje domin biyan buƙatar al’umma, musamman a lokacin buƙata ta musamman.

NMDPRA ta buƙaci ‘yan kasuwa da masu motoci da su guji ɓoye mai, saye da fargaba ko kuma ƙara farashi ba bisa ƙa’ida ba, tana mai cewa za ta ci gaba da sa ido a kasuwa tare da ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da cewa babu tangarɗa wajen rabon man.

“Hukumar na gode wa dukkan masu ruwa da tsaki a sashen man fetur bisa ƙoƙarin su na tabbatar da isar mai ba tare da katsewa ba, kuma muna tabbatar da aniyar mu ta kare tsaron makamashi a ƙasar nan,” inji ta.

Previous Post

CBN da Gwamnatin Tarayya sun ƙaddamar da shirin daƙile tsadar rayuwa da hauhawar farashi

Next Post

Tinubu ya sabunta naɗin Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA na tsawon shekaru 5

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
Tinubu ya sabunta naɗin Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA na tsawon shekaru 5

Tinubu ya sabunta naɗin Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA na tsawon shekaru 5

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!