• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Thursday, October 1, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnan Neja ya yi ƙarin haske kan dokar da ta tilasta wa limamai karɓar lasisin yin huɗuba ko wa’azi

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
September 15, 2025
in Labarai
A A
0
Gwamnan Neja ya yi ƙarin haske kan dokar da ta tilasta wa limamai karɓar lasisin yin huɗuba ko wa’azi
Gwamna Mohammed Umaru Bago

Gwamna Mohammed Umaru Bago

Gwamna Mohammed Umaru Bago na Jihar Neja ya ƙara bayyana dalilan tilasta wa malamai da limamai na Musulunci da Kirista karɓar lasisin tantancewa da amincewar gwamnati kafin su yi wa’azi da huɗubobi a masallatai da coci-coci a faɗin jihar.

Ya ce lallai tilas kafin kowane limami ya hau mumbari ya yi huɗuba a ranar Juma’a, sai ya fara damƙa kwafen huɗubar domin hukuma ta tantance kafin ranar.

Hakan na ƙunshe cikin ƙarin hasken da ya yi a wata tattaunawa da gidan talbijin na TVC ta yi da shi a jiya Lahadi.

Bago ya ce gwamnatin sa ta fito da wannan doka ne domin tabbatar da cewa wa’azoji da huɗubobin malamai ba su zama musabbabin tayar da hargitsi ko ruruta baƙar adawa da gwamnati da sunan wa’azi ba.

Ya ce: “Ban hana kowa yin wa’azi ba. Amma dai duk limamin da zai yi huɗuba a masallacin Juma’a, to ya fara kawo kwafen huɗubar a tantance kafin ranar tukunna. Wannan kuwa shi ne daidai, domin ko a Saudiyya hakan ake yi.

“Bai fa yiwuwa don kawai ka samu damar zama malami ko limami, sai ka fita kana surfa maganganun da ka iya haddasa fitina, ko ka buɗe babin rigima da gwamnati. Kuma wai kai gani kake daidai ne.”

Da aka tambaye shi ko hakan na da nasaba da damuwar da ake yi kan masu yaɗa munana da tsauraran aƙidu a cikin al’umma, sai ya ce, “Ƙwarai kuwa, wannan ne dalilin. Muna so mu riƙa sanin abin da suke wa’azi a kai, mu riƙa sauraron abin da suke faɗa. Kuma muna aiki tare da jami’an tsaro na DSS, ‘yan sanda, NSCDC har ma da sojoji.”

Tuni dai Babban Daraktan Harkokin Addini na Jihar Neja, Umar Farooq, ya bada sanarwa cewa duk wanda ke so ya yi wa’azi a Jihar Neja, sai ya yanki lasisin tantancewa da amincewa tukunna.

Ya ce wa’adin karɓar lasisin zai ƙare nan da watanni biyu, lokacin da dokar za ta fara aiki gadan-gadan.

Tags: Gwamna Mohammed Umaru BagolasisilimamaiNejawa'azi
Previous Post

Gwamnatin Tarayya za ta ciyar da ‘yan makaranta miliyan 50 a 2026 – Adebowale

Next Post

‎Tinubu ya gama hutu, zai dawo Abuja gobe

Related Posts

Nijeriya ta gyara tafiyar ta, yanzu zamanin wadata ya zo – Tinubu
Labarai

Nijeriya ta gyara tafiyar ta, yanzu zamanin wadata ya zo – Tinubu

October 1, 2026
Ranar Zuciya ta Duniya: Idris ya yi kira da a ƙara kaimi wajen yaƙi da cututtukan zuciya
Kiwon Lafiya

Ranar Zuciya ta Duniya: Idris ya yi kira da a ƙara kaimi wajen yaƙi da cututtukan zuciya

September 30, 2026
Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya
Labarai

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya

September 29, 2026
Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Next Post
‎Tinubu ya gama hutu, zai dawo Abuja gobe

‎Tinubu ya gama hutu, zai dawo Abuja gobe

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!