• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Friday, October 2, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnatin Tarayya za ta ciyar da ‘yan makaranta miliyan 50 a 2026 – Adebowale

ALI KANO by ALI KANO
September 14, 2025
in Labarai
A A
0
Gwamnatin Tarayya za ta ciyar da ‘yan makaranta miliyan 50 a 2026 – Adebowale
Dakta Aderemi Adebowale

Dakta Aderemi Adebowale

Gwamnatin Tarayya ta ce tana ƙoƙarin faɗaɗa Shirin Ciyar Da ‘Yan Makaranta Daga Gida na Ƙasa (National Home-Grown School Feeding Programme, NHGSFP) ta yadda za a riƙa ciyar da ɗalibai miliyan 50 a cikin shekara mai zuwa ta 2026.

Babbar Manajar Cibiyar Inganta Rayuwa ta Ƙasa (National Social Investment Programme Agency, NSIPA), Dakta Aderemi Adebowale, ita ce ta bayyana haka a hirar ta da Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN) a Abuja.

Ta ce: “Muna ƙoƙarin haɗawa da yara masu ƙananan shekaru – firamare 1 zuwa 3, firamare 4 zuwa 6 – a shirin ciyar da ‘yan makaranta, da ma yaran da ba su zuwa makaranta, wanda muke yi mataki-mataki don mu haɗa komai.

“Saboda haka, ya zuwa shekara ta 2026, muna hangen za mu riƙa ciyar da kusan ‘yan makaranta miliyan hamsin a makarantun firamare a Nijeriya.

“In da so samu ne, kamata ya yi ciyar da ‘yan makaranta ya zama tsakanin N500 zuwa N1,000 kan kowane yaro.

“Ko da a N500 kan kowane yaro ne, ya kamata ka iya ba yaran abinci mai Gina jiki kuma mai daɗi a kowace rana.”

Adebowale ta ƙara da cewa ta samu iyakance farashi ta hanyar yin haɗaka da ƙananan manoma, da masu dubawa, da tsarin kai abincin, da abokan hulɗa masu sa ido.

“Da wannan haɗakar, za mu iya iyakance farashin ya zama mafi ƙanƙanta. Ba za mu riƙa amfani da farashin kasuwa ba.

“Saboda haka, sai mun amince da farashin daga ‘yan kwangila, da masu sayarwa, da manoma har mu cimma farashi mai rahusa na kowane kwanon abinci. Da zarar mun yi hakan, sai mu ɗora da biyan kuɗi da kuma kawo kayan.”

A ranar 27 ga Mayu, 2025 ne dai Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin “Alternate Education and Renewed Hope National Home-Grown School Feeding Project,” wanda manufar sa ita ce a samar da abinci ga yaran da ba su zuwa makaranta da masu samun ƙarancin abinci har miliyan 20 ya zuwa shekara ta 2026.

Ministan Jinƙai da Rage Fatara na lokacin, Farfesa Nentawe Yilwatda, shi ne ya ƙaddamar da shi a Abuja.

A yanzu shi Yilwatda shi ne Shugaban jam’iyyar APC na Ƙasa.

Tags: ciyar da 'yan makarantaDakta Aderemi Adebowaleɗalibai
Previous Post

Gargaɗi: An Hango Bala’in Ambaliyar Ruwan Sama A Jihohi 11 Ran Alhamis

Next Post

Gwamnan Neja ya yi ƙarin haske kan dokar da ta tilasta wa limamai karɓar lasisin yin huɗuba ko wa’azi

Related Posts

Nijeriya ta gyara tafiyar ta, yanzu zamanin wadata ya zo – Tinubu
Labarai

Nijeriya ta gyara tafiyar ta, yanzu zamanin wadata ya zo – Tinubu

October 1, 2026
Ranar Zuciya ta Duniya: Idris ya yi kira da a ƙara kaimi wajen yaƙi da cututtukan zuciya
Kiwon Lafiya

Ranar Zuciya ta Duniya: Idris ya yi kira da a ƙara kaimi wajen yaƙi da cututtukan zuciya

September 30, 2026
Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya
Labarai

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya

September 29, 2026
Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Next Post
Gwamnan Neja ya yi ƙarin haske kan dokar da ta tilasta wa limamai karɓar lasisin yin huɗuba ko wa’azi

Gwamnan Neja ya yi ƙarin haske kan dokar da ta tilasta wa limamai karɓar lasisin yin huɗuba ko wa'azi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!