• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Kada ka damu, za mu sa a sake ka, Gwamnan Abiya ya faɗa wa Nnamdi Kanu 

ALI KANO by ALI KANO
December 1, 2025
in Labarai
A A
0
Kada ka damu, za mu sa a sake ka, Gwamnan Abiya ya faɗa wa Nnamdi Kanu 
Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu

Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu

Gwamnan Jihar Abiya, Mista Alex Otti, ya roƙi shugaban ƙungiyar IPOB da ke kurkuku, Nnamdi Kanu, da ya ci gaba da kasancewa cikin natsuwa da jajircewa yayin da yake ƙara ƙoƙarin tattaunawa domin ganin an sako shi.

Otti ya yi wannan tsokacin ne lokacin da ya ziyarci Kanu a gidan yarin Sakkwato, wata ziyara da aka tabbatar da ita daren Lahadi a wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ferdinand Ekeoma, ya fitar.

Gwamnan ya je gidan gyara halin ne tare da Babban Lauyan Jihar Abiya kuma Kwamishinan Shari’a, Ikechukwu Uwanna (SAN); da ƙanin Kanu, wato Emmanuel Kanu; da manyan jami’an gwamnatin Jihar Sakkwato.

A lokacin ziyarar, Otti ya shaida wa shugaban na IPOB cewa matakan da ya ɗauka sama da shekaru biyu da suka gabata domin warware matsalar sun “ƙaru duk da abubuwan da suka faru kwanan nan.”

A cewar sanarwar gwamnatin, Otti ya ƙarfafa wa Kanu gwiwa, ya ce masa ya “ci gaba da zama cikin natsuwa amma da ƙarfin zuciya,” yana tabbatar masa da cewa wannan lamarin “za a warware shi ta hanyoyin gudanarwa,” kuma a ƙarshe zai sake samun ‘yancin sa.

Gwamnan ya bayyana jin daɗin sa cewa Sarkin Musulmi ya goyi bayan buƙatar sakin Kanu da kuma rage tashin hankali a yankuna.

Kanu, wanda aka ce ya yi cikin farin ciki yayin ziyarar, ya gode wa Otti bisa wannan mataki.

Ya shaida wa gwamnan cewa babban abin da yake yabawa shi ne nagartaccen mulki da duk wani ƙoƙari da zai inganta rayuwar jama’a da gwamnan yake yi a jihar sa.

Haka kuma ya yi addu’ar Allah ya jagoranci Otti da tawagar sa yayin da suke ci gaba da yi wa jihar hidima.

Gwamnatin Abiya ta bayyana cewa Kanu “cikin murmushi yake” a yayin ganawar, tare da nuna godiya ga sabon ƙoƙarin da ake yi domin warware matsalar sa.

An dai tsaurara matakan tsaro a kewayen harabar gidan yarin a lokacin ziyarar.

Idan kun tuna, a ranar 21 ga Nuwamba, 2025, ne Kotun Tarayya a Abuja ta samu Kanu da laifukan da suka shafi ta’addanci, ta kuma yanke masa hukuncin ɗaurin rai-da-rai a gidan yarin.

A cikin ‘yan sa’o’i kaɗan bayan haka, aka mayar da shi daga hannun hukumar DSS a Abuja zuwa Gidan Gyaran Hali na Sakkwato, wani mataki da ya janyo ce-ce-ku-ce.

Mai Shari’a James Omotosho na Kotun Tarayya, Abuja, ne ya yanke hukunci a doguwar shari’ar da aka yi wa Kanu, inda kotun ta same shi da laifi kan tuhume-tuhume bakwai da suka shafi ta’addanci da Gwamnatin Tarayya ta gabatar.

Can a baya a watan Oktoba 2023 wata Kotun Jihar Inugu ta soke da kuma rusa ayyana IPOB a matsayin ƙungiyar ta’addanci, ta kuma yanke hukuncin biyan diyyar naira biliyan 8 a kan waɗanda ake ƙara – wato Ƙungiyar Gwamnonin Kudu-maso-gabas da Gwamnatin Tarayya, waɗanda su ne na farko da na biyu a ƙarar.

Tags: AbiyaAlexOttigidanYarikurkukuNnamdiKanuSakkwatoSokoto
Previous Post

Sojojin Birged ta 3 sun ceto mutum 7 da aka yi garkuwa da su a Jihar Kano

Next Post

Cikar Jerry Gana shekara 80: Sadaukarwar sa ga gina ƙasa da ƙarfafa dimokiraɗiyya abin koyi ne — Ministan Yaɗa Labarai

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura
Labarai

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

November 25, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa
Labarai

Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa

November 24, 2026
Next Post
Cikar Jerry Gana shekara 80: Sadaukarwar sa ga gina ƙasa da ƙarfafa dimokiraɗiyya abin koyi ne — Ministan Yaɗa Labarai

Cikar Jerry Gana shekara 80: Sadaukarwar sa ga gina ƙasa da ƙarfafa dimokiraɗiyya abin koyi ne — Ministan Yaɗa Labarai

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!