• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya bar adadin kashi 27% matsayin kuɗin ruwa ga masu ka karɓar rance a bankuna

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
November 26, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Gwamnan CBN ya gargaɗi masu wulaƙanta takardar Naira
Mista Olayemi Cardoso, Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN)

Mista Olayemi Cardoso, Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN)

A matsayin sa na babban jigon kula da dukkan bankuna a Nijeriya, kuma jagoran bunƙasa tattalin arzikin ƙasa, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bar adadin kashi 27% a matsayin kuɗin ruwa, daga kuɗaɗen da masu karɓar rance za su amsa daga bankuna.

Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, shi ne ya bayyana haka, bayan tashi daga Taron Kwamitin Tsare-tsaren Kuɗi (MPC) na Babban Bankin Najeriya (CBN), a ranar Talata, a hedikwatar bankin da ke Abuja.

Da yake ganawa da manema labarai, Cardoso ya ce CBN yana ci gaba da dakatar da ƙarin tsauraran matakai, domin bai wa manufofin baya damar fara aiki yadda ya kamata.

Cardoso ya bayyana haka a Abuja bayan kammala taron MPC na 303, inda ya ce yawancin membobin kwamiti sun jefa ƙuri’a don ci gaba da tsare-tsaren manufofin kuɗi na yanzu, duk da kiraye-kirayen da masana’antu da ‘yan kasuwa suka riƙa yi kan a sassauta kuɗin ruwan, domin rage tsadar karɓar ramce a bankuna.

Wannan dai shi ne karo na huɗu a 2025 da aka bar adadin kuɗin ruwa a matakin da yake, bayan saukar ɗigo 50 kacal a watan Satumba, wanda shi ne sauƙin da aka yi bayan tsauraran matakai a 2024.

Wannan taro wanda shi ne na 303 a tarihin kafa CBN, kuma na ƙarshe a shekarar 2025.

Taron ya gindaya wa bankuna cewa tilas kowane banki ya riƙa ajiye kashi 45% na kuɗin sa a CBN, wato ‘Cash Reserve Ratio’ (CCR). Shi wannan adadin kuɗi ne da bankuna ke ajiyewa a CBN, ba tare da suna ɗiba daga ciki suna bayarwa rance ko sayen hannayen jari da su ba.

Sai kuma geji da ƙarfin biyan basussuka a cikin gajeren lokaci, wato
‘Liquidity Ratio’, wanda ya tsaya a kashi 30% ɗin sa.

Cardoso ya ce wannan mataki na nufin “ƙarfafa nasarar da aka samu wajen rage hauhawar farashi.”

CBN ya bayyana cewa hauhawar farashi ya ragu a watanni bakwai a jere, ya sauka zuwa 16.05% a Oktoba daga 34% a bara.

Hauhawar farashin abinci ya koma 13.12%, yayin da na cikin gida ya ragu zuwa 18.69%.

An danganta wannan raguwar da tsauraran matakan kuɗi sakamakon daidaiton kasuwar canjin kuɗi, ƙaruwar masu zuba jari daga waje, da daidaiton farashin main fetur.

Ya sanar da cewa Asusun Ajiyar Kuɗaɗen Waje ya ƙaru zuwa $46.7bn, daga $42.77bn a Satumba.

Cardoso ya danganta hakan da ƙaruwa a fitar da kayayyakin da ba na mai ba, ƙaruwar samar da yawan mai, ƙaruwa a kuɗaɗen shiga a Najeriya, sai kuma dawowar masu saka jari daga waje.

Ya kuma ce yanzu matafiya na iya yin amfani da katin naira a ƙasashen waje ba tare da takurawar da aka sani da ta gabata ba.

Alamomin ci gaban tattalin arziki a cikin ƙasa:

Kwamitin MPC ya lura cewa Najeriya ta samu ci gaban tattalin arziki daga kayayyakin da sarrafawa a cikin gida, wato GDP na kashi 4.23% a watannin Afrilu, Mayu da Yuni, daga kashi 3.13% a farkon shekara.
Haka nan PMI ya tashi zuwa 56.4 a Nuwamba, mafi girma cikin shekaru biya, wanda haka yana nuna ƙarfafa harkokin kasuwanci musamman a ɓangaren da ba na mai ba.

Ya ce zuwa yanzu bankuna na ci gaba ƙoƙarin ƙarfafa jarin su. Har ya ce a yanzu haka bankuna 16 sun kammala, yayin da 27 ke cikin matakin ɗaga jari.

Maƙalewar Kuɗaɗen Tallafin Lamuni:

Cardoso ya bayyana cewa binciken cikin gida ya nuna an kashe Naira tiriliyan10.93 a tallafin da aka bayar a baya, inda har yanzu ba a kai ga ƙarni Naira tiriliyan 4.69 ba tukuna, waɗanda ba a biya ba.

Ya ce an amso yanzu ta dawo da Naira tiriliyan 2, amma ragowar ya na takure bankin wajen ɗaukar sabbin tsare-tsare.

Ya ce tsarin tallafin baya ya kawo tangarɗa da cikas a kasuwa, yana jaddada cewa yanzu CBN zai tallafa wa ci gaban tattalin arziki ta hanyoyi marasa samar da cikas a kasuwa.

Ya ƙara da cewa haɗin kai tsakanin hukumomin kuɗi da na gwamnati ya ƙara ƙarfi, wanda ya ce shi ne ginshiƙin da ya haifar da daidaito da ɗorewar tattalin arziki kan miƙaƙƙar turba.

Tags: Babban Bankin NijeriyabankunaCBNOlayemi Cardosorance
Previous Post

’Yan Matan Makarantar Kebbi Da Aka Sace Sun Sami ’Yanci Ta Hanyar Tattaunawa Da Ɓarayin Daji

Next Post

CBN zai haramta wa ‘yan gidoga masu rubuta cek na bogi yin hulɗa da banki tsawon shekara biyar

Related Posts

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

November 25, 2026
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

November 17, 2026
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

November 16, 2026
Next Post
CBN zai haramta wa ‘yan gidoga masu rubuta cek na bogi yin hulɗa da banki tsawon shekara biyar

CBN zai haramta wa 'yan gidoga masu rubuta cek na bogi yin hulɗa da banki tsawon shekara biyar

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!