Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin tsohon Babban Hafsan Hafsoshi, Janar Christopher Musa (mai ritaya), a matsayin sabon Ministan Tsaro.
An tabbatar da naɗin da Shugaban Ƙasa ya yi ne a yau Laraba ta hanyar ƙuri’ar murya, bayan zaman tantancewa da ’yan majalisar suka gudanar a zauren su na babban kwamitin da ya haɗa kowa da kowa, inda suka tambaye shi jerin tambayoyi masu yawa kan aikin tsaro da makomar rundunonin soji.
Janar Musa, wanda ya yi murabus daga aikin soja kusan kwanaki 40 da suka gabata, shi ne Shugaba Bola Tinubu ya sake gabatar wa majalisar a matsayin zaɓin sa na Ministan Tsaro a ranar Talata, tare da neman gaggawar tabbatar da shi.
A yayin zaman tantancewar, ’yan majalisar sun tattauna da shi kan batutuwan da suka shafi tsaro, matsalolin hare-hare da suke fuskantar ƙasar nan da sababbin dabarun da ake sa ran zai kawo domin ƙarfafa tsaron ƙasa.
Majalisar ta amince da naɗin nasa bayan ba a samu wata adawa kai-tsaye ba a zauren majalisar.






