• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Batutuwa 25 dangane da attajirai 3,028 na duniya: Tasirin Ɗangote da Abdulsamad Rabi’u A Duniya

Ashafa Murnai Barkiya by Ashafa Murnai Barkiya
May 27, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
  • Me Ya Sa Babu Ɗan Ƙabilar Igbo A Jerin Attajiran Afrika Da Duniya Baki Ɗaya?
  • Ɗangote: Bahaushen Da Mutum 82 Kaɗai Suka Fi Shi Ƙarfin Arziki A Duniya
  • Abdulsamad Rabi’u: Bahaushen Da Bayarabe Ɗaya Ne Ya Fi Shi Ƙarfin Arziki

Mujallar Forbes ta watan Afrilu, 2025 ta fito da sabon jadawalin attajiran duniya, su 3,028. A cikin bayanin da mujallar ta yi, ta bayyana cewa ta yi amfani da ma’aunin darajar Dalar Amurka a kasuwar hada-hadar canji ta ranar 7 ga Maris, 2025, inda ta auna ƙarfin arzikin kowanen su a Mizanin Hada-hadar Hannayen Jari a duniya.

New Citizen Hausa ta bi diddigin jadawalin waɗannan manyan attajirai su 3,025, inda ta zaƙulo waɗansu muhimman bayanai kamar haka:

1. Aliko Ɗangote shi ne mutum na 83 a jerin manyan attajirai na duniya, daga cikin mutum sama da biliyan 8 da miliyan 221 da ke raye a duniya, a ƙididdigar ranar 13 ga Maris, 2025.

2. Ɗangote shi ne baƙar fatan da ya fi kowane baƙar fata ƙarfin arziki a duniya.

3. Ƙarfin arzikin Ɗangote ya kai Dala biliyan 23.9, ko a ce Dala biliyan 24 a ƙiyasance.

4. Ɗangote shi ne mafi ƙarfin arziki a Afrika da Afrika ta Yamma.

5. Shekara 14 kenan a jere Ɗangote na riƙe da kambun mafi ƙarfin arziki a Afrika da cikin baƙaƙe na duniya baki ɗaya.

6. Ƙarfin arzikin Ɗangote ya ninka arzikin Yarabawa biyu masu ƙarfi a Afrika har sau uku da ɗoriya.

7. Abdulsamad Rabi’u (BUA), shi ne na 3 a ƙarfin arziki a Najeriya, na 7 a jerin baƙaƙe na duniya, kuma na 6 na Afrika.

8. Ƙarfin arzikin Abdulsamad BUA ya kai Dala biliyan 5.1 a ƙididdigar Forbes ta 2025.

9. Ɗangote ya ninka Abdulsamad ƙarfin arziki har nunki huɗu.

10. Ƙididdigar Forbes dai na nufin babu wani ɗan ƙabilar Igbo ƙasaitaccen attajirin da ƙarfin arzikin sa ya kai ko ya haura darajar Dala biliyan ɗaya.

11. Ƙididdigar ta nuna babu ɗan ƙabilar Igbo ko ɗaya a jerin manyan attajiran Afrika 20.

12. Wannan ƙididdiga ta nuna babu ɗan ƙabilar Igbo a jerin attajirai baƙar fata su 23 na duniya.

13. Attajirai huɗu ne kacal daga Najeriya waɗanda ke cikin jerin attajirai na duniya. Su ne Aliko Ɗangote, Mike Adenuga, Abdulsamad Rabi’u da Femi Otedola. Wato Bahaushe biyu, Bayarabe biyu.

14. Ƙididdigar Forbes dai na nufin a ƙabilar Igbo babu mai ƙarfin arzikin mawaƙiyar nan ‘yar rawar kwambilo, wato Rihanna, wadda ke da Dala biliyan 1 da miliyan 400.

15. Daga cikin waɗannan attajirai 3,028 na duniya, 902 a Amurka suke. Sai Chana da Hong Kong 512. Indiya kuma 205.

16. A 1987, shekarar da Forbes ta fara wannan ƙididdigar, biloniyoyi 140 kaɗai aka samu a duniya. Bayan shekaru 20 kuma an samu biloniyoyi 1,000 a 2007.

17. Tsakanin 2007 zuwa 2017 adadin attajiran sun ƙaru zuwa mutum 2000.

18. Daga 2017 kuma zuwa 2025, adadin ya kai 3,028.

19. Cikin 2025 an samu ƙarin attajirai masu sama da Dala biliyan 1 har mutum 285 a duniya.

20. Ƙarfin arzikin Ɗangote ya kusa ninkawa ne a cikin 2025, albarkacin Matatar Ɗangote da ya gina a Legas.

21. A ƙididdigar 2024 ƙarfin arzikin Ɗangote ya na Dala biliyan 13.4 ne. An haɗa da matatar sa ce ya koma Dala biliyan 23.9 a 2025.

22. Elon Musk shi ne mafi ƙasaitar arziki a duniya, mai ƙarfin Dala biliyan 342.

23. Forbes ta jinjina wa Ɗangote wajen juriyar da ya nuna har ya gina katafariyar matatar man fetur, wadda ita ce ta bakwai a girma a duniya.

24. “Inda Ɗangote ya fi ba da mamaki shi ne yadda ya kwashi tulin yashi daga cikin teku mai yawan cubic miliyan 365, ya gina tashar jiragen ruwa tasa ta kan sa, don amfanin matatar sa,” cewar Forbes.

25. Ƙididdigar Forbes ta nuna ba a samun ƙasaitaccen attajiri a cikin manyan masu riƙe da muƙaman gwamnati, sai dai a samu ƙasurgumin ɓarawo.

Abin Lura: Duk Dala biliyan 1 ta haura Naira tiriliyan 1 da rabi.

Previous Post

Batutuwa 25 Dangane Da Manyan Attajirai 3,028 Na Duniya 

Next Post

Sauye-sauyen da na kawo sun fara haifar da ɗa mai ido – Tinubu a jawabin cika shekaru biyu

Related Posts

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

November 25, 2026
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

November 17, 2026
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

November 16, 2026
Next Post

Sauye-sauyen da na kawo sun fara haifar da ɗa mai ido - Tinubu a jawabin cika shekaru biyu

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!