Shugaba Bola Tinubu ya kammala hutun sa kafin ranar da aka tsara zai gama, kuma zai dawo Abuja gobe Talata don ci gaba da aikin sa.
Kakakin shugaban ƙasa, Mista Bayo Onanuga, shi ne ya bayyana haka ciki n wata takarda a yau a Abuja.
Tinubu dai ya tafi Faransa ne a ranar 4 ga Satumba don yin wani ɓangare na hutun sa na shekara, wanda da farko zai raba lokacin hutun tsakanin Faransa da Birtaniya.
Onanuga ya ce hutun kwana 10 shugaban ya karɓa.
A zaman sa a Paris, Shugaba Tinubu ya yi zaman cin abinci tare da Shugaban Faransa, Emmanuel Macron a Fadar Élysée.
Shugabannin biyu sun tattauna muhimman al’amurra da dama da suka shafi batun haɗin kai kuma suka amince da buƙatar ƙarfafa dangantakar da ke tsakanin Nijeriya da Faransa ta fuskar albarkar juna da zaman lumana a faɗin duniya.







