Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga ƙasashen Afirka da su ƙarfafa haɗin kai wajen yaƙi da yaɗuwar labaran ƙarya, dawo da amincewar jama’a da kuma tabbatar da murya guda ta Afirka kan batutuwan da suka shafi nahiyar.
Idris ya yi kiran ne ranar Talata a yayin ganawa da takwarorin sa na Kenya, William Kabogo Gitau, da Sudan, Khalid Ali Al-Aiser, a gefen Taron Hulɗar Jama’a na Duniya na shekarar 2026 (World Public Relations Forum, WPRF) da ke gudana a Abuja.
Ministan ya ce dole ne ƙasashen Afirka su ƙara haɗin kai wajen tunkarar ƙalubalen sadarwar da suke fuskanta, musamman yaɗuwar labaran ƙarya.
Ya ce: “Dole ne mu nemo hanyoyin yin aiki tare a matsayin ƙasashen Afirka. Muna da muradu iri ɗaya kuma muna fuskantar ƙalubale iri ɗaya, don haka ya kamata matakan da za mu ɗauka su kasance bisa manufa guda. Muna buƙatar ƙarfafa haɗin kai domin tabbatar da cewa sahihan bayanai sun isa ga al’ummar mu, kuma ana wakiltar murya da ra’ayin Afirka yadda ya kamata.”
Dangane da alaƙar Nijeriya da Kenya, Idris ya bayyana shirye-shiryen Nijeriya na ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu. Ya ce zai tattauna da hukumomin da abin ya shafa kan batutuwan da wakilin Kenya ya gabatar, ciki har da batun biza da sauran al’amuran da suka shafi ƙasashen biyu.
Ya kuma bayyana goyon bayan Nijeriya ga ƙarin tattaunawar diflomasiyya, ciki har da shirin ziyarar aiki ta shugaban ƙasa.
A nasa jawabin, Ministan Yaɗa Labarai, Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital na ƙasar Kenya, William Kabogo Gitau, ya nuna damuwa kan wahalhalun da ’yan Nijeriya suke fuskanta wajen samun biza da tafiya Kenya. Ya ce ’yan Kenya na iya shiga Nijeriya ba tare da biza ba na tsawon kwanaki 60, don haka ya buƙaci a samar da daidaito da sauƙaƙa zirga-zirga tsakanin ƙasashen biyu.
“Muna da buƙata dangane da samun biza da kuma matakan da ’yan Nijeriya ke bi yayin tafiya Kenya. Muna fatan za a magance wannan domin sauƙaƙa zirga-zirga tsakanin ƙasashen mu biyu,” inji Mista Kabogo.
Dangane da Sudan kuwa, Idris ya sake jaddada goyon bayan Nijeriya ga ƙasar tare da bayyana fatan samun zaman lafiya da kawo ƙarshen rikicin da ake fama da shi. Ya ce ƙasashen biyu suna da daɗaɗɗiyar alaƙa ta tarihi, al’adu da dangantakar iyali, musamman tsakanin al’ummomin arewacin Nijeriya da Sudan.
Ya ƙara da cewa Nijeriya tana da muradin ganin Sudan ta samu zaman lafiya da farfaɗowa daga rikicin.
A nasa ɓangaren, Ministan Al’adu, Yaɗa Labarai, Kayayyakin Tarihi da Yawon Buɗe Ido na Sudan, Malam Khalid Ali Al-Aiser, ya gode wa gwamnatin Nijeriya bisa goyon bayan siyasa da take bai wa ƙasar sa, inda ya bayyana Nijeriya a matsayin muhimmiyar abokiyar hulɗa.
Ya yi kira da a farfaɗo da haɗin gwiwar ƙasashen biyu, tare da roƙon Nijeriya ta yi amfani da tasirin kafafen yaɗa labaran ta da alaƙar diflomasiyyar ta wajen taimakawa wajen bayyana halin da ake ciki a Sudan yadda ya kamata.

Ya nuna sha’awar ƙarfafa alaƙar kafafen yaɗa labarai na ƙasashen biyu da kuma cimma yarjejeniyar fahimtar juna (MoU).
“Muna godiya da goyon bayan siyasar da Nijeriya ta ba mu a wannan lokaci mai wuya. Muna kallon Nijeriya a matsayin babbar abokiyar hulɗa, kuma a shirye muke mu yi aiki tare domin farfaɗo da kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin ƙasashen mu,” inji Al-Aiser.
Ganawar ta gudana ne gabanin taron teburin ministocin yaɗa labarai na Afirka da aka tsara gudanarwa ranar Laraba, 18 ga Nuwamba, a matsayin wani ɓangare na shirin WPRF.
Ana sa ran taron zai ba ministocin damar tattauna muhimman batutuwan sadarwa da suka shafi nahiyar tare da duba hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwa.







