• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

FATI ABDUL by FATI ABDUL
November 16, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kayan abinci na sayarwa a kasuwa

Kayan abinci na sayarwa a kasuwa

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta ce hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba, daga kashi 14.63 cikin 100 da aka samu a watan Satumba.

NBS ta bayyana hakan ne a cikin rahoton ta na Fihirisar Farashin Kayayyaki (CPI) da Hauhawar Farashi na watan Oktoba, wanda ta fitar a Abuja ranar Litinin.

Rahoton ya ce hauhawar farashin kayayyaki a Oktoba ya ragu da maki 4.9 idan aka kwatanta da kashi 18.97 da aka samu a Oktoban 2025.

Haka kuma rahoton ya bayyana cewa idan aka kwatanta da watan da ya gabata, hauhawar farashin kayayyaki a Oktoba 2026 ya kai kashi 0.43 cikin 100, wanda ya ƙaru da maki 0.38 idan aka kwatanta shi da kashi 0.06 da aka samu a Satumba na 2026.

Rahoton ya ce: “Wannan na nufin cewa a watan Oktoba, saurin ƙaruwar matsakaicin farashin kayayyaki ya fi wanda aka samu a watan Satumba na 2026.”

Ya bayyana cewa manyan ɓangarori uku da suka fi taimakawa wajen hauhawar farashin kayayyaki a tsakanin Oktoba 2025 da Oktoba 2026 su ne abinci da abubuwan sha marasa maye, da suka bayar da gudunmawar kashi 5.63; ayyukan gidajen cin abinci da masauki, kashi 1.83; da sufuri, kashi 1.50.

A ɓangaren da ya fi bayar da ƙaramar gudunmawa kuwa, akwai nishaɗi, wasanni da al’adu da kashi 0.04; abubuwan sha masu maye, taba da ƙwayoyi masu sa maye da kashi 0.05; da inshora da ayyukan hadahadar kuɗi da kashi 0.07.

Rahoton ya ce Fihirisar Farashin Kayayyaki (CPI) ta ƙaru zuwa 147.0 a Oktoba, wanda ke nuna ƙarin maki 0.06 daga 146.4 da aka samu a Satumba.

Ya kuma bayyana cewa hauhawar farashin abinci a watan Oktoba ya kai kashi 19.13 cikin 100 idan aka kwatanta da makamancin watan a shekarar da ta gabata, inda aka samu kashi 16.30.

Sai dai idan aka kwatanta da watan da ya gabata, hauhawar farashin abinci ya kasance a kashi -0.75, wanda ke nuna ƙaruwar maki 0.80 idan aka kwatanta da kashi -1.55 da aka samu a Satumba.

NBS ta danganta wannan sauyi da matsakaicin farashin wasu kayan abinci, ciki har da man girki na kwalba mai girman santilita 75, kifin gwangwani sadin na Titus mai nauyin giram 125, koren wake na gwangwani, daskararren kifin makerel da kuroka (Apo).

Sauran sun haɗa da shinkafar gida, sabon kifi tarwaɗa (catfish), naman sa, man ja na kwalba mai girman santilita 75 da garin gero da ake sayarwa a awo, da sauran su.

Rahoton ya ce hauhawar farashin kayayyaki idan aka cire amfanin gona da makamashi, wato hauhawar farashin asali (Core Inflation), ta kai kashi 10.78 cikin 100 a Oktoba idan aka kwatanta da makamancin lokacin a shekarar da ta gabata.

Ya ce: “Wannan na nuna raguwar maki 10.47 idan aka kwatanta da kashi 21.25 da aka samu a Oktoba na 2025.

“Idan aka kwatanta da watan da ya gabata, hauhawar farashin asali ta kasance a kashi -0.53 a Oktoba, wanda ke nuna raguwar maki 1.64 idan aka kwatanta da kashi 1.11 da aka samu a Satumba.”

Rahoton ya kuma bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a birane ya kai kashi 14.84 cikin 100 a Oktoba idan aka kwatanta da makamancin lokacin a shekarar da ta gabata.

Sai dai idan aka kwatanta da watan da ya gabata, ya kai kashi 0.43, wanda ke nuna raguwar maki 0.10 idan aka kwatanta da kashi 0.53 da aka samu a Satumba na 2026.

A yankunan karkara kuwa, rahoton ya ce hauhawar farashin kayayyaki ya kai kashi 12.17 cikin 100 a Oktoba idan aka kwatanta da makamancin watan a shekarar da ta gabata.

Idan aka kwatanta da watan da ya gabata, hauhawar farashin a yankunan karkara ya kai kashi 0.18, wanda rahoton ya ce ya nuna ƙaruwar maki 1.07 idan aka kwatanta da kashi 1.79 da aka samu a Satumba.

Dangane da jihohi, rahoton ya nuna cewa Jihar Imo ce ta fi kowace jiha hauhawar farashin kayayyaki a Oktoba idan aka kwatanta da makamancin lokacin a shekarar da ta gabata, da kashi 28.66. Sai Inugu da kashi 22.81, da Kaduna da kashi 21.55.

A ɗaya ɓangaren kuma, Jihar Taraba ce ta fi samun ƙarancin hauhawar farashin kayayyaki da kashi 6.12, sai Sokoto da kashi 6.68, da Ekiti da kashi 7.64.

Sai dai idan aka kwatanta da watan da ya gabata, Jihar Bauchi ce ta fi samun ƙaruwar hauhawar farashin kayayyaki da kashi 11.23, sai Borno da kashi 10.94, da Yobe da kashi 9.93.

Rahoton ya ce jihohin Oyo da kashi -6.71, Osun da kashi -4.78 da Akwa Ibom da kashi -4.41 sun samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki idan aka kwatanta da watan da ya gabata.

Dangane da hauhawar farashin abinci kuwa, Jihar Ondo ce ta fi kowace jiha samun ƙaruwar farashi a tsakanin Oktoba 2025 da Oktoba 2026, da kashi 31.74. Sai Legas da kashi 31.43, da Imo da kashi 29.75.

Rahoton ya ce Nasarawa ce ta fi samun ƙarancin ƙaruwar farashin abinci da kashi 3.70, sai Bayelsa da kashi 7.11, da Kano da kashi 7.13.

Idan aka kwatanta da watan da ya gabata, Jihar Yobe ce ta fi kowace jiha samun ƙaruwar farashin abinci da kashi 18.41, sai Kebbi da kashi 16.45, da Borno da kashi 13.96.

A ɗaya ɓangaren kuma, jihohin Legas da kashi -5.93, Filato da kashi -5.83 da Binuwai da kashi -5.49 sun samu mafi ƙarancin ƙaruwar farashin abinci idan aka kwatanta da watan da ya gabata.

Tags: hauhawar farashiHukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS)tsadar rayuwa
Previous Post

Kamfanin Ɗangote ya ƙaddamar da tirela mai amfani da lantarki ta farko da aka harhaɗa a Nijeriya

Next Post

An kama ‘yan Najeriya takwas a Kanada kan satar motoci na dala miliyan 4.5

Related Posts

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

November 25, 2026
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

November 17, 2026
Kamfanin Ɗangote ya ƙaddamar da tirela mai amfani da lantarki ta farko da aka harhaɗa a Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Kamfanin Ɗangote ya ƙaddamar da tirela mai amfani da lantarki ta farko da aka harhaɗa a Nijeriya

November 16, 2026
Next Post
An kama ‘yan Najeriya takwas a Kanada kan satar motoci na dala miliyan 4.5

An kama 'yan Najeriya takwas a Kanada kan satar motoci na dala miliyan 4.5

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!