• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Kamfanin Ɗangote ya ƙaddamar da tirela mai amfani da lantarki ta farko da aka harhaɗa a Nijeriya

IRO MAMMAN by IRO MAMMAN
November 16, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Kamfanin Ɗangote ya ƙaddamar da tirela mai amfani da lantarki ta farko da aka harhaɗa a Nijeriya
Wasu tireloli na Matatar Mai ta Ɗangote

Wasu tireloli na Matatar Mai ta Ɗangote

Kamfanin Dangote Sinotruk West Africa Limited, wanda haɗin gwiwa ne tsakanin rukunin kamfanonin Dangote na Alhaji Aliko Dangote da kamfanin China National Heavy Duty Truck Group Co., ya ƙaddamar da tirela mai amfani da lantarki ta farko da aka harhaɗa a gida Nijeriya.

An ƙaddamar da motar ne a masana’antar haɗa motoci ta kamfanin da ke Ikeja, a Jihar Legas, yayin wani taro da manyan jami’an kamfanonin biyu da jami’an gwamnatin Jihar Legas suka halarta.

Shugaban rukunin kamfanonin Sinotruk, Liu Wei, ya bayyana motar a matsayin “motar farko mai amfani da sabon makamashi da aka harhaɗa a nahiyar Afirka.”

Sai dai kamfanin bai bayyana farashin motar, ƙarfin batirin ta, tsawon hanyar da za ta iya tafiya da caji guda ko yawan motocin da yake shirin ƙerawa ba.

Mataimakin Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote Industries Ltd., Devakumar Edwin, ya ce shiga harkar ƙera motocin lantarki wani cigaba ne da ya ginu a kan matakin da kamfanin ya ɗauka a baya na sauya amfani da man fetur zuwa iskar gas mai matsewa (CNG).

Ya bayyana cewa motocin kasuwanci masu amfani da lantarki na iya rage kuɗaɗen gudanarwa da kuma hayaƙin da suke fitarwa, yana mai cewa bikin ƙaddamarwar “ya wuce ƙaddamar da sababbin motoci kawai.”

Edwin ya bayyana cewa kamfanin ya riga ya kafa tawagar kula da masu sayen motocin sa bayan saye, sannan yana shirye-shiryen samar da kayayyakin caji, kayayyakin gyara da ƙwararrun ma’aikatan fasaha da masu motocin lantarki a Nijeriya za su buƙata.

Ya ƙara da cewa Sinotruk za ta horas da injiniyoyi da masu fasaha ‘yan Nijeriya, ciki har da shirye-shiryen horaswa ta aikace-aikace ga wasu zaɓaɓɓun ma’aikata a masana’antun ta da ke ƙasar Sin.

Da yake magana a madadin Kwamishinan Sufuri na Jihar Legas, Oluwaseun Osiyemi, Manajan Daraktan Kamfanin Sufurin Motocin Bas na Legas, Olasunkanmi Ojowuro, ya bayyana wannan mataki a matsayin “babban cigaba a tarihin masana’antu na Nijeriya.”

Sarkin gargajiya na Ogba da Shugaban Ƙaramar Hukumar Ikeja su ma sun yi jawabi a wajen taron, inda suka buƙaci ƙara samar da kayayyaki da ayyuka a cikin gida, samar da guraben ayyukan yi da kuma tallafin gwamnati, musamman wajen inganta samar da wutar lantarki da gina wuraren cajin motocin.

Shekaru goma na ƙera manyan motoci

Kamfanonin Dangote Group da Sinotruk sun taɓa ƙulla yarjejeniyar haɗin gwiwa a shekarar 2014, inda tirela ta farko ta fita daga layin haɗa motoci a shekarar 2017, a wata masana’anta da suka gina a Legas kan kuɗi dala miliyan 100.

An tsara masana’antar ne domin haɗa motoci har guda 10,000 a duk shekara. A lokacin, Ɗangote ya bayyana cewa jarin zai samar da guraben ayyukan yi kusan 3,000.

A tsakiyar shekarar 2024, kamfanin haɗin gwiwar ya faɗaɗa ayyukan sa ta hanyar buɗe sabon layin haɗa motocin da ake shigo da sassan su daban-daban daga ƙasashen waje (CKD), musamman na ƙananan da tireloli.

Sabon layin samar da motocin ya ƙunshi aikin waldar sassan ƙarfe, shafa musu fenti ta hanyar amfani da lantarki (electro-coat) da kuma haɗa sassan motar gaba ɗaya. Wannan shi ne aikin farko na cikakken haɗa kabin tireloli irin sa a yankin.

Liu ya bayyana cewa kamfanin ya riga ya haɗa motoci sama da 8,000 a Nijeriya.

Ya ce nau’ikan motocin da kamfanin ke samarwa sun ƙaru daga tireloli zuwa tifofi, ƙananan motoci, motocin fikaf-fikab (pickups) da bas-bas.

Ya ƙara da cewa kamfanonin biyu na shirin fara ƙera tireloli da wasu sassan jikin motoci, tare da inganta layukan samar da motoci da kuma ƙara ƙarfin masana’antar wajen haɗa motoci.

Muhimmancin manyan motoci a harkokin kasuwancin Dangote

Manyan motoci na taka muhimmiyar rawa a harkokin kasuwancin Ɗangote.

Kamfanin Dangote Cement, wanda yana daga cikin manyan rassan kasuwancin hamshaƙin attajirin, yana da ɗaya daga cikin manyan motocin dakon kaya da ake da su a Nijeriya.

Haka kuma, matatar man fetur ta rukunin kamfanonin da ke yankin Lekki ta fara rarraba mai kai-tsaye ga dillalai a shekarar 2025, ta hanyar amfani da tankokin dakon mai masu amfani da iskar gas ta CNG.

Daular kasuwancin Ɗangote

Aliko Ɗangote, mai shekaru 69, shi ne mutum mafi arziki a Afirka, a cewar mujallar Forbes da kamfanin Bloomberg.

Ya fara tara arzikin sa ne ta hanyar kasuwancin kayayyakin masarufi kafin ya faɗaɗa harkokin sa zuwa masana’antun siminti, sukari, gishiri da fulawa, daga bisani kuma ya shiga harkokin samar da takin zamani da tace ɗanyen mai.

Ɗangote ne ke da ikon mallakar kamfanin Dangote Cement Plc, wanda shi ne mafi girman kamfanin samar da siminti a nahiyar Afirka.

Matatar man fetur ɗin sa da ke yankin Lekki Free Trade Zone, mai ƙarfin tace ganga 650,000 na ɗanyen mai a kowace rana, ita ce matatar da ke da mafi girman layin tace mai guda ɗaya a duniya.

A halin yanzu, matatar tana sayar da hannun jari ga jama’a ta hanyar wani gagarumin tayin sayar da hannun jari a karon farko (IPO) a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Nijeriya.

Tags: Aliko ƊangoteChina National Heavy Duty Truck Group CoDangote Refinerytirelawutar lantarki
Previous Post

Babban gangamin APC a Jos yana nuna amincewar Arewa ta Tsakiya ga jagorancin Tinubu, inji Minista

Next Post

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

Related Posts

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

November 25, 2026
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

November 17, 2026
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

November 16, 2026
Next Post
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!