Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa yana nan daram kan tabbatar da daidaiton manufofin kuɗi da tsarin hada-hadar kuɗi, tare da bunƙasa tattalin arzikin da kowa zai amfana da shi da kuma ƙarfafa juriyar tattalin arzikin ƙasar.
Daraktar Sashen Masu Ruwa da Tsaki da kuma Alaƙar Hukumomi, Hajiya Hakama Sidi-Ali, ita ce ta bayyana hakan a Ibadan, wurin shirin sauraren ra’ayoyi, shawarwari da tambayoyin jama’a, mai suna ‘CBN Listens’, mai taken: “Samar da Tsarin Hada-hadar Kuɗi Mai Ƙarfi, Juriya da Bai Wa Kowa Dama Domin Bunƙasar Tattalin Arziki Mai Ɗorewa.”
A wurin taron wanda ya gudana ranar Alhamis a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, Hajiya Hakama ta bayyana cewa samar da manufofi masu inganci da aiwatar da su yadda ya kamata, sun dogara matuƙa kan ci gaba da tattaunawa da jama’a, tare da karɓar shawarwari da ra’ayoyin su.
Ta ce, “Shigar da kowa cikin tsarin hada-hadar kuɗi na daga cikin muhimman ginshiƙan ci gaban ƙasa, domin yana faɗaɗa damar tattalin arziki, rage talauci, tallafa wa harkokin kasuwanci da kuma samar da wadata da al’umma baki ɗaya za ta amfana da ita.”
Hakama ta ƙara da cewa CBN na ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da cibiyoyin hada-hadar kuɗi, kamfanonin fasahar kuɗi (fintech), masu gudanar da harkokin kuɗi ta wayar salula, abokan hulɗa na ci gaba da gwamnatocin jihohi domin faɗaɗa ayyukan kuɗi ga mutanen da ba sa samun irin waɗannan ayyuka ko kuma waɗanda ba su da isasshen damar samun su.
Gyare-gyaren Da CBN Ya Aiwatar
Da take tsokaci kan muhimman gyare-gyaren da CBN ya jagoranta cikin watanni 38 da suka gabata, Hakama ta ce an tsara matakan ne domin dawo da daidaiton tattalin arziki, inganta gaskiya da bayyana gaskiya a kasuwanni, da kuma bunƙasa samar da dukiya domin rage talauci.
Ta bayyana cewa matakan sun haɗa da haɗa farashin musayar kuɗaɗen waje zuwa tsari guda, ƙara gaskiya da bayyana yadda ake gudanar da hada-hadar kuɗaɗen waje, da kuma ƙaddamar da tsarin ‘B-Match‘ domin gudanar da cinikayyar kuɗaɗen waje.
Sauran muhimman tsare-tsaren da ya lissafa sun haɗa da nasarar sake samar da jarin bankuna domin ƙarfafa juriyar su da inganta gasa da takwarorin su na duniya.
Haka kuma, ta bayyana ƙaddamar da tsarin BVN ga waɗanda ba mazauna Nijeriya ba (Non-Resident BVN), wanda zai sauƙaƙa wa ’yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje samun yin ayyukan hadahadar banki a cikin gida.
Sannan ta kuma yi nuni da ƙaddamar da tsarin hadahadar kuɗi da ake sa ran cimma nasarar da nan da 2038, wato tsarin Nigeria Payments System Vision 2028, wani tsari da aka tsara domin inganta tsarin biyan kuɗi a Nijeriya.
Matakan Rage Hauhawar Farashi Da Kula Da Yawan Kuɗi
A nan, ta bayyana cewa, domin inganta kula da yawan kuɗin da ke zagayawa a da’irar tattalin arziki da rage matsin hauhawar farashi, CBN ya aiwatar da dokar ajiye kashi 75 cikin 100 na wasu kuɗaɗen ajiyar gwamnati da ba sa ƙarƙashin tsarin Asusun Bai-ɗaya na ‘Treasury Single Account’ (TSA) a matsayin Adadin Ajiyar Tilas (Cash Reserve Ratio – CRR).
Ta ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin CBN na sarrafa yawan kuɗin da ke zagayawa a da’irar tattalin arziki da kuma rage matsin hauhawar farashi.
Ƙaddamar Da Sabon Ma’aunin Kuɗin Lamuni Na Gajeren Wa’adi
A nan, Hakama Sidi Ali ta kuma bayyana cewa CBN, tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Dillalan Kasuwannin Kuɗi (Financial Markets Dealers Association – FMDA), ya ƙaddamar da Nigerian Overnight Financing Rate (NOFR).
Ta ce an samar da ma’aunin ne domin ya zama abin dogaro kuma a bayyane wajen tantance farashin gejin ladar kuɗin lamunin na ɗan gajeren lokaci, bisa la’akari da yanayin kasuwa da kuma kyawawan ƙa’idojin da ake amfani da su a duniya.
Kira Ga Masu Ruwa da Tsaki Su Bayar da Gudunmawa
Da take sake jaddada aniyar CBN wajen faɗaɗa damar samun ayyukan harkokin kuɗi ga kowa, Hakama ta ce ba za a iya samun bunƙasar tattalin arziki mai ɗorewa ba idan ba a samar da damar tattalin arziki ga dukkan sassan al’umma ba.
Saboda haka, ta buƙaci mahalarta taron da su bayyana ra’ayoyin su cikin gaskiya, domin taimakawa wajen tsara matakan manufofin kuɗi na gaba.
Mahalarta taron sun haɗa da wakilan Gwamnatin Jihar Oyo, sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma, cibiyoyin hada-hadar kuɗi, ƙungiyoyin kasuwanni da ’yan kasuwa, ƙungiyoyin ƙwararru, jami’o’i da sauran cibiyoyin ilimi, ƙungiyoyin fararen hula, masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), ɗalibai da kuma shugabannin kafafen yaɗa labarai.
Shirin ‘CBN Listens‘ na daga cikin hanyoyin da babban bankin ke amfani da su wajen tattaunawa da jama’a da karɓar shawarwarin su, domin tabbatar da cewa manufofin sa sun yi la’akari da buƙatu da ƙalubalen da al’umma ke fuskanta.







