• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Sunday, November 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Idris na so kafofin yaɗa labarai su guji yaɗa labaran ƙarya

FATI ABDUL by FATI ABDUL
October 22, 2026
in Labarai
A A
0
Idris na so kafofin yaɗa labarai su guji yaɗa labaran ƙarya
Ministan Yaɗa Labarai, Alhaji Mohammed Idris, yana gabatar da jawabin sa

Ministan Yaɗa Labarai, Alhaji Mohammed Idris, yana gabatar da jawabin sa

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris, ya yi kira ga kafofin yaɗa labarai a Nijeriya da su ƙara himma wajen tantance sahihancin labarai tare da guje wa yaɗa bayanan ƙarya da labaran da aka ƙawata don tayar da hankali, musamman yayin da zaɓen 2027 ke ƙaratowa.

Ministan ya yi wannan kiran ne yau Alhamis a Abuja, yayin ƙaddamar da sabon tsarin haɗa sassan aikin jarida na kamfanin Media Trust Group, mai wallafa jaridar Daily Trust.

Idris ya ce kafofin yaɗa labarai na da muhimmiyar rawar da za su taka wajen tabbatar da cewa sahihan bayanai ne ke jagorantar rahotanni da sharhin da ake gabatarwa ga al’umma, ba son zuciya ko muradin siyasa ba.

Ya bayyana cewa yayin da zaɓen 2027 ke ƙaratowa, za a samu ƙaruwar saƙonnin siyasa, zarge-zarge da martani tsakanin masu ruwa da tsaki, lamarin da ke buƙatar ’yan jarida su riƙa bincika sahihancin duk wani bayani kafin yaɗa shi.

Ya ce, “Yayin da Nijeriya ke tunkarar babban zaɓen 2027, nauyin da ke kan kafofin yaɗa labarai zai ƙara girma.”

Ministan ya yi gargaɗin cewa bai kamata kafofin yaɗa labarai su fifita saurin fitar da labari ko jan hankalin masu karatu a kan sahihancin labari ba, yana mai cewa irin wannan ɗabi’a na iya jawo asarar amincewar da jama’a suke da ita ga kafafen.

Ya jaddada muhimmancin bin ƙa’idojin aikin jarida da suka haɗa da adalci, gaskiya, bayyana bayanai yadda suke da kuma bambance ra’ayi da sahihin labari.

Idris ya kuma yi gargaɗin cewa wasu ’yan cikin gida da na ƙasashen waje na iya amfani da lokacin siyasa wajen yaɗa bayanan ƙarya da za su iya haddasa rashin fahimta da barazana ga zaman lafiyar ƙasa.

Saboda haka, ya buƙaci hukumomin yaɗa labarai su zuba jari wajen horas da ma’aikatansu tare da samar musu da kayan aikin tantance sahihancin bayanai. Ya kuma bukaci kafafen da su riƙa haɗin gwiwa wajen yaƙi da yaɗa labaran ƙarya, duk da gasar da ke tsakaninsu.

Ministan ya ce bunƙasar fasahar (AI), da suka haɗa da hotunan bogi da bidiyoyin da aka ƙirƙira ko sauya wa, sun ƙara wahalar da aikin tantance sahihancin bayanai.

Ya bayyana cewa sahihancin bayanan da jama’a suke samu zai taka muhimmiyar rawa wajen gina amincewa da tsarin dimokuraɗiyya.

Ya ce gwamnatin tarayya na ƙarfafa shirye-shiryen wayar da kan jama’a kan yadda za su tantance bayanan da suke samu, ciki har da ƙoƙarin da ya taimaka wajen kafa Cibiyar Ƙasa da Ƙasa ta Wayar da Kan Jama’a kan Kafofin Yaɗa Labarai da Bayanai ta UNESCO, mai matsayi na 2, a Abuja.

Ya ƙara da cewa gwamnati na kuma tattaunawa kan yadda za a yi amfani da fasahar AI cikin tsari da ɗaukar matakan da suka dace a harkar yaɗa labarai.

Idris ya sake jaddada cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kallon kafofin yaɗa labarai a matsayin abokan hulɗa masu muhimmanci wajen ci gaban ƙasa da inganta dimokuraɗiyya.

Ya ce gwamnati na goyon bayan ’yancin aikin jarida da kuma rawar da ’yan jarida suke takawa wajen bincikar ayyukan hukumomin gwamnati da tambayar masu riƙe da madafun iko.

Sai dai ya bayyana cewa ya kamata a haɗa ’yancin aikin jarida da samar da hanyoyin da za su tabbatar da dorewar tattalin arzikin kamfanonin yaɗa labarai, yana mai cewa aikin jarida ba hidima ga al’umma kaɗai ba ne, har ma da sana’ar da ke samar da ayyukan yi da bayar da gudummawa ga tattalin arzikin ƙasa.

Da yake magana kan sabon tsarin aikin jarida na Media Trust Group, ministan ya ce matakin ya nuna yadda kamfanin ke ƙoƙarin dacewa da sauye-sauyen da ke faruwa a harkar yaɗa labarai, inda jama’a ke buƙatar sahihan bayanai ta jaridu, rediyo, talabijin da kafafen intanet.

Ya taya shugabanci da ma’aikatan kamfanin murna bisa wannan ƙoƙari, tare da ƙarfafa musu gwiwar mayar da sabon tsarin cibiyar ƙirƙira, binciken zurfi da yaɗa labarai bisa ƙa’idojin aikin.

Ministan ya kuma buƙaci kafofin yaɗa labarai su riƙa ba da kulawa ga labaran nasarori da abubuwan alheri da ke faruwa a Najeriya, ba wai mayar da hankali kan matsaloli da gazawa kawai ba.

Ya ce bai kamata a ɗauki aikin jarida a matsayin sana’ar adawa da gwamnati a kowane lokaci ba, domin labaran abubuwan da ke tafiya yadda ya kamata su ma sun cancanci kulawa kamar yadda ake ba rahotannin gazawa da matsaloli.

Ya buƙaci ’yan jarida su ci gaba da kare ’yancin aikinsu tare da bayar da gudummawa wajen samar da sahihin bayani da ci gaban ƙasa.

Manyan baƙin da suka halarci taron sun haɗa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin; Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi; da Darakta-Janar na Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA), Kashifu Inuwa, da sauran manyan baƙi da masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai.

Previous Post

Tinubu ya taya Kwankwaso murnar cika shekaru 70

Next Post

Taron Jin Ra’ayoyin Jama’a A Ibadan: CBN ya himmatu wajen shigar da kowa cikin tsarin hada-hadar kuɗi da bunƙasar tattalin arziki mai ɗorewa – Hakama Sidi-Ali

Related Posts

Tinubu ya ƙudiri aniyar ba manoma lamunin kuɗi ba tare da ruwa ba
Siyasa

Tinubu ya ƙudiri aniyar ba manoma lamunin kuɗi ba tare da ruwa ba

November 28, 2026
Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura
Labarai

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

November 25, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
Next Post
Rahoton CBN: An yi hadahadar kuɗi ta wayar hannu har adadin naira tiriliyan 372 cikin 2025

Taron Jin Ra'ayoyin Jama'a A Ibadan: CBN ya himmatu wajen shigar da kowa cikin tsarin hada-hadar kuɗi da bunƙasar tattalin arziki mai ɗorewa – Hakama Sidi-Ali

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!