• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Sunday, November 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

2027: ADC ta zargi Kwankwaso da yi wa Tinubu aiki a fakaice

ALI KANO by ALI KANO
October 16, 2026
in Siyasa
A A
0
2027: ADC ta zargi Kwankwaso da yi wa Tinubu aiki a fakaice
Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso lokacin wata ziyara a Fadar Shugaban Ƙasa

Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso lokacin wata ziyara a Fadar Shugaban Ƙasa

Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ya zargi Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), da taimakawa wajen cimma muradun siyasar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, bayan kiran da ya yi ga tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da ya janye takarar sa domin Peter Obi ya tsaya takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Kwamitin ya bayyana kiran da Kwankwason ya yi a matsayin abin zargi da kuma son kai, yana mai cewa matakin na iya raunana ‘yan adawa tare da amfani ga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

A cikin wata sanarwa da ya fitar yau Juma’a, Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC, Kola Ologbondiyan, ya ce kalaman Kwankwaso a wata hira da gidan talbijin na Channels sun nuna cewa ya karkatar da hankalin sa daga muhimman batutuwan da suka shafi al’ummar Nijeriya.

Atiku Abubakar dai shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027.

Ologbondiyan ya soki Kwankwaso bisa mayar da hankali kan shugabannin ‘yan adawa maimakon ƙalubalantar gwamnatin Tinubu, wadda ya ce ‘yan Nijeriya ke ɗokin kaɗa ƙuri’a domin kawo ƙarshen ta saboda matsin tattalin arziki da rashin tsaro da ƙasar nan ke fuskanta.

Ya bayyana tabbacin cewa Atiku zai lashe zaɓen shugaban ƙasa a Jihar Kano, mahaifar Kwankwaso, ko da ba tare da goyon bayan tsohon gwamnan ba.

A cewar sa, matsin rayuwa, yunwa, talauci da rashin tsaro da al’ummar ƙasar nan suke fuskanta su ne za su yi tasiri wajen yanke shawarar masu zaɓe a zaɓen mai zuwa.

Mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen na ADC ya kuma nuna shakku kan matakin Kwankwaso, la’akari da alaƙar siyasar sa da Peter Obi da kuma jam’iyyar NDC.

Ya ce ya kamata jagoran ‘yan adawa da ke son kawar da gwamnatin da ke kan mulki ya mayar da hankali wajen ƙarfafa ‘yan adawa, maimakon yunƙurin raunana wani ɗan takarar shugaban ƙasa na ‘yan adawa.

Ologbondiyan ya ce: “Maimakon yaƙin neman zaɓe a kan Shugaba Tinubu, wanda ‘yan Nijeriya ke ɗokin kaɗa ƙuri’a domin kawar da gwamnatin sa, Kwankwaso ya mayar da hankali ne kan Atiku Abubakar, ɗan takarar ADC, wanda miliyoyin ‘yan Nijeriya suke ganin zai iya dawo da daidaiton tattalin arziki da kuma sauƙaƙa tsadar rayuwa.”

Ya yi zargin cewa Kwankwaso ya fi mayar da hankali kan burin sa na siyasa bayan zaɓen 2027 maimakon magance matsalolin da ƙasar nan ke fuskanta a halin yanzu.

Ya ƙara da cewa: “Bayan rahotannin da suka nuna cewa ya taɓa bayyana ofishin mataimakin shugaban ƙasa a matsayin ‘tayar ajiya’, da alama ya fi damuwa da shirya tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2031 fiye da magance matsalolin gaggawa da ke addabar ‘yan Nijeriya a yau.”

Ologbondiyan ya yi zargin cewa matakin Kwankwaso ya haifar da tambayoyi game da wanda yake son ya yi nasara a zaɓen 2027, yana mai cewa abin da yake yi ya fi amfani ga APC mai mulki fiye da kowace jam’iyyar adawa.

Sai dai, mai magana da yawun ADC ɗin ya ƙalubalanci ra’ayin cewa goyon bayan Kwankwaso shi ne muhimmin abin da kowane ɗan takarar shugaban ƙasa ke buƙata domin samun nasara a Jihar Kano.

Da yake magana kan zaɓen shugaban ƙasa na 2003 da 2007, Ologbondiyan ya tuna cewa tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya samu nasara a Kano duk da cewa ba shi da goyon bayan Kwankwaso a lokacin. Ya ce Atiku ma zai iya samun irin wannan nasarar a zaɓen 2027.

Ya ce: “Abin da Kwankwaso yake yi yana nufin taimakawa wajen cimma muradun Shugaba Tinubu. Wannan wata dabara ce da APC ta saba amfani da ita, ta hanyar amfani da waɗanda ke son haɗa kai da ita a cikin ‘yan adawa domin haifar da ruɗani, tayar da saɓani da raunana ƙoƙarin haɗin gwiwa na kawo sauyin siyasa.”

Ologbondiyan ya bayyana cewa ‘yan Nijeriya sun waye, kuma ba za su bari a karkatar da hankalin su da dabarun siyasa da aka tsara domin raunana ‘yan adawa da kuma taimaka wa gwamnatin da ba ta da farin jini ba.

Ya zargi Kwankwaso da kasancewa yana fifita burin sa na siyasa fiye da muradun haɗin gwiwar jam’iyyun adawa.

A cewar sa, kiran da Kwankwaso ya yi na a fifita Obi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa bai ta’allaka da ƙarfafa damar Obi ta samun nasara kaɗai ba, sai dai yana iya kasancewa wani yunƙuri na shirya tattaunawar siyasa da za a yi nan gaba gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2031.

Tags: ADCNDCPeter ObiRabiu Musa Kwankwasozaben2027
Previous Post

Zaɓen 2027: Idris ya yi gargaɗi kan sayen ƙuri’u, rashin fitowar masu zaɓe da rikicin zaɓe

Next Post

NDC ba za ta janye wa Atiku a zaɓen 2027 ba – Kwankwaso

Related Posts

Tinubu ya ƙudiri aniyar ba manoma lamunin kuɗi ba tare da ruwa ba
Siyasa

Tinubu ya ƙudiri aniyar ba manoma lamunin kuɗi ba tare da ruwa ba

November 28, 2026
Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Sanata Barau ya haɗa malamai sama da 2,000 domin tallata Tinubu, Gwamna Abba da ’yan takarar APC
Siyasa

Sanata Barau ya haɗa malamai sama da 2,000 domin tallata Tinubu, Gwamna Abba da ’yan takarar APC

November 24, 2026
Kwankwaso ya tura ni wajen Tinubu bayan mun yi alƙawarin komawa APC, inji Abba Yusuf
Siyasa

Kwankwaso ya tura ni wajen Tinubu bayan mun yi alƙawarin komawa APC, inji Abba Yusuf

November 23, 2026
Next Post
Kwankwaso ya koma ADC, ya ƙarfafa haɗakar adawa a Kano

NDC ba za ta janye wa Atiku a zaɓen 2027 ba - Kwankwaso

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!