Gwamnatin Nijeriya ta bayyana aniyar mayar da hankali kan bunƙasa zuba jari, ƙarfafa kasuwannin kuɗi da samar da ci gaba mai ɗorewa, bayan matakan da aka ɗauka na daidaita tattalin arzikin ƙasar.
An bayyana hakan ne yayin tarurrukan da Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso da Ministan Kuɗi kuma Ministan da ke Kula da Tattalin Arziki, Mista Taiwo Oyedele, suka gudanar ga manyan shugabannin Asusun Bada Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya a birnin Bangkok, ranar Litinin, 12 ga Oktoba, 2026.
A yayin waɗannan tarurrukan da aka gudanar a gefen taron shekara-shekara na IMF da Bankin Duniya na shekarar 2026, jami’an Nijeriya dai sun gana da Mataimakin Manajan Darakta na Farko na IMF, Mista Dan Katz, da Shugaban Bankin Duniya, Mista Ajay Banga.
Tattaunawar da aka yi da wakilan IMF ta mayar da hankali kan hasashen tattalin arzikin Nijeriya, muhimman manufofin tattalin arziki da kuma hanyoyin faɗaɗa haɗin gwiwar fasaha tsakanin ɓangarorin biyu.
A ɗaya ɓangaren kuma, ganawar da aka yi ɗin da shugabannin Bankin Duniya ta mayar da hankali kan samar da kuɗaɗen ayyukan raya ƙasa, ƙarfafa rawar kamfanoni masu zaman kan su, bunƙasa ababen more rayuwa, sauye-sauyen fasahar zamani da kuma faɗaɗa damar samun hidimomin kuɗi.
A cewar bayanan da aka gabatar, CBN na ƙara mayar da hankali kan yadda daidaituwar tattalin arziki za ta taimaka wajen gina tsarin kuɗi mai ƙarfi, inganta kasuwannin kuɗi da ƙarfafa amincewar masu zuba jari.
Haka kuma, ana sa ran inganta alaƙar hada-hadar kuɗi tsakanin Nijeriya da sauran ƙasashen duniya zai taimaka wajen buɗe sabbin damarmakin zuba jari da bunƙasa tattalin arzikin ƙasar.
Tarurrukan sun kuma nuna muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin manufofin kuɗaɗen gwamnati da na babban banki, domin samar da yanayin tattalin arziki mai tabbas wanda zai taimaka wajen ƙarfafa amincewar masu zuba jari da tallafa wa harkokin kasuwanci.
Mataimakin Gwamnan CBN mai kula da manufofin tattalin arziki, Philip Ikeazor, ya halarci tarurrukan tare da manyan jami’ai daga Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya da Babban Bankin Nijeriya.
Rahoton ya nuna cewa babban burin Nijeriya a mataki na gaba shi ne gina kan matakan daidaita tattalin arzikin da aka ɗauka, ta hanyar ƙarfafa tsarin kuɗi da samar da yanayin da zai tallafa wa cigaban tattalin arziki mai ɗorewa a dogon lokaci.







