• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Sunday, November 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

Shettima ga Arewa: Kada ku damu, babu abin tsoro a wa’adin Tinubu na biyu

* Mataimakin Shugaban Ƙasa ya buƙaci ‘yan Arewa su haɗa kai domin sake zaɓen Tinubu a 2027, yayin da A4A ta tabbatar da goyon bayan ta ga takarar

FATI ABDUL by FATI ABDUL
October 12, 2026
in Siyasa
A A
0
Shettima ga Arewa: Kada ku damu, babu abin tsoro a wa’adin Tinubu na biyu
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, yana musabaha da Shugaban Kwamitin Amintattu na ƙungiyar "Arewa for Asiwaju" (A4A), tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, yayin da Darakta-Janar na A4A, tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Abubakar Badaru, yake kallo, lokacin da Shettima ya karɓi tawagar ƙungiyar a Abuja

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, yana musabaha da Shugaban Kwamitin Amintattu na ƙungiyar "Arewa for Asiwaju" (A4A), tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, yayin da Darakta-Janar na A4A, tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Abubakar Badaru, yake kallo, lokacin da Shettima ya karɓi tawagar ƙungiyar a Abuja

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana cewa babu wani dalilin da zai sa Arewa ta ji tsoron sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a karo na biyu, yana mai cewa yankin ya amfana sosai da gwamnatin sa, kuma akwai sauran alherin da zai samu idan aka sake zaɓen ta a zaɓen 2027.

Shettima ya bayyana hakan ne yau Litinin, lokacin da ya karɓi tawagar ƙungiyar Arewa for Asiwaju (A4A), wata cibiya da ke aiki domin ganin an sake zaɓen Shugaba Tinubu a wa’adi na biyu, a ziyarar ban-girma da ta kai masa fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Ya yi kira ga shugabanni da al’ummar Arewa da su haɗa kai su zama tsintsiya maɗaurin ki ɗaya wajen neman ci gaban yankin da inganta rayuwar al’ummarsa, yana mai cewa waɗannan na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatin Tinubu ta sa a gaba.

A cewar sa, Arewa ta samu wakilci da dama a muƙaman gwamnati, tare da ayyukan raya ƙasa da shirye-shiryen da suka shafi tattalin arziki da jin daɗin jama’a.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ce: “Mu haɗa kai a matsayin al’umma, mu yi aiki domin cigaban yankin mu da cigaban jama’ar mu ta hanyar sake zaɓen wannan gwamnati. Muna amfana, kuma muna da damar ci gaba da amfana da wannan gwamnati ta hanyoyi da dama.

“Bankin Noma ya bayar da lamunin Naira biliyan 450 ga manoma ƙanana 700,000 a Nijeriya, kuma kusan kashi 70 cikin 100 na waɗanda suka amfana ‘yan Arewa ne.

“Gwamnatin yanzu tana ƙoƙarin kammala manyan ayyukan raya ƙasa a sassa daban-daban na ƙasar nan. Ina tabbatar muku cewa Shugaban Ƙasa yana ƙaunar Arewa, kuma zai yi aiki domin Arewa.”

Shettima ya gode wa shugabannin A4A bisa goyon bayan da suke bai wa Shugaba Tinubu, sannan ya buƙace su da su ƙara himma wajen wayar da kan jama’a da tattara goyon baya a matakin ƙananan hukumomi, mazaɓu da al’ummomi daban-daban a faɗin Arewa.

Zaman Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da ‘yan ƙungiyar Arewa for Asiwaju (A4A) da suka ziyarce shi

Darakta-Janar na A4A, tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Abubakar Badaru, ya bayyana cewa ƙungiyar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba har sai ta cimma burin ta na ganin Arewa ta taka rawar gani wajen sake zaɓen Shugaba Tinubu a 2027.

Badaru ya ce ƙungiyar na shirin tattaunawa da shugabannin addinai, ciki har da malaman Musulunci da na Kiristanci, da sauran fitattun ‘yan Nijeriya domin bayyana musu dalilan da suka sa take ganin ya dace a sake zaɓen tikitin Tinubu da Shettima.

Ya ce: “Dangane da tattaunawa da manyan mutane, mun yi nisa sosai. Mun sha ganawa da su, kuma kwamitin amintattu zai sake ganawa da su domin ƙarfafa nasarorin da muka samu da kuma bayyana dalilin da ya sa ya kamata a goyi bayan wannan tikiti.

“Muna kuma tallafa wa Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa (PCC) a dukkan ƙananan ayyukan da suke buƙatar mu yi, domin su babban tsari ne. Mu kuma muna son mayar da hankali sosai kan hulɗa da jama’a a matakin tushe, wato ƙananan hukumomi da mazaɓu.”

Shi ma Shugaban Kwamitin Amintattu na A4A, tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya ce ƙungiyar, wadda ta taka rawa wajen neman zaɓen Tinubu a 2023, tana da niyyar sake yin irin wannan ƙoƙari a zaɓen 2027.

Shekarau ya bayyana cewa ƙungiyar ta gudanar da tarurruka da gwamnonin Arewa da sauran masu ruwa da tsaki domin musayar ra’ayi da tsara hanyoyin haɗin gwiwa da za su taimaka wajen cimma manufar sake zaɓen Shugaban Ƙasa.

Ya kuma ce A4A ta kammala shirye-shiryen samar da cikakkiyar sakatariya domin inganta ayyukan ta da daidaita harkokin ƙungiyar.

A cewar sa, sakatariyar za ta ƙunshi ofisoshin daraktoci, yayin da masu kula da jihohi za su riƙa gabatar da rahotanni, nazarin su da karɓar umurnin gudanar da ayyuka.

Shekarau ya kuma gayyaci Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, domin ya ƙaddamar da sabon ginin ofishin A4A a hukumance ranar Asabar, 17 ga Oktoba, 2026.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai tsofaffin gwamnonin Jihar Filato, Cif Joshua Dariye da Sanata Simon Lalong; tsohon Gwamnan Taraba, Rev. Jolly Nyame; tsohon Gwamnan Kogi, Alhaji Yahaya Bello; tsohon Gwamnan Katsina, Barista Ibrahim Shehu Shema; tsohon Gwamnan Bauchi, Malam Isa Yuguda; Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Manufofi da Tsare-tsare, Hajiya Hadiza Bala Usman; da Shugaban Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya.

Haka kuma, taron ya samu halartar wasu manyan jami’an gwamnati, da membobin Kwamitin Amintattu da sakatariyar ƙungiyar A4A.

Tags: A4AArewaArewa for Asiwaju (A4A)Badaru AbubakarKashim ShettimaMalam Ibrahim Shekarauzaben2027ƙungiya
Previous Post

Ministan Yaɗa Labarai ya kare rangwamen farashin mai na NNPC, ya ce sauye-sauyen tattalin arziki za su samar da wadata

Next Post

Raɗɗa ya ƙara tallafin karatun ɗalibai da kashi 100% bayan shekaru 18 ba tare da ƙari ba

Related Posts

Tinubu ya ƙudiri aniyar ba manoma lamunin kuɗi ba tare da ruwa ba
Siyasa

Tinubu ya ƙudiri aniyar ba manoma lamunin kuɗi ba tare da ruwa ba

November 28, 2026
Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Sanata Barau ya haɗa malamai sama da 2,000 domin tallata Tinubu, Gwamna Abba da ’yan takarar APC
Siyasa

Sanata Barau ya haɗa malamai sama da 2,000 domin tallata Tinubu, Gwamna Abba da ’yan takarar APC

November 24, 2026
Kwankwaso ya tura ni wajen Tinubu bayan mun yi alƙawarin komawa APC, inji Abba Yusuf
Siyasa

Kwankwaso ya tura ni wajen Tinubu bayan mun yi alƙawarin komawa APC, inji Abba Yusuf

November 23, 2026
Next Post
Raɗɗa ya ƙara tallafin karatun ɗalibai da kashi 100% bayan shekaru 18 ba tare da ƙari ba

Raɗɗa ya ƙara tallafin karatun ɗalibai da kashi 100% bayan shekaru 18 ba tare da ƙari ba

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!