• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Sunday, November 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

Gwamnan Bauchi ya yaba wa Tinubu kan gyare-gyaren tattalin arziki da inganta tsaro

WAKILIN MU by WAKILIN MU
October 6, 2026
in Siyasa
A A
0
Gwamnan Bauchi ya yaba wa Tinubu kan gyare-gyaren tattalin arziki da inganta tsaro
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan gyare-gyaren tattalin arziki da matakan inganta tsaro da gwamnatin sa take aiwatarwa, yana mai cewa matakan sun fara haifar da sakamako mai kyau a Jihar Bauchi da ƙasa baki ɗaya.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, lokacin da ya karɓi baƙuncin Ministan Kuɗi da Kula da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele, da Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama’a, Dakta Muhammad Ali Pate, waɗanda suka kai masa ziyarar ban-girma a Gidan Gwamnati da ke Bauchi.

Yayin da yake bayyana goyon bayan gwamnatin jihar ga manufofin Gwamnatin Tarayya, Gwamna Mohammed ya ce matakan da gwamnatin Tinubu ke ɗauka a fannonin tattalin arziki da tsaro suna haifar da sauyi mai amfani a aikace.

Ya ce al’ummar Jihar Bauchi suna sane da ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya ke yi na daidaita tattalin arziki da magance matsalolin tsaro, yana mai cewa jama’a na ganin tasirin waɗannan matakai.

Gwamnan ya yaba da kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi, yana mai cewa haɗin gwiwar na taimakawa wajen aiwatar da manufofi da shirye-shiryen ci gaba.

Bala Mohammed ya kuma jinjina wa Tinubu kan samar da ayyukan cigaba ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba, inda ya bayar da misalin Jihar Bauchi da Jihar Oyo a matsayin wasu daga cikin jihohin da suka amfana da irin wannan tsari.

A ɓangaren tsaro kuwa, gwamnan ya yaba da matakan da Shugaban Ƙasa ya ɗauka wajen tura jami’an tsaro ƙarƙashin kulawar Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu, tare da hukumomin soji, domin yaƙi da ‘yan bindiga da suka addabi wasu sassan Jihar Bauchi a baya.

Ya ce matakan sun taimaka wajen fatattakar ‘yan bindigar tare da inganta tsaro da zaman lafiya a jihar.

Tags: BauchiGwamna Bala Mohammedgyare-gyareShugaba Bola Ahmed Tinubutattalin arzikitsaro
Previous Post

Binciken CBN: ’Yan Nijeriya sun fi maida hankali wajen sayen abinci fiye da zuba jari da sayen gidaje a Satumba

Next Post

Shekara ukun Cardoso: Mun gaji gundarin dala miliyan 859 a asusun kuɗaɗen waje, yanzu kuwa ya cika maƙil da dala biliyan 40 – CBN

Related Posts

Tinubu ya ƙudiri aniyar ba manoma lamunin kuɗi ba tare da ruwa ba
Siyasa

Tinubu ya ƙudiri aniyar ba manoma lamunin kuɗi ba tare da ruwa ba

November 28, 2026
Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Sanata Barau ya haɗa malamai sama da 2,000 domin tallata Tinubu, Gwamna Abba da ’yan takarar APC
Siyasa

Sanata Barau ya haɗa malamai sama da 2,000 domin tallata Tinubu, Gwamna Abba da ’yan takarar APC

November 24, 2026
Kwankwaso ya tura ni wajen Tinubu bayan mun yi alƙawarin komawa APC, inji Abba Yusuf
Siyasa

Kwankwaso ya tura ni wajen Tinubu bayan mun yi alƙawarin komawa APC, inji Abba Yusuf

November 23, 2026
Next Post
CBN ya ƙaddamar da sabon kundin dokokin canjin kuɗaɗen waje

Shekara ukun Cardoso: Mun gaji gundarin dala miliyan 859 a asusun kuɗaɗen waje, yanzu kuwa ya cika maƙil da dala biliyan 40 - CBN

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!