• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekara ukun Cardoso: Mun gaji gundarin dala miliyan 859 a asusun kuɗaɗen waje, yanzu kuwa ya cika maƙil da dala biliyan 40 – CBN

Ashafa Murnai Barkiya by Ashafa Murnai Barkiya
October 6, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
CBN ya ƙaddamar da sabon kundin dokokin canjin kuɗaɗen waje
Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Olayemi Cardoso

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Olayemi Cardoso

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa har kusan ƙarshen 2023, adadin dalolin da ke asusun kuɗaɗen wajen Nijeriya bai wuce dala miliyan 859 kacal ba.

Wannan a cewar bankin ya nuna a 2023 an samu gagarimin koma-baya da aka samu wanda ba a taɓa samun irin sa a tarihin CBN.

CBN ya ƙara da cewa ƙanƙantar adadin a wancan lokaci ya yi ƙasa da kuɗin da ake buƙata wajen biyan kuɗin shigo da kaya na ƙasa da wata ɗaya.

CBN ya ƙara da cewa bayan shekaru uku darajar asusun ta sake ɗagawa cike maƙil zuwa dala biliyan 40 a ƙarƙashin jagorancin Gwamnan CBN na yanzu, Olayemi Cardoso.

Mataimakin Gwamnan CBN Mai Kula da Ayyukan Kamfanoni, Dr. Muhammad Abdullahi, ne ya bayyana hakan a wajen buɗe taron ƙara wa juna sani karo na 38 na Ƙungiyar Masu Rubuta Labaran Harkokin Kuɗi da Editocin Harkokin Kasuwanci, wanda aka gudanar cikin makon juya Abuja jiya.

Ya ce shugabannin da suka karɓi ragamar CBN a shekarar 2023 a ƙarƙashin Cardoso, ta tarar da matsaloli masu yawa, kuma dole ta aiwatar da sauye-sauye daban-daban domin magance su yadda ya kamata.

Ya ce: “Ya zuwa shekarar 2023, kasuwar canjin kuɗin waje ta Nijeriya ta kasance a rarrabe sosai, inda ake da bambance-bambancen farashi daban-daban na musayar kuɗi, tare da wata babbar kasuwar bayan fage.”

Ya ce wannan ya sa ya yi matuƙar wahala ga ’yan kasuwa su san wane farashin canji ne za a yi amfani da shi ko kuma lokacin da za a samu kuɗin waje.

“Bambancin da ke tsakanin farashin hukuma da na kasuwar bayan fage ya kai matsakaicin sama da kashi 60 cikin 100 a shekarar 2022, sannan ya wuce kashi 100 cikin 100 a wasu lokuta daga baya a waccan shekarar.

“Domin a fahimci girman lamarin, Bankin Duniya ya kiyasta cewa tallafin ɓoye da tsarin farashin canjin kuɗin ya haifar ya janyo wa ƙasar asarar kusan kashi uku cikin 100 na Gejin Ƙarfin Tattalin Arzikin Cikin Gida (GDP) a shekarar 2022.

“Matsin lambar ya kuma shafi ajiyar kuɗin waje na ƙasar nan. Adadin ajiyar kuɗin waje gaba ɗaya bai bayar da cikakken bayanin halin da ake ciki ba. Bayan cire wasu sanannun basussuka da wajibai na ɗan gajeren lokaci, bayanan CBN sun nuna cewa ajiyar kuɗin waje da za a iya amfani da ita kai tsaye ta tsaya a dala miliyan 859 a rubu’i na biyu na shekarar 2023.

“Haka kuma, basussukan da suka taso daga yarjejeniyoyin saye da sayar da kuɗin waje sun haura dala biliyan 7, lamarin da ya ƙara rashin tabbas ga da yin kaffa-kaffar da ’yan kasuwa da masu zuba jari suka riƙa yi da Nijeriya.

“A lokaci guda, jarin da ke shigowa ƙasar nan ya ragu, yayin da rashin tabbas game da samun kuɗin waje ya sa ya yi wahala ga ’yan kasuwa su tsara farashin kayayyaki, shirya zuba jari da kuma cika wasu wajibcin su.

“Kowace matsala ta ƙara jawo wata. Tsarin rabon kuɗin waje ta hanyar umarnin gwamnati ya raunana siginar da farashi ke bayarwa, tare da samar da damar yin amfani da bambancin farashi domin samun riba ba bisa ƙa’ida ba.”

Ya ce yawan kuɗin da ke yawo a cikin tsarin ya ƙara matsin lamba a kasuwar kuɗin waje.

“Daga nan kuma rashin tabbas ya sa ƙarin harkokin kasuwanci suka koma daga kasuwar hukuma, abin da ya ƙara raunana amincewa da tsarin.”

Ya ce waɗannan matsaloli ne suka zama tushen sauye-sauyen da CBN ya aiwatar a cikin shekaru uku da suka gabata.

Ya ce: “Kasuwar kuɗin waje tana buƙatar farashi mai bayyana a sarari da kuma ingantaccen tsarin hada-hadar kuɗi, amma zai yi wuya a ɗore da waɗannan sauye-sauye ba tare da tsaurara kula da yawan kuɗin da ke cikin tsarin ba.

“Haka kuma muna buƙatar bankuna masu ƙarfi waɗanda za su iya gudanar da ayyukan su yadda ya kamata yayin da ake aiwatar da waɗannan sauye-sauye. Wannan shi ne tunanin da ya jagoranci sauye-sauyen da suka biyo baya.

Previous Post

Gwamnan Bauchi ya yaba wa Tinubu kan gyare-gyaren tattalin arziki da inganta tsaro

Next Post

Tinubu ya yi alhinin rasuwar Nafi’u Baba-Ahmed

Related Posts

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

November 25, 2026
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

November 17, 2026
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

November 16, 2026
Next Post
Tinubu ya yi alhinin rasuwar Nafi’u Baba-Ahmed

Tinubu ya yi alhinin rasuwar Nafi'u Baba-Ahmed

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!