Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan gyare-gyaren tattalin arziki da matakan inganta tsaro da gwamnatin sa take aiwatarwa, yana mai cewa matakan sun fara haifar da sakamako mai kyau a Jihar Bauchi da ƙasa baki ɗaya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, lokacin da ya karɓi baƙuncin Ministan Kuɗi da Kula da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele, da Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama’a, Dakta Muhammad Ali Pate, waɗanda suka kai masa ziyarar ban-girma a Gidan Gwamnati da ke Bauchi.
Yayin da yake bayyana goyon bayan gwamnatin jihar ga manufofin Gwamnatin Tarayya, Gwamna Mohammed ya ce matakan da gwamnatin Tinubu ke ɗauka a fannonin tattalin arziki da tsaro suna haifar da sauyi mai amfani a aikace.
Ya ce al’ummar Jihar Bauchi suna sane da ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya ke yi na daidaita tattalin arziki da magance matsalolin tsaro, yana mai cewa jama’a na ganin tasirin waɗannan matakai.
Gwamnan ya yaba da kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi, yana mai cewa haɗin gwiwar na taimakawa wajen aiwatar da manufofi da shirye-shiryen ci gaba.
Bala Mohammed ya kuma jinjina wa Tinubu kan samar da ayyukan cigaba ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba, inda ya bayar da misalin Jihar Bauchi da Jihar Oyo a matsayin wasu daga cikin jihohin da suka amfana da irin wannan tsari.
A ɓangaren tsaro kuwa, gwamnan ya yaba da matakan da Shugaban Ƙasa ya ɗauka wajen tura jami’an tsaro ƙarƙashin kulawar Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu, tare da hukumomin soji, domin yaƙi da ‘yan bindiga da suka addabi wasu sassan Jihar Bauchi a baya.
Ya ce matakan sun taimaka wajen fatattakar ‘yan bindigar tare da inganta tsaro da zaman lafiya a jihar.







