Gwamnatin Tarayya ta kare matakin da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka na rashin halartar Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) karo na 81 a New York, tana mai cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima zai wakilce shi tare da jagorantar tawagar Nijeriya.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Shettima zai gabatar da jawabin Nijeriya a Babban Taron, tare da halartar manyan taruka da ganawa da shugabannin ƙasashe, ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da abokan hulɗar cigaba.
Idris ya ce Tinubu yana hutu a halin yanzu, yana mai cewa ba sabon abu ba ne ko kuma abin da zai rage matsayin Nijeriya na diflomasiyya ga Shugaban Ƙasa ya ba Mataimakin sa damar jagorantar tawagar ƙasar.
Ya ce Shettima na ɗauke da cikakken ikon Shugaban Ƙasa da na Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya, inda ya ƙara da cewa abubuwan da zai gudanar a New York za su mayar da hankali kan batutuwan zaman lafiya da tsaro, bunƙasar tattalin arziki, yaƙi da sauyin yanayi, gyaran tsarin kuɗaɗen duniya, cigaba mai ɗorewa, da haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa.
Ministan ya kuma mayar da martani kan kalaman tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar da wata ƙungiyar neman tasiri da ke Amurka da yake ɗaukar nauyin ta, waɗanda suka yi ayar tambaya kan rashin halartar Tinubu tare da ƙoƙarin danganta wasu dalilai da matakin.
Idris ya ce adawa ta siyasa da muhawara mai ƙarfi a bainar jama’a suna daga cikin ginshiƙan dimokiraɗiyya, amma ya yi gargaɗin kada a gabatar da zato a matsayin tabbataccen abu.
Ya buƙaci ’yan siyasa da su yi taka-tsantsan yayin magana kan batutuwan da suka shafi alaƙar Nijeriya da sauran ƙasashe da kuma martabar ƙasar.
Ministan ya ce Nijeriya tana daraja daɗaɗɗiyar alaƙar ta da Amurka, wadda ta haɗa da kasuwanci da zuba jari, haɗin gwiwar tsaro, makamashi, cibiyoyin dimokiraɗiyya, zaman lafiyar yankin da kuma alaƙar jama’a tsakanin ƙasashen biyu.
Ya ce ana gudanar da wannan alaƙa ne ta hanyoyin diflomasiyya da na gwamnati da aka tanada, kuma bai kamata a haɗa ta da kalaman siyasa na jam’iyyu ko ayyukan ƙungiyoyin neman tasiri masu zaman kan su da ke aiki a madadin ’yan siyasa ba.
Ya ce: “Saboda haka, Gwamnatin Tarayya tana kira ga ’yan Nijeriya da kafafen yaɗa labarai da su bambanta tsakanin bayanan da aka tabbatar, halastaccen ra’ayin siyasa da kuma hasashen da ba shi da tushe.”
Ya tabbatar wa da ’yan Nijeriya cewa za a wakilci ƙasar nan yadda ya kamata a Babban Taron, kuma za a ci gaba da kare muradun Nijeriya tare da ƙarfafa alaƙar ta da abokan hulɗar ta na ƙasa da ƙasa.







